Part 4/5

534 32 0
                                    

🐲🐲🐲
          UQUBAR UWAR MIJINA
🐲🐲🐲
(Based On True Life Story)(Full of Sorrow)

Story Nd Written By
Khadeejaht Hydar
Young Novelist

✍✍✍✍✍✍✍✍
GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION
✍✍✍✍✍✍✍✍

❄We are bearers of soo golden a gun, we write assiduously perceive no pain, so magical our creative golden pen, be hold our words, A product of our pen savour our words for it will cause u no pain❄

Dedicated to
ABDOOOUUL❤🔥One love 4 ur care nd prayers.

(4)&(5)
Ana saura sati d'aya biki ,lokacin angama wani shirye shirye komai ya kammala lokaci kawai  ake jira.

Yau takama laraba duk wani dangi nawa sun iso,wasuma daga guri mai nisa amma har sun iso,hak'ik'a naji dad'in ganinsu.

Washe  gari alhamis yakama saka lalle,haka akasamin lalle ma a al'adance.

Washe gari da safe ran juma'a jama'a suka shaida d'aurin aurena da Khamis Wanda d'aurin auren yasamu halartar mutane dayawa daga ko'ina saboda Alhamduliilah Baba na yanada jama'a.

Ba'ayi wata bidi'a ba  amma anyi walima anci ansha an k'ayatar,muna dawowa gida na shirya cikin shadda mai tsada da sark'ar gwal da d'ankunne da abin hannu duk iri d'aya.

Haka akazo tafiya dani amma fir nak'i fita ina kukan rabuwa da iyayena ,haka naje na rungumi Ummana ina kuka kamar anmin mutuwa itama kuka take tanamin fatan Allah yazaunar dani lafiya yakareni  daga sharri.

Haka aka turani cikin mota aka kaini gidana wanda babu nisa da na surukata,toh Bayan anshigar dani d'akina na shiga da k'afar da k'afar dama nayi nafila kamar yadda malamai suka nuna.

Bayan kowa ya wuce ne ango ya shigo tare da abokansa ,bayan sunyi nasihohinsu da sauransu suma suka wuce,bayan duk wani abinda musulunci ya tanada.

Alhamduliilah angona yasameni cikakkiyar budurwa,Wanda hakan yasashi k'ara mini wani girma a zuciyarsa.

Da safe daga gidan Mahaifiyarsa aka kawomana abinci,toh nikam ganin haka yasa naji inason uwarmijina nace"....Ashe abinda ake fad'a akanta ba gaskiya bane.

Uhmm karkiyi saurin yanke hukunci Fatee Ba'anan gizo ke sak'a ba

Haka rayuwa take tafiya cikin lafiya da kwanciyar hankali,har nayi sati Mahaifiyarsa ce ke aiko mana da abinci.

Bayan sati d'aya ne nafara girki,inda na girka abinci na aika mata dashi harta aikomin da sak'on gaisuwa.

Bayan wata d'aya da auranmu naje gaida uwar mijina,munsameta a zaune a parlour tana kallo.

Har kasa na tsuguna na gaidata ta amsa fuska babu walwala,gaba nane fad'i nace"....to meke shirin faruwa ne?.

Haka bandad'eba na koma gida saboda Sam kallon datake Nina dashi bangane masa ba,tundaga ranar bansake zuwa ba saboda ni mutum ce mai tsoron zuciya da hak'uri.

Cikin ikon Allah falalar arziki tafara bud'ewa mijina,to rannan yaje gun wani Malami don kaiwa sadaqa.

Bayan sun gaisa da Malamin,saboda a matsayin  kawu yake agunsa,se yace masa Khamis  zan fad'a maka wata magana matarka itace silar  da ubangiji yasa kakesamun falala matarka tana d'auke da arziki ga duk namijin daya aureta kuma Bayan haka matarka alkhairi ce ga rayuwarka don haka ka rik'eta hannu biyu don ita ba abin wulak'antawa bace.

Godiya ya masa yana mejin dad'i ya samu mata mai rik'on Addini ga sanin yakamata,daya dawo gida ma cikin farinciki yake.

Toh bayan Wata shida da auranmu  abubuwa suka fara canzawa daga uwar mijina saboda sam yanzu ta tsiri wani hali saita zo gidana tayini tana masifa,koda yayi niyyaryin magan sai inmasa nuni daya bari saboda ita mmahaifiyace,kuma ni duk abinda takemin bantaba nuna damuwa taba.

Toh akwai ranar datazo ta tarar banda lafiya,a maimakon ta tausayamin saita rufeni da duka wai tazo ko ruwa ban bataba.

Tana cikin dukana gashi ni nakasa tashi,sai Allah ya kawo Khamis tana ganinshi tafara kukan munafirci wai tazo nace ta koma ai ba gidan ubanta bane.

Sanin halinta kuma ana tsaye akayi batare da sanintaba yasashi fara bata hak'uri,dakyar ta hak'ura ta tafi.

Shikuma guna yazo a hankali yace"....Dan Allah Fatima kiyi hak'uri ban aureki ba saida uwata ta yarjemin kuma don ina sonki plss kina hak'uri WATARANA SAI LABARI.

A hankali nace ba komai ya wuce,yace"....meke damunkine?,nace"....ciwon ciki nake amma yanzu da sauk'i,shiya taimakamin na dafa mana abinci mai sauri sannan nasha magani muka kwanta.

Ku kasance tare da Young Novelist.

Comment .
Like.
Share.

🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎
Royal Blood Typing
🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎

UQUBAR UWAR MIJINAWhere stories live. Discover now