*Rana Zafi*🔥
*Inuwa k'una*💥*Na Sadnaf*🎀🎀
*Page 2*
*Free page*Malam Inuwa da Amina sune asalin sunan iyayen Badamasi da Surajo asalin su yan yobe ne yanayin kasuwan shi shiya mayar da Malam Inuwa Jos kasancewar shi manomin kayan lambu irinsu dankalin turawa, haka dai suke rayuwar su cikin rufin asiri har zuwa lokacin da Badamasi da Surajo suka gama makarantar primary a lokacin ne sai Badamasi ya nuna yafi ra'ayin sana'ar mahaifin su noma inda Surajo kuma ya nuna shi karatun shi yakeso yaci gaba, Malam Inuwa bai takurawa d'aya a cikin su akan sai yabi ra'ayin d'an uwanshi ba anan yayi musu fatan nassara a dukkan al'amuran su daga nan suka fara tafiya gona shida Badamasi in kayan da suka noma sunyi 'ya'ya kuma ya cire amfanin gonar da Badamasi suke kwasar kayan zuwa sauran garuruwa domin siyar da amfanin gonar zuwa lokacin tuni idanuwan Badamasi sun bud'e a harkar kasuwancin nashi.
Inda kuma duk wani ciku-ciku daya kamata ayiwa Surajo na tafiya makaranta Malam Inuwa yayi na kud'i kuma ya biya haka shima ya fara zuwa makarantar shi kuma Alhamdllh yana fahimtar karatun sosai saboda daman shine burin shi (jan hankali ga iyaye kamata kuna karfafawa yaranku gwiwa akan abinda sukeso ta hakane kawai hankalin ka zai kwanta babu ta yadda zaka tursasa yaro yayi abinda bayaso kuma kayi tunanin zaka samu abinda kakeso).
Haka rayuwa taci gaba da tafiya inda girma ya fara kama Malam Inuwa saiya zamana Badamasi ke kula da harkokin kasuwancin kasancewar lokacin yana da shekara 28 Surajo kuma yana da shekara 26 zuwa lokacin ya gama secondary school d'inshi harya fara university d'inshi anan cikin jos.
A harkar kai kayan nomar da Badamasi ke kaiwa wataran abokin shi yayi mishi tayin sukai yola koda ya sanar da Malam Inuwa a take ya amince mishi da fatan Allah yasa suje a sa'a haka suka shirya suka tafi bayan sunje sun saida duk kayan su da suka kai, a lokacin ne wata yarinya Aisha take kai musu tallan nono bafulatana ce batafi shekara 15 ba tun kawo musu nono na farko Badamasi yaji yana k'aunar yarinyar Sabida yadda yarinyar take da nutsuwa ga kunya tun kafin subar Yola Badamasi ya bayyana mata kudirin shi kuma baiyi k'asa a gwiwa ba wajen zuwa ya gaida iyayenta yaje ya gaishe su kuma suma sunyi na'am dashi.
Bayan dawowar Badamasi da kwana 2 ya samu mahaifin shi ya sanar mishi ya samu matar da yakeso sannan ya sanar da shi a inda suke Malam Inuwa yaji dad'i sosai dan ya dade yana yiwa Badamasi Zancen yayi Aure yana wani nok'ewa a take ya aika Badamasi gurin Baffannin shi dake Yobe ya sanar musu inda sukace za suzo dan suje nema mishi aure kamar yadda Malam Inuwa yace.
Hakance kuwa ta kasance bayan kwana 2 sai ga yan Yobe sunzo kwanansu d'aya suka shirya suka tafi Yola da rakiyar Abokin Badamasi bayan zuwansu tarb'a me kyau suka samu bayan gaishe-gaishe anan suka fad'i abin daya kawosu a take iyayen Aisha sukayi na'am da k'udirin nasu basu taho ba saida suka saka ranar biki nan suka baro garin cikin farin ciki.
Lokacin da suka dawo suka sanarwa Badamasi farin cikin shi kasa b'oyuwa yayi saboda ba k'aramin so yake yiwa Aisha ba kasancewar itace macen da idanuwan shi suka fara tozali dashi har ya iya furta mata kalmar so, gidan da Malam Inuwa ya siya guda 2 ne gidajen a jere daman ya siya ne domin yaran nashi ba wasu manya bane gidanen d'akuna 3 ne a cikin ko wanne gida sai kitchen sai band'aki a take ya d'auko muk'ullin na Badamasi ya bashi da takardun yana "na godewa Allah daya bani ikon ganin wannan lokaci na auren ka saura auta" ya k'arasa da murmushi a fuskar shi dariya Surajo yayi jin furucin mahaifin yace "Baffa ai nikam aure ba yanzu ba sai nayi degree nayi masters na samu aiki saina fara tunanin aure" cikin dariya Badamasi yace "ai kayi mai wuyar tunda ka saka lokaci konan da shekara 10 ne ranar ai zatazo" Inna ce tace "wannan haka yake duk abinda aka sakawa rana zaizo" Baffa yace "tabbas Allah yayi muku albarka ya k'ara had'e kawunan ku" da "ameen" suka amsa.
