*FOUR WRITERS*
*Rana Zafi*🔥
*Inuwa k'una*💥*Na Sadnaf*🎀🎀
*Rana Zafi Inuwa k'unna Sadnaf*
*Zabin Zuciya Umma Yahaya musa (sisin mama*)
*Imtihal Sadnas*
*Rayuwa ta Rahama Na lelle*
*Ga mai Bukatar Fitattu Hud'u Sai ya tura #500 zuwaga wanan acct d'in 2029764071 First Bank ko Recharge Card ta Wanan lambar 08037251895 sai ka turo da Shaidar biya ta layin nan 08033719070 idan daya kakeso 200 karku Sake a Baku labarin*
*Page 3*
*Free page*"Ni Ka Saka Surajo"?
Zainab tace tana nuna kanta gabanta na d'an Fad'uwa Dan bata tab'a Tunanin Surajon Zai Saketa ba
Tsaki Surajo yayi ya tattara Su Nana ya shige dasu d'akinsa yana banko mata K'ofa har ga Allah Zainab ta dade da Ficewa daga Ransa Duk zaman nan da yake da ita Hakuri yake yi Duk Yanda ya kai ga ya B'oyewa Badamasi Halin da yake ciki sai daya Gane da kansa ya kuma Yi mishi Nasiha daya cigaba da Hakuri shi ya hana ya k'ara Aure tuntun da tunin ya mata kishiya ko a yanzu daya saketa Sam baiyi Nadamar Sakin daya mata ba.
Zainab kuwa Sabida Girman Kai bata nemi su sulhunta ya maidata D'akinta ba ta d'au Hijabinta ta tafi Gidansu.
Mahaifiyarta Ido kawai ta zuba mata a lokacin data gama fad'a mata Gaskiya da Karyar abinda Yasa Surajo ya saketa inda Hanne tace " Ai Surajo ma yayi k'ok'ari ba kad'an ba da sai A yanzu ya sakeki na dade ina zuba idon dawowarki Gidanan da Sunan Sakakiya Sabida ba kowa ne Zai Jure irin Halinki ba Sai Surajon da Allah ya bawa Hakuri toh Sai Kizo ki Samu waje mu zauna dama kadaici ya isheni haka nan Sai na Sakar miki ayyukan Gidan ki cigaba da yi Kosai da Awaran Yamma da nake Fama dashi na huta yanzu Sai ki d'ora daga Inda na tsaya"
Zainab sakin Baki tayi tana Kallon Hanne jin maganganun daya ke fitowa daga bakinta bata san lokacin data Fashe da kukan B'akin ciki ba tana "Haba Inna baki ji mai nace ba Sakina fa akayi a madadin kisan Yanda zakiyi na koma d'akina ki kira Surajo ki bashi Hakuri ya maidani d'akina shine zaki fara Lissafin Yanda zan ringa tayaki siyar da awara da kosai"?
" Kinci ubanki Zainab"
Hanne tace a Fusace Fuskarta na Bayyana B'acin ran data Danne tunda Zainab ta shigo gidan tana kora mata jawabin Sakin da aka mata
"Bazan kira Surajo nace ya maidaki ba Zainab ba dai bakya jin Magana ba bazaki gyara Halinki ba wlh indai k'unci ne yanzu kika fara shiga ba baki nayi miki ba Na d'auka zakiyi Hankali da kika Yi Aure na d'auka da kika hayayyafa zaki yi hankali Ashe bazaki tab'a hankali ba Ina ruwanki Dan ya bad'a Jawaheer ga yayansa?Siyar da ita yayi da zaki masa wanan cin mutuncin ko kin manta yafiki iko da ita Zainab wanan bashine Tarbiyyar Dana Baku ba wlh bansan a ina kika kwaso Halinki ba Duk d'ibar Albarkar da kike yiwa matar yayan mijin ki wlh inada labari kallonki kawai nake tunda kin kashe Aurenki kin dawo Gida sai Kizo mu zauna duniya ta koya miki hankali amma haram in kira Surajo akan ya maidaki Shashasha kawai maza tashi ki Surfa min wake Dan wlh ke zakiyi aikin Gidanan"
Daga haka Hanne ta tashi ta shige d'aki tabar Zainab na gunshek'en kuka.
A cikin kwana Biyu Zainab tabi ta fice daga Hayyacinta Kwana biyu kawai tayi a gidansu amma gani take tafi Shekara dubu a gidan ko baccin kirki bata iya yi ga izayar da Hanne ke gana. Mata Sam bata barinta ta Huta katifa biyu ne a d'akin amma tanaji tana Gani Hanne ta dage sai dai ta kwanta a kasa bazata kwanta mata a katifa ba.
Karfi da yaji ta fara Addua Allah ya kawo Surajo ya maidata D'akinta Dan bazata iya wanan Rayuwar ba tayi danasanin abinda tayi yafi a kirga gashi lokacin babu waya balle ta nemeshi ta bashi Hakuri.
