*FOUR WRITERS*
*Rana Zafi*🔥
*Inuwa k'una*💥*Na Sadnaf*🎀🎀
*Rana Zafi Inuwa k'unna Sadnaf*
*Zabin Zuciya Umma Yahaya musa (sisin mama*)
*Imtihal Sadnas*
*Rayuwa ta Rahama Na lelle*
*Ga mai Bukatar Fitattu Hud'u Sai ya tura #500 zuwaga wanan acct d'in 2029764071 First Bank ko Recharge Card ta Wanan lambar 08037251895 sai ka turo da Shaidar biya ta layin nan 08033719070 idan daya kakeso 200 karku Sake a Baku labarin*
*Page 6*
*Free Page*Jawaheer sai data Samu awa d'aya a zaune akan Gadon ko kad'an bataji tana jin Bacci ba Sai Fad'uwar Gaba da Rashin Nutsuwa da take Fama dashi.
Abubakar kuwa Wuyansa yaji ya kage Sabida yanda ya Nannad'e Jikinsa Sabida yana da tsayi ba laifi banda Sauraye dake ta Cizonsa da Cinnaku D'auriya kawai yake yi dan yasan ko Yaya yayi Motsi Jawaheer zata iya ji ya rasa mai ya hana ta kwanciya har yanzu gashi yanzu idan yace fitowar zaiyi zata iya saka masa ihu Su Baffa su jiyo shi Kafin ya bad'e mata Hodar.
Jawaheer kuwa ba wai dan tana jin bacci ba ta mik'e ta nufi band'aki ta d'auro alwala dan tayi shafai da wutr dan Shine Abu na karshe da take yi kafin ta kwanta.
Abubakar kamar ya saka Hannu aka yayi ta zunduma ihu haka yaji yana kallonta ta tada Sallah shima sai data kusa awa d'aya akan Sallayar nan kuwa Jawaheer Addua kawai take akan Allah ya kareta daga Sharrin Abubakar.
Sai wajen k'arfe d'aya da Rabi ta mik'e da ga kan Sallayar ta Nad'e Sallayar ta ajiye a gefe har ta nufi wadrobe d'inta Dan ta canza kayanta zuwa Na Bacci haka kawai kuma Tayi tunanin barin na Jikinta tunda ba Nauyi ne dashi ba kuma bai Takura ta ba.
Kashe Fitilar d'akin tayi dan bata iya bacci a cikin Haske.
Haka kawai taji Gabanta yayi mumunan Fad'uwa haka kawai wani irin tsoro ya rufeta.
Da Sauri ta k'unna Fitilar Haske ya Gauraye d'akin ta fara dube dube dan Gani take kamar zata ga Abubakar ya shigo d'akin.
K'ofar ta kara dubawa ta tabbatar da a kulle yake ta duba windows ma taga ba ta inda koda Mage zai Samu k'ofar shigowa balle mutum ajiyar Zuciya ta Sauke a hankali tana tunanin Tsoron data saka a ranta ne ke sakata fad'uwar Gaba.
Shahada tayi ta kashe Fitilar ta hau kan gadonta da Sauri ta kwanta idonta Tar dan ko kadan babu alamar bacci a idonta a hankali ta janye d'aya pillon dake gefenta ta jawo Tabaryar turmin k'arfen da ta dade tana Ajiyarsa Tun daga lokacin da taga Abubakar na san shigo mata d'aki karfi da yaji Dan taga alamar tana Bukatarsa Indai Bazaiji Kunyar Neman keta mata haddi ba itama bazata ji kunyar ji masa Rauni ba duk da tasan k'arfin namiji Dana Mace ba d'aya bane bazai k'arbi Budurcinta cikin Sauki ba Sai ya sha wahala haka kawai ta damke Turmin k'arfen a hannunta Gam tana dan karewa d'akin kallo cikin hasken daya shigo ta window daya sa take iya ganin komai na d'akin duk da fitila a kashe yake ko kadan bata Fatan Bacci ya d'auketa.
A cikin Zuciyarta ta fara Karanta Suratul Mulk dan ta Haddace shi tsaf minti talatin da kwanciyarta wanda ya dai dai da karfe Biyun na dare taji alamar motsi a Kasan gadonta wani irin tsinkewa Zuciyarta yayi Gaban ta na balain Fad'uwa jikinta ya hau karkarwa har cikin ta na murd'e mata ko'ina na jikinta Rawa yake inda ta tattara duka k'arfinta ta aza shi akan turmin Karfen ta rik'e shi gam.
Abubakar kuwa fitowa yayi daga karkashin Gadon yana Tunanin Bacci Jawaheer tayi.
Mik'a ya fara yi yana wuwula wuyansa daya Sage masa ya fara Sosa jikinsa inda Sauraye da cinnaku suka yayagi Rabonsu.
