*RAYUWAR DARAKHSHAAN*
_True life story_*mallakar*
👇🏻
*OUM MUMTAZ*_Wattpad@ummie2018_
_Instagram @Itz me real oum mumtaz_
_Facebook @ oum mumtaz_
G-mail: fatimafateh5@gmail.com
*_WAnnan littafin da farko nayi niyyar nayi shi a matsayin na kud'i!! amma kuma sbd wasu dalilai ne yasa na maishe sa a matsayin free book!! so dan haka idan har naga kuna zuba man sharhi yadda ya kamata da yaddar Allah bazan baku kunya ba,domin kuwa wannan littafin true life story ne daya faru da gaske akan wasu yammata guda biyu! wanda kuma muke fama da irin wayannan cases din cikin al'ummar mu! idan har kuna bibiye da alk'alami na akan wannan littafin pls shawara nake bukata akan dik wasu abinda kaci karo da shi bawai zagi,tsinuwa da dai sauran su ba sa aka san readers kanyi a fannin sharhi! ina fatan baza ku bani kunya ba my fan's...?_*
_chapter 1_
Tafiya take cike da yanayinta na kuzari dake tafe da tsantsar natsuwa da kai tsaye mutum bazai iya cewa sauri takeyi ba! hannunta rike da key na motar ta kirar 206 tana karkad'awa fuskar ta shimfide da wadataccen murmushi dake kara fiddo da ainahin sihir taccen kyawunta da bashi da hayaniya!
yarinya ce,amma ba can ba,domin kuwa a shekarun haihuwa zata kai a k'alla shekaru 20 zuwa da daya ne! dik da inda ta ratsa cikin jami'ar tasu tana kutsawa,takan ci karo da mata da maza,wanda kuma sukanyi gaisuwa ta mutunci kadaran kadahan kamin taci gaba da tafiyarta!
saida ta iso kofar hole d'in da suke da lectures kamin taci birki,inda ta tarda student wajen su biyar sunyi cirko cirko,da alamun suma sunyi late ne kamar yadda itama tayi! wanda hakan yasa sam bataji dadin hakan ba! har kuma hakan ya gaza boyuwa bisa ga kyakkyawar fuskarta sbd sanin halin _DR MADAKI_ a fannin zuwa latti sam sam baya shiri da mutum koda kuwa ciki daya kuka fito dashi!
mace daya ce a wurin dik sauran maza ne,gaisawa tayi da su cikin muryarta mai taushi da ba wata mai dadin sauraro bace na azo a gani! amma dai kuma takanyi mamaki a dik lokutan dataji maza da dama kan cewa wai muryarta akoi dadi...?
matsowa tayi zuwa inda dayar student din take sukayi musaba ha cikin sakin fuska yarinyar tace "kice kema da kanki yau kinyi latti _mrs sammako...?_"
girgiza kai kawai tayi hadi dayin murmushi sbd jin batu na class mate din nata kuma kawarta wato _DIYANAH_,domin kuwa ita a karan kanta tasan cewa kaf cikin yan class nasu babu wanda ya kaita iya doka lattin zuwa daukar lecture! wanda kuma tasan daniyah dinma ta fadi hakan sbd shegen tsokala irin nata!
cikin kasa kasa da murya daniyah tace "ya kama ta fa kije ta wajen window ko Allah zaisa mutumin naki idan ya gano ki ya mana alfarmar shigewa sbd kinsan class nashi is very important to us baki dayan mu"
cike da gamsuwa kuma ta gyada mata kai,domin kuwa itama sam bazata so suyi missing na wannan class din ba sbd amfanin dayake dashi gare su!
mazan dake wurin ma sai wani marai raice mata fuska suke sbd sun san idan Allah ya taimake su zasu samu damar shiga idan dr madaki ya gano fuskar muradin zuciyar tasa!
saida ta sai saita fuskarta,ta wani marairaice kamar mai wata ciwon kamin ta matso sosai zuwa jikin window d'in hole din ta laiko kanta! aikuwa kamar hadin baki karaf idanunsu ya sarke cikin na juna tsakanin ta da wani matashin dattijo dake tsaye a jikin board da aka haske shi da projector! yana zuba masu darasi cike da tsantsar kwarewa da kuma iyawa!
dogo ne sosai mutumin,irin masu dirin jiki dinnan da kallo daya mutum idan yayi masa akace ya fasalta shi za'a ce masa dirarren mutum ne!
daliban dake cikin hole din kwata kwatan su basu wuce su 24 ba,wanda kuma kwata kwata matan cikin su guda uku ne,21din kuwa maza ne baki dayan su! duba na tsanaki idan akayi wa daliban za'a fuskanci yanayi na shakka da kuma girmamawa da suke ma wannan lecturer din dake ansa sunan dr madaki mai shekaru 45 da a duniya!