Part 6/7

501 26 0
                                    

~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*

*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*

🐲🐲🐲
          UQUBAR UWAR MIJINA
🐲🐲🐲
(Based on true Life Story)(Full of Sorrow)



Story Nd Written By
Khadeejaht Hydar
Young Novelist

Dedicated to
Zee xynab Ht u much,tnx 4 everitin. 1 love to u My Zeeta.

(6)&(7)

Da safe ciwona yayi tsanani hankali a tashe muka nufi asibiti, gwajin farko aka tabbatar mana ina d'auke da juna biyu har na tsawon sati uku.

Murna gun Khamis kamar ya zuba ruwa a k'asa yasha,ba laifi Mahaifiyarsa ma tayi murna da samun cikin wanda hakan yasa ta d'an sassauta mugun halinta akaina.

Wani gamin kuma tana aikomin da abinci ko na safe ko na rana wani gamin kuma na dare,Uhm ni Fatima da nasani dabanci  abincinba.

A rashin sanina ashe Uwar   mijina bokaye da Malamai take bi don ta raba aurena,da kuma tasaka rayuwata cikin garari da taskun bak'inciki da tashin hankali.

Ita a tunaninta wai ya koma k'ark'ashina yana bautamin yana kashemin kud'i,batasan  cewa bani k'adai zata cuta ba harma da d'anta amma tabbas tafi cutata.

Haka muke rainon cikinmu kuma tana kayomin abinci inaci,donma daga gida ana kawomin rubuta.

Ita ala dole kada na haifi abinda ke cikina,balantana na haifi namiji  yazama shine zaici gado ba'ita ba.

Fans kunji abinda yasa wasu basason uwarmiji fa,Ku kalli yadda take shirin tarwatsa Y'ar mutane.

Sai isa inzakiyi aure ka rok'i zabin Allah,don wasu uwarmijin su batada matsala ze iya kasancewa  Y'an uwan mijinne,kuma kome uwar miji zata miki ki kasance mai hak'uri kamar yadda Fatima tayi to inma ta cuceki Allah ze saka miki.

Amma tabbas uwar miji uwace,kuma abin ayaba mata ne,abin a kyautata matane,abin a tarayrayetane,kuma a kula da'ita Allah yabamu iyayen  MIJI na gari Masu maye mana gurbin iyayenmu.


Cikin ikon Allah na haifi y'ata mace,kyekyawa kamar balarabiya saboda Khamis ma ba bayaba gun kyau da haske.

Ranar suna taci sunan mahaifiyata saboda Sam mahaifiyarsa tak'i yarda asa sunanta,ko miye dalilinta bansaniba.

Haka rayuwa take tafiyar mana cikin jin dad'i  har nayi arba'in,to lokacin ne Mama wutar  tsanar datakemin   tasake ruruwa.

Saboda ko zuwa gunta nayi bata d'aukar y'ata,hakanma yasa Khamis yahanani zuwa gidan ta.

Akwai ranar   datazo gidanmu da sassafe tanata fad'a, a lokacin Ilham tana rarrafe sai taje gunta tana tab'ata.

Wata tsawa ta daka mata saikace wata babba,wani razanannan ihu Ilham tayi sainaji tayi shiru ashe suma tayi.


Tundaga rannan bansake bari Ilham ta sake zuwa gunta ba,amma bantaba fad'awa mijina ba saboda naga yana k'ok'ari ganin bantakuraba kuma banason hankalinsa  ya tashi.

Aranar da Y'ata ta shiga shekara d'aya,a ranar natafi gidanmu kuma aranarne uwar Mijina tasamu nasarar binne wani sihiri a k'ofar parlour na,kuma sihirin  bana mutum d'aya b.

Saboda daman tana neman hanya Malamai sunce mata asiri baze kama niba,aljani baze iya kusanta taba,saboda ina da addu'a   kuma Iyayena suna min Addu'a.

Saida yamma na dawo,saida na taka inda asirin yake tukun na naje inda zan bud'e na shiga parlour.

Ina shiga parlourn naji kaina yayi nauyi jikina yafara rawa,da sauri na zauna ina addu'a dakyar nasamu nutsuwa nashige d'akina.

Se bayan magrib yadawo Bayan na gabatar masa da abinci yaci,amma yanayinsa na yau ya canza ko d'aukar yarinyar beyiba ita kuma sai mik'a hannu take don ya d'auket,amma sam babu walwala a fuskarsa.

Gaba nane ya fad'i saboda be tab'ayimin haka ba,koda wani ya bat'a masa rai baya zuwa gida da fushi.

Bayan mun gama cin abincin mun koma parlour,na zauna kusa dashi nace".....Baban Ilham meyafaru ne yau naganka haka?,yace".....bakomai mekika gani. "

Tace".....naga kamar ranka a bac'e,yace".... A'a bakomai seda safe daganan yatafi d'akinsa."

Abinda be tab'a yiba kenan mu raba d'akin kwana,haka na kwanta zuciyata tana zullumin kode nice na masa laifi amma nayanke shawarar gobe zan tambayesa.

Da safe bayan nagama komai nayi wanka nayi kwalliya har k'arfe goma banga alamar saba,nan naje d'akinsa don naduba ko lafiya.

Da sallama nashiga amma me wayam babu kowa,na d'an saurara ko zanji alamar yana band'aki amma shiru kakeji.

Haka na fito jiki a sanyaye ina tunanin har girman laifin danayi yakai yafita babu sallama,nace"....ko de ya fita ina  barcine aikin  gaggawa Yaka masa?.

Haka muka wuni Allah ma yasa  munada kayan abinci,muna kwance nasaka k'ira'a a parlour naga mutum akaina.


Da  sauri na tashi ina gaidata amma ko kulani batayiba se cewa tayi ina d'ana yake,nace"...Mama da sassafe ya fita,a tsawace tace"....inason ganinsa yanzu."

Zanyi magana se gashi ya shigo ,tace"....Alhamduliilah d'an albarka daman kai nazo nema, so nake yanzu base yau ba ka saki yarinyarnan.

K'arasowa yayi ya gaidata tace"....sannu d'an albarka,tace"...so nake ka saki wannan  Mara tarbiyyar mara mutuncin.


A hankali yace"....Mama dan Allah kiyi hak'uri inason matata,tace"....lallema ninakemaka magana  kakemin musu,eh hakane tagama dakai nayarda daganan ta juya ta fice tace"....zan dawo kuma saikinbar gidannan."

 
A hankali yace".....kiyi hak'uri Fatima nima daga jiya zuwa yau bansan meke damuna ba,nace bakomai Allah ya shige mana gaba."

Yace".....karki damu da maganar Mama muna tare  dake nace".... Insha Allah.

Muje zuwa.
Ku kasance yare da Young Novelist.

🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎
ROYAL BLOOD TYPING
🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎

UQUBAR UWAR MIJINAWhere stories live. Discover now