*FOUR WRITERS*
*Rana Zafi*🔥
*Inuwa k'una*💥*Na Sadnaf*🎀🎀
*Rana Zafi Inuwa k'unna Sadnaf*
*Zabin Zuciya Umma Yahaya musa (sisin mama*)
*Imtihal Sadnas*
*Rayuwa ta Rahama Na lelle*
*Ga mai Bukatar Fitattu Hud'u Sai ya tura #500 zuwaga wanan acct d'in 2029764071 First Bank ko Recharge Card ta Wanan lambar 08037251895 sai ka turo da Shaidar biya ta layin nan 08033719070 idan daya kakeso 200 karku Sake a Baku labari*
*Page 10*
*Free page*Jawaheer Bata daina d'ari d'ari da Fargaba ba Sai data ga an kwashi Wata biyu Babu abinda Abubakar Yayi Mata Duk da Har lokacin Bata k'ara saka shi a idonta ba Duk da ta Dawo Gaban Mahaifiyarta amma a wajen Hajjo take indai suka dawo Daga Makaranta bama dai Ishashen lokaci dan Karfe Biyu da Rabi suke dawowa Daga Boko Uku su Tafi Islamiyya su taso karfe Shidda a weekends kawai take wuni a gidan Hajjo kuma sosai hakan ke Farantawa Hajjo Rai Duk da tunda abinan Ya faru bata kara jinta daidai ba Sabida Damuwar dake cinta a Rai dan a gaban Idonta Abubakar ya Fand'are bazata iya komai akan sa indai zai Shigo Gidan Sau dubu Sai tayi Masa Nasiha sau dubu amma ta inda Maganar ta yake Shiga ta nan yake fita dan tana Gama magana zaice ya Gode Sai ya tashi ya tafi.
Rabon data ga Dariya a fuskar Abubakar ta manta Kullum fuskarsa kwame take cikin faka fakan glass ga wani Dab'iar da ya koyo ta askin Marasa Tarbiyya Shi da bai fiye saka kananan kaya ba Sai gashi yanzu sune Suturarsa ga wanda ya san shi a baya kallo d'aya Zai masa yasan ya canja gashi kuskure kad'an Su Abba da baffa karami zasuyi ya rufe su da duka.
Sabida d'akin waje da Baffa Badamasi ya mayar shi kamar ciki da Palo suka koma gabad'ayansu cikin Abubakar da Jabeer suka d'auka palon kuma Abba Abba karami da baffa suka d'auka.
Zuwa yanzu Duk sun San yana shan Sigari a ranar da Abba ya fara Ganin yana shan Sigari ya Rik'e Baki Yana "Yaya Sigari kake Sha ba kyau fa"
Abba bai gama rufe baki ba Abubakar yayi Cilli da Karen Sigarin Yayi Ball da Abba Sai ga Bakin Abba ya fashe.
Aikuwa a guje Baffa Kaninsu yaje ya gayawa Hajjo ta yafo mayafinta ta fito.
Warin Sigarin dataji a d'akin su Shi ya tabbatar mata da Zargin da ta dade tana yi Na Abubakar kila ya fara zuke zuke.
Kuka Ranar Hajjo ta wuni tana yi daya kusa Haddasa mata Zazzabi Da kuwa ta tari Baffa Badamasi da zancen.
Ga mamakinta bai Nuna ya damu ba Yace mata Ya Dade da Sanin Yanayi ta kwantar da hankalinta ta daina Saka damuwa a ranta ta cigaba da addua kawai Akan Allah ya shiryeshi tunda Shi kadai ne ya Canja a cikinsu Sauran Suna nan da tarbiyyar da suka musu.
Baffa Badamasi kuwa babu wanda ya kai shi Damuwa da Halin da Abubakar yake ciki Jarumtaka kawai yake yi yake danne damuwarsa Babu wanda yasan damuwarsa Sai Abba Surajo dan Musamman ya Samu Abubakar a d'akin su daya ga babu kowa yayi ta mishi Nasiha shine har da cewa ba dan basa son shi suka goyi bayan Jawaheer ba Kuskurensa suka nuna mishi kuma a rayuwa dole ka k'i naka duniya ta so shi ko kuma kaso naka duniya tak'i shi ya kara da tunda wanan lalurar ta Same shi kar yayi tunanin ya samu Nakasa ne a rayuwa kar ya manta da Yayi Karatun Zamani daidai gwargwado Sannan yana da ilimin Addini yanzu tunda Wanan lalurar ta Same shi yanzu ya ringa bin shi Kasuwa idan ma yana ganin baya san irin Kasuwancinsa Zai Bud'e mishi Shago ya zuba masa Duk abinda yake so ya ringa Siyarwa Daga baya ya Samo mata yayi mishi Aure ko a haya ne ya fara Zama kafin ya samu Gidan Kansa.
Yanda Abubakar ya Nutsu yana jin Baffa Badamasi Tunani zakayi Nasiharsa yake d'auka Sai daya gama Magana tsaf.
Abubakar ya d'ago Idonsa Guda d'aya Yana