*FOUR WRITERS*
*Rana Zafi*🔥
*Inuwa k'una*💥*Na Sadnaf*🎀🎀
*Rana Zafi Inuwa k'unna Sadnaf*
*Zabin Zuciya Umma Yahaya musa (sisin mama*)
*Imtihal Sadnas*
*Rayuwa ta Rahama Na lelle*
*Ga mai Bukatar Fitattu Hud'u Sai ya tura #500 zuwaga wanan acct d'in 2029764071 First Bank ko Recharge Card ta Wanan lambar 08037251895 sai ka turo da Shaidar biya ta layin nan 08033719070 idan daya kakeso 200 karku Sake a Baku labarin*
*Page 4*
*free page*
Jawaheer d'auke idonta Tayi Da Sauri a lokacin da suka had'a ido da Abubakar daya k'afeta da ido yana wani Abu da baki kamar tsohon Mayye ta tsani wanan kallon da yake mata kamar ya had'iyeta a cikin Shekarar nan yabi ya canja mata yana gwada mata Halayyen da da duk baya mata yanzu bashida burin daya Wuce yaga ya kawo Hannu Jikinta gashi yanzu kai tsaye yake fad'o mata cikin d'aki Sabanin d'a da Sai dai ya kwankwasa mata k'ofa idan kuwa a Palo ya tarar da ita a Zaune sai ya ringa k'ok'arin Zama a kusa da ita Jiya haka kawai tana Zaune tana Assignment d'in da aka basu bata san da shigowarsa ba Sai ji Tayi ana Shafa mata Gashi Ya wani rik'e jelar gashinta yana wasa dashi Sai da Hajjo Ta fito ta daka masa tsawa tare da masa Fad'a Sam bata ganewa Abubakar d'in Yanzu dan bata tab'a Zama Comfortable idan yana nan har sai taga ya fita.
Da Sauri ta tare musu abin hawa suka shige kafin ya tsallako tana jan sirrin tsakin takura mata da yake yi.
Sai Wajen k'arfe Uku suka dawo Gidan a gajiye Su Nana suka nufi B'angarensu Jawaheer itama tayi Nasu B'angaren dan sosai take jinta a Gajiye bata da burin daya Wuce ta watsa ruwa ta kwanta Sabida yau ba Islamiyya.
Ganin tana ta Sallama ba'a Amsa mata ba yasa ta nufi d'akin Hajjo tana kwada Sallama ga mamakinta sai taga bata d'akin itace har da duba band'aki nan ma bata ciki.
Tunanin Kila ta fita Unguwa ne yasa ta fito ta shige d'akinta Sosai taji dadi da babu kowa dan zata sha baccinta ta more sai yanzu ta tuna Hajjo tace mata zata je Gidan wata 'yar uwarta da akayi wa Haihuwa Abba da Abba k'arami da Baffa kuwa dama basa nan suna wajen Baffa Badamasi tunda Yau babu Islamiyya tare suke dawowa Jabeer kuwa yana can kano university of Buk Sai ya Samu Hutu yake zuwa Abubakar ne yake level 3 a university of Jos.
K'ofar Palo kawai ta rufe hankalinta kwance ta Shige d'akinta tana wurgi da Hijabin Jikinta dan Allah ne kawai ya san irin zafin da take ji
Dankwalin kanta ta cire shima ta wurgar take Gashinta da akayiwa kananan kalba ya zubo Saman kafad'arta ta fara cire kayan jikinta.
Abubakar tunda yaji alamar shigowarta ya lab'e a bayan labule dan ya dade yana Neman irin wanan opportunity d'in da zai zamana ba kowa shi ko bai Sameta ba ya samu dai ya rage Zafi.
Yasan indai Jawaheer tasan shi kadai ne a gida B'angarensu Nana zata wuce bazata Yarda tazo nan B'angaren ba dan daidai da Hajjo bata san zai dawo Gida ba Musamman tace masa zata fita yaje ya samu Baffa Badamasi a shago su dawo tare dan ita ma haka kawai taji hankalinta bai kwanta da Barin Abubakar da Jawaheer a waje d'aya ba ita kanta tasan Abubakar ya canja Sam bata ganewa irin kallon da yake bin Jawaheer dashi a 'yan kwanakin nan Jiya Ranta ba k'aramin b'aci yayi ba data ga ya na shafa Gashin Jawaheer Sosai ta nuna masa b'acin Ranta a karshe ta had'a da mishi Nasiha akan kar ya manta Jawaheer ba Muharramarsa bace Shaidan zai iya Shiga tsakaninsu har ta shiga d'aki haka kawai Zuciyarta ta kasa Nutsuwa da barin sa waje d'aya da Jawaheer Duk da ita ta haifeshi ta kuma san irin tarbiyyar data bashi amma hakan bai sa hankalinta ya kwanta ba.