44

63 23 0
                                    

WITHOUT MY DREAMS

44

Jikin Hidaya a sanyaye ko taya Aunty aikin ta kasa yi yau saboda kalaman da taji daga mama, dukda taji abinda ya faru amma sam Aunty bata nuna mata ba hasali ma murmushi tayi tace "yanzu muke hirarku da Yaya, maza duba fridge kiga akwai 'kan'kara mai yawa". Sam Aunty bata bata fuskar tambayarta abinda ke faruwa ba haka suka cigaba da ayyukansu tunani kala-kala fal a zuciyar Hidaya, ga tunanin mahaifiyar Jawad ga na Mama.

Ranar bata da lectures hakan ya sanya ta koma part d'in su Muneera suka zauna suka fara hira. Tambayarta Muneera tayi tace "ya kuwa matsalarku da Jawad ina fata kun sasanta". Shiru Hidaya tayi na dan lokaci tana tunanin irin amsar da zata bata, sunyi sha'kuwar da ba zata iya mata 'karya ba amma kuma shawarar da Aunty ta bata abin dubawa ce, bai kamata ta 'karawa Muneera damuwa akan damuwarta ba musamman yanzu da ta rabu da Aaseem akan dalilin da Hidaya ta kasa ganewa, duk tambayar da ta mata ta kasa bata gamsasshiyar amsa. Idan har zata 'boye mata abinda ke ranta itama ya kamata ta iya bakinta. Numfashi ta sauke tace "eh mun sasanta yau ma Ammi zata zo suyi magana da Aunty akan lokacin da za'a tsaida".

Gaba d'aya Muneera ta maida hankalinta ga Hidaya wani sashi na zuciyarta na farin ciki da samun nutsuwar da Hidaya tayi wani sashi kuma yana akasin hakan, saidai ta d'auki abinda take ji a matsayin kewa ganin zata yi nisa da twinnie d'inta. Mama dake la'be a 'kofar d'akin 'kirjinta ne yayi wani mugun bugawa ta bar wurin da sauri ta nufi d'akinta, zagaye takeyi a d'akin cikin tashin hankali sannan tace "kai, inaa, bazai yiwu ba, wallahi bazai yiwu ba na rantse da Allah ba za'ayi wannan auren ina raye ba, kan uba? Duk kud'in da na kashe zai tashi a banza kenan?"

Mayafinta ta d'auka ta fito cikin sauri saidai tana fita farfajiyar gidan sukayi kaci'bis da Baba, kallonta yayi yace "ina zakije haka? Bayan Hafsa tace min akwai b'akin da zasu zo?" Kai tsaye ta shirgo 'karya domin yanzu ta zama professional a yiwa Baba 'karya tace "Alhaji ba'ki kuma? Ba uwar saurayin Hidaya ce zata zo ba ni ko me zan zauna nayi mata? Ba nisa zanyi ba barka zan le'ka yarinyar 'kawata ta haihu". Kallonta baba yayi sannan ya girgiza kai yace "sai kin dawo, amma kafin ki tafi yarinyarnan Muneera, naga ta fara dare a waje". A fusace Mama tace "wai Alhaji meyasa kake min haka ne iyi? Wani irin dare ne Hidaya bata kai a waje ba kuma ta dawo tace daga makaranta take sai Muneera ce zaka yi magana saboda ta kai dare a waje?" Dafe kai baba yayiYa shige part d'insa ba tareda ya sake tanka mata ba. Cije baki Mama tayi tana jin tamkar ta ran'kwashi kanta, tayi babban kuskure domin layar da malamin ya bata wadda zata sakawa Baba gaba d'aya ta manta da ita a jakarta, da ace ta saka layar da abin yazo da sau'ki da bai samu damar bud'e baki ba ma balle har yace 'yarta tana kaiwa dare a waje.

A yanzu mama ta zama 'yar gari cikin 'kan'kanin lokaci ta isa gidan malam ko batulu bata sanarwa ba, tana zuwa ta tarar da mutane biyu a gidan saida ta jira, ji take tamkar za'a d'aura auren Hidaya ba tareda ta aiwatar da abinda ke zuciyarta ba, a yanzu imaninta ya fara tafiya d'an tausayin da take dashi duk babu, ji take zata iya aikata komai domin ganin ta cimma burinta. Tana zaune aka gama da matan dake ciki da hanzarinta ta shiga d'akin, ko gaisawa bata jira sunyi ba tace "Malam aikinnan fa sam baiyi ba". Gyara zama malamin yayi yace "kamar yaya Hajiya? A gabanki dai nayi komai Hajiya". Girgiza kai Mama tayi tace "to gaskiya saidai ko an samu matsala ta wani 'bangaren, ita 'yar tawa da kace maza zasu dinga rububinta tsawon fa sati biyu kenan ko fi amma saurayi d'aya tayi, a haka zata haska malam? Gashi 'yar kishiyar tawa aikin ma kamar 'kara kusanto dasu yayi domin yanzu da nake maka maganarnan suna can suna tsaida lokacin aurenta da saurayin nata, aikin alhaji ne ma ban samu saka layar ba na sha'afa amma nasu kam gaskiya a duba min".

'Kasa Malamin ya d'auko yace "ya sunan saurayin da inda yake zaune?" Fad'a mishi mama tayi yayi zane-zanensa sannan ya girgiza kai yace "hajiya matsalar daga saurayin take domin yana da 'karfin tsari a jikinsa wanda shigarsa zaiyi wahala idan har ba kwantar dashi zamuyi gaba d'aya ba, kuma aikinmu yana nan bai 'baci ba domin na miki rantsuwa da wanda ya halicceni babu wanda zai ga yarinyarnan ya kalleta a matsayin mutum ma balle mace, abinda zamuyi yanzu shine mu nesanta shi da ita ko da lafiya ko babu, idan aikin bai shigeshi ba zamu turashi kan mahaifiyarsa ko wani sha'ki'ki wanda yake jin maganarsa mu cusa musu tsanar yarinyar yanda ba zasu ta'ba amincewa aurenta ba, sai maganar 'yarki...gaskiya Hajiya saidai idan matsalar daga ita ne amma kowa ya shaida aikina baya lalacewa ba'a samun akasi, idan har muka 'kara wani aikin akan wannan zai iya yin 'karfin da maza zasu dinga lalata da ita, saboda haka kije zanyi aiki a kan ita 'yar kishiyar taki ita kuma taki 'yar ki zuba idanu ki 'kara jira zaki sha mamaki".
__________________________

WITHOUT MY DREAMS (HAUSA NOVEL)✔️Onde histórias criam vida. Descubra agora