*FOUR WRITERS*
*Rana Zafi*🔥
*Inuwa k'una*💥*Na Sadnaf*🎀🎀
*Rana Zafi Inuwa k'unna Sadnaf*
*Zabin Zuciya Umma Yahaya musa (sisin mama*)
*Imtihal Sadnas*
*Rayuwa ta Rahama Na lelle*
*Ga mai Bukatar Fitattu Hud'u Sai ya tura #500 zuwaga wanan acct d'in 2029764071 First Bank ko Recharge Card ta Wanan lambar 08037251895 sai ka turo da Shaidar biya ta layin nan 08033719070 idan daya kakeso 200 karku Sake a Baku labarin*
*Page 5*
*Free Page*Tana kwanciya kuwa bacci ya d'auketa Sabida bata da Fargaban Akwai mai shigo mata d'aki.
Ana kiran Sallah Asuba ta fad'a Toilet Tayi Alwala ta gabatar da Nafila Raka'a biyu kafin lokacin Sallar yayi.
Sai da gari ya fara Haske bayan ta ja dogon addua akan Allah ya karkato mata da hankalin Mahaifiyarta kanta ya kuma tsareta daga Sharrin Abubakar ta Shafa ta mik'e ta cire Hijabinta Tayi Waje dan ta saba idan ta tashi bata komawa bacci Sai ta gyara ko'ina ta d'ora Breakfast wani zubin kafin 7 ma ta gama abinda zatayi Sai dai Aisha kawai tazo ta tarar da ta gama komai.
Kamar yanda Tayi tsamani kuwa babu wanda ya tashi daga Gidan Haka ne yasa ta shiga kitchen ganin Akwai doya da komai da ake Bukata ta feraye doya yanda zai ishesu ta d'ora akan Wuta ganin akwai ganda a dafenta had'ine kawai baa yi masa ba yasa ta maida gandar kan wuta ta zuba masa kayan hadi komai da komai ta rufe ta barshi yayi ta Dahuwa.
Tana Girki tana Gyaran Gidan ahaka wajen 7::15 ta gama komai ta juye ruwan zafin da zasu sha Tea d'in a flask ta rufo kitchen d'in dan taje Tayi Wanka.
Ta nufi d'akinsu Nana Zainab ta fito da ga d'akin Abba Surajon Idonta fal bacci da alama ma Abba Surajon ne ya tasheta Ganin ko'ina tsaf sai kamshi dake tashi yasa ta ware ido tana kallon ko'ina palon kuwa sai tashin kamshi yake ga flask da aka jera da kofuna a tsakiyar carpet.
Mamaki ne ya rufeta dan yanzu tana ta tunanin abinda zata yiwa Yaran da zasuci su tafi kar su makara inda Tayi tunanin dafa musu kawai indomie suci su tafi.
San yara bai bari ta koya musu girki ba ita take abinta da kanta ta basu suci wanda a ganinta Gata take yiwa su Nanan
Da dai da gyaran gida ita take yi bata saka su shiyasa wani zubin Abba Surajo ke mata fad'a akan ba Gata take musu ba karta manta mata ne kuma gidan wani zasuje dolensu su ringa yi.
Indai Su Nana sun yi wani Abu a gidan to Abba Surajo ne ya sakasu.
Sosai taji dadin aikin da Jawaheer ta rage mata amma a fili kuwa d'aure Fuska Tayi tana tab'e baki.
Jawaheer data Sunkuyar da kai tunda ta fito ganin tana tab'e Baki yasa ta Tsugunna tana "Umma Ina Kwana Allah yasa ban b'ata miki Rai ba Doya na soya Sai ferfesun gandan Dana Gani da Shayi naga kamar doyan sai yafi rik'e ciki akan Indomie da zan jira har ki fito ki fad'amin abinda zanyi sai kuma naga zamu iya Makara"
Tunda ta fara Magana Zainab ta saki baki tana kallonta cikin tsananin mamaki Girgiza kai Tayi tana " A yanzu kika soya doya da kwai har da ferfesu dasu Shayi har dasu gyaran gida ikon Allah"
Zainab tace tana tafa Hannuwa tare da gyara Zama akan kujera tana kallon jawaheer da take tunanin ko Laifi Tayi da bata jira Anyi mata umarni ba.
"Haba Ashe Aisha Bautar min da 'ya take Shiyasa ta dage ta rik'e ta Ashe Aisha 'yar aiki ta maidaki bansani ba idan ba jaka ta maidaki ba a yaushe mutum daga sallar asuba Zai yi irin wanan aikin cikin k'aramin lokaci Jawaheer kinga abinda kika jawa kanki ko ke yanzu daki dawo gabana ki dawo cikin 'yan uwanki kin Gwammace Aisha Tayi ta Bautar dake Aisha ta Cuceni Ashe ba dan Allah ta rik'e ki ba dan ta ringa azabtar dake ta Rik'e ki yanzu idan nayi Magana sai ace bana san Zaman lafiya yanzu ni na isa na saka Abubakar ko Jabeer suyimin irin wanan Bautar da kike musu to ai shikenan Jawaheer kije kiyi Tayi ga kananenki nan a cikin gatansu babu wanda yake Bautar dasu Allah ya Baku Sa'a kallonku nake ke da ita wlh idan kuka kaini bango zan d'au mataki akanku dan babu shegen Dana haifawa ke da zai ringa nuna min isa akanki in bake ba ban tab'a ganin wacce ta guji Mahaifiyarta ta zabi wata ba idan ma Surkullensu na Fulani Tayi miki zaki dawo Hayyacinki ne"
