Page 7

139 13 0
                                    

*FOUR WRITERS*
    
*Rana Zafi*🔥
      *Inuwa k'una*💥

           *Na Sadnaf*🎀🎀

*Rana Zafi Inuwa k'unna Sadnaf*

*Zabin Zuciya Umma Yahaya musa (sisin mama*)

*Imtihal Sadnas*

*Rayuwa ta Rahama Na lelle*

*Ga mai Bukatar Fitattu Hud'u Sai ya tura #500 zuwaga wanan acct d'in 2029764071 First Bank ko Recharge Card ta  Wanan lambar  08037251895 sai ka turo da Shaidar biya ta layin nan 08033719070 idan daya kakeso 200 karku Sake a Baku labarin*

*Page 7* 

           *Free page*

Jawaheer ta tsorata Sosai da halin da Hajjo take ciki hakane yasa ta zub'e akan gwiwarta tana Ruko hannun Hajjon dake ta Kakarwa tana "Innalillahi wa inna ilaihi Rajiun Duk D'auriyar Hajjo da kawaici sai gata agaban Abubakar tana k'ok'arin Rik'e Abubakar da Baffa Badamasi ya kankame masa Kai.

Yanzu itace Silar Jefa Hajjo da Baffa Badamasi a cikin wanan Halin idan suka san itace Silar abinda ya same shi Zasu yafe mata kuwa? dan Duk da tasan Suna Kaunarta kamar 'yar da suka Haifa a cikin su amma Sai Sun fi San Jininsu akanta.

Ganin babu mai k'ok'arin Kai Abubakar Asibiti a cikin su sabida tsananin Rud'ewa yasa Tayi waje da gudu ta Nufi B'angaren Abba Surajo.

Ko Sallama batayi ba cikin Kuka ta hau kwalla Kiran " Abba Abba Abba"

Yar rige rigen fitowa Zainab da Abba Surajon Sukayi.

Jawaheer cikin Kuka ta ringa nuna masa waje tana kiran Sunan "Yaya Abubakar"

Aguje Abba Surajo  Yayi Waje Zainab kuma ta tab'e Baki tana "Mai Ya Samu Abubakar d'in?

Kukan daya ci K'arfinta ne ya hanata Magana

Zainab taja tsaki tana " Wawiya kawai ji yanda take kuka kamar Uwarta ce ta mutu ko da yake bazan yi mamaki ba ai tunda yayanki ne wani Abu ya same shi"

Jawaheer Waje Tayi da Sauri dan ta biyewa Mahaifiyar tata haka zata Tayi ta Fad'ar Maganganu ta hanata Tafiya.

Tana zuwa taga Baffa Badamasi da Abba Surajo sun kinkimo Abubakar sunyi Waje dashi Hajjo kuwa ta  biyo bayansu tana Share Hawaye itama da Saurinta tabi bayansu  adai dai lokacin da suka saka Abubakar a bayan Taxi suka shige cikin Motar suka Tafi.

Hajjo ta tare musu Wani suka bisu a baya.

A  babban Private Hospital Na Eye Medical Centre dake cikin Garin Jos suka kai Abubakar dan  Sun  k'ware akan duba ido Wanda har daga wasu Garuruwan ana zuwa Sabida sun kware Sosai akan duba ido dan ko jijiyoyin idonka ne sukayi Weak ka daina gani Sosai zasu d'oraka akan Magani Kuma a dace matsalar su kawai Tsada mai k'aramin k'arfi bazai iya zuwa Asibitin ba

Abba Surajo Bai Damu da  tsadar Asibitin ba shi dai  Burinsa ya zamana Babu Abinda ya samu idon Abubakar d'in dan yanda yayo Waje nan yana tsoron Abubakar ya rasa idonsa guda d'aya Weakness d'in dayake Hangowa a jikin Baffa Badamasi yafi komai d'aga masa hankali baya san abinda Zai jefa Shi a cikin Damuwa dan Zai iya komai ko da Zai zamana ya sadaukar da farincikinsa ne Zai yi dan ya farantawa Baffa Badamasi Rai dan haka shi Zai d'au Nauyin jinyar Abubakar d'in inta kama ya fito da duk Savings d'insa da yafi Shekara biyar yana tare ne zai Tafi a kan Samun Lafiyar Abubakar Sai ya fito dashi dan daidai da abincin da yake ci a gidan sa Baffa Badamasi ne yake d'aukar Nauyinsa har Sutura shi ke yiwa yayansa ya hana shi yak'i Hanuwa inda ya nuna masa yana so ya bar wa yayansu Good Example da zasu taso a haka Suma kansu a had'e.

Suna zuwa aka k'arbi Abubakar akayi Emergency dashi Baffa Surajo kuwa bil hakki da gaskiya  Gani yake kwakulewa Abubakar ido akayi ana shiga dashi ya samu waje d'aya ya Zauna yana Tunanin Wane azzalumi ne haka ya kwakulewa Abubakar ido mai yayi masa haka da zafi a iya Saninsa Jiya da Abubakar ya shiga cikin gidan bai kara fitowa ba har ya shiga gidan ya kulle to ko bayan ya shigo cikin Gidan ya fita ga maganar da Hajjo ta masa na yace mata zaije gidan Abokinsa yayi Karatu to ko canja raayinsa yayi daya gaya mata haka ya shige d'aki yayi kwanciyarsa dan tabbas wajen 12 Suka rabu da Abba Surajo ya kulle gidan bai ga fitowar Abubakar daga Gidan ba har ya shiga cikin gida.

Rana Zafi Inuwa K'unnaWhere stories live. Discover now