25

263 28 13
                                    

25

       "Wai ina Hidaya take ne?" Aunty ta tambaya tana le'ka d'akin Muneera dake kwance, bata amsa mata ba domin bata ma san tayi tambayar ba tana can duniyar tunani sai Mama ce ta amsa tace "tana can tana d'aukan hotunan Areefah sun shiryata".

"kai, yarannan sunsan munada aiki a gabanmu zasu tafi wasu hotuna? Ya jikin nata". Numfashi Mama ta sauke tace " wannan abun ya fara bani tsoro wallahi Hafsa, yarinya kullum abu sai gaba yake sake yi? Kinga jiya da yau da na mata wanka na fito na barta zama tayi cikin toilet d'in har saida ta bushe, shima dawowa nayi naga bata nan na le'ka na sameta a zaune tana kuka, itama Areefah saboda rashin kulawar da take samu tunda ta haifeta sai tsamurewa takeyi, ace a rana jaririya saidai tasha nono sau biyu zuwa uku shima sai anyi daga da uwar tata? Na kasa gane kan ciwonnan nata". Mama ta 'karashe maganar tamkar zatayi kuka, babbar damuwarta itace yanda Muneera bata mata magana, idan tana so ta san abinda Muneera ke ciki ko take so saidai ta had'ata da Hidaya ita kad'ai ke iya bud'e mata baki tayi magana.

Banda ramewa da lalacewa babu abinda Muneera tayi a kwanaki biyar da haihuwarta. Bata cin abinci sai Mama ta sakata gaba ko kuma Hidaya ta lalla'bata, ga rashin zuwan yusuf ya sake 'kara mata damuwa. Duk uban da 'yarsa zatayi kwana biyar a duniya bai zo yaga lafiyarta ba baza'a kirashi a uba ba, to menene amfanin rayuwarta da ta  Areefah idan har Yusuf bazai damu dasu ba?

Hajiyar yusuf da 'kannensa sunzo sun ga jaririya sannan suka sanar musu zasu dawo a yau su kawo kayan barka, wannan yasa Aunty ke ta shige da fice wajen ganin ta had'a musu abinci mai kyau da su da 'yan barkar dake yawan zuwa gidan domin gida baya rabo da mutane.

"To yaya kinyi maganar samar mata magani amma banji kin sake cewa komai ba".

Kallon Aunty Mama tayi tace " wallahi inaso na nema mata maganin shaid'anu da na mayu da sammu domin inada tabbacin a cikin ukunnan ne, to amma Hafsa banaso kowa ya san halin da yarinyarnan ke ciki ina gudun dariyar mutane".

Zama Aunty tayi tace " Yaya lafiya na gaba da komai kuma addu'a itace maganin kowane matsala, duk wanda zai maka dariya saboda ciwo ya same ka baisan shi da wani irin ciwo Allah zai jarabceshi ba. Zanyi waya garinmu na sanar musu su tahomin da maganin kinsan mu jeji ba'a rasa magunguna, idan akayi sa'a aka dace shikenan ba sai kowa yaji ba sai kuma a had'a mata da addu'o'i".

Godiya sosai Mama take ma Aunty har saida aunty taji kunya, tashi tayi taje ta kar'bi Areefah a hannun su Hidaya ta goyata sannan tace suyi abinda ya kamata, ba don ransu naso ba suka tashi suka shiga ayyukansu.

Bayan sun gama sunyi wanka suka nufi d'akin Muneera, tana zaune gaban wardrobe d'inta ta zuba mata idanu, saida Hidaya ta kira sunanta sau uku sannan ta juyo tace "oh banji shogowarku ba".

"Muneera banason tunaninnan da kikeyi please, you have to take it easy nasani kina cikin damuwa amma a yanzu yawan tunanin da kike zai iya jefaki cikin matsala, dan Allah Muneera ko dan Areefah ki rage ma kanki wannan tunanin".

'kwalla ce ta zubo mata ta har ta bud'e baki zatayi magana ta kalli zee tayi shiru, tashi zainab tayi ta fita ta barsu su biyu. Cikin kulawa Hidaya tace "yanzu sai ki fad'amin me kikeji".

"Hidaya babu abinda banaji, a yanzu kuka ne kawai abinda yake min dad'i idan kika tambayeni ya ake murmushi ko dariya ma na manta saidai na gani Kuna yi".

Hugging d'inta Hidaya tayi tace " kowane tsanani yana tare da sau'ki twinnie, Allah is testing your imaan amma ke kina 'ko'karin ki gaza cin wannan jarrabawa tashi, naji idan Yusuf yayi maki laifi menene laifin Areefah? "

Shiru tayi tareda juyar da kanta tace " ban sani ba".

Fita Hidaya tayi ta kar'bo Areefah ta dawo ta zauna tace "wannan yarinyar tazo duniya ba tareda sanin komai ba, amma kinsan me kike koya mata a matsayinki na uwa? 'kiyayya da 'kullata. Kina tunanin 'yar da uwarta take gudunta zata tashi ta zamo tana son mutane nan gaba? Kina tunanin idan kika cigaba da gudun Areefah zata nuna miki soyayya a lokacin da kike bu'katarta? "

WITHOUT MY DREAMS (HAUSA NOVEL)✔️Where stories live. Discover now