12

306 16 0
                                    

WITHOUT MY DREAMS
Kitty
12

Tunda 12 ta gota Muneera bata shigo ba Mama ke cikin tashin hankali, wayarta gaba d'aya an kira a kashe.

Zirga-zirga Mama keyi tsakamin gate zuwa part d'inta zuwa part d'in Aunty, har Aunty da Hidaya Suma sun shiga damuwa. Duk wanda Hidaya ta kira sai suce sun bar wurin Muneera na ciki, Sofie ce kawai tace sun fito tare amma tun 11 suka fito domin ita har ta jima ma a gida.

1am nayi hankalin mama ya sake tashi ta nufi part d'in Baba ta sanar mishi Muneera fa bata dawo ba, da farko ya nuna rashin damuwarsa amma ganin yanda hankalin iyalinsa ya tashi da ma mutanen da sukazo tayasu farin ciki yasa ya fito daga part d'insa shima. Har Yusuf Hidaya ta kirawo amma shima baiyi picking ba.

A lokacin da Muneera ta shigo ta hango Baba ya juya ya koma part d'insa, a hankali me gadi yace "tun d'azu mutanen gidan ke suke nema lafiya dai ko?"

"Lafiya" .ta furta tareda tsaki sannan ta shige da gudu, kai tsaye part d'in Aunty ta nufa inda sukayi karo da Mama ta fito zata sake duba gate.

Baya mine tayi tace "yi ha'kuri Mama ban ganki ba".

Wata ajiyar zuciya Mama ta sauke tace " Muneera? " Amsawa Muneera tayi saida Mama ta 'kare ma fuskarta kallo sannan ta wanketa da mari tace " daga gidan uban wa kike?"

Dafe kumatu Muneera tayi tace "mama daga wurin biki mana". Wani Marin Mama ta kai mata wanda ya saka ta saki rigar hannunta ta fad'i 'kasa, sai a yanzu Mama ta lura da rigar hannunta, cikin 'karaji tace "bazaki fad'a min inda kikaje ba dan ub**ki!!! Menene dalilin da yasa Kika cire rigarki? Muneera ke wacce irin mahaukaciya ce eh!! Sai 1:30 zaki shigowa mutane gida sannan kice daga wurin biki kike? Wato kin bi yaronnan kunce kunyi iskancinku sannan zaki dawowa mutane gida? Wallahi Kika sake aka fasa aurenki gobe saidai ki sauya wata uwar ba ni ba lalatacciya kawai".

" Mama wallahi ba abinda..... Um baimin komai ba rigata 'ballewa tayi mama.... " . Wani dukan Mama ta kai mata Baba ya janyeta yace "ya isa haka, tun daga waje nake jiyo muryarki kina zagin ubanta shi mene laifin uban nata? "

" Kayi ha'kuri Alhaji banji shigowarka ba, amma ka barni na karairaya yarinyarnan na huce takaicin da nake ji, na tara 'yan uwana a gidannan amma yarinyarnan batada buri da ya wuce ta bani kunya? Tun dawowar Hidaya dangina ke 'kananun maganganu akan halayyar yarinyarnan, Alhaji na gaji da halayen da takeyi a gidannan".

" Idan kinyi ha'kuri gobe war haka tana gidan mijinta, ko me ta aikata magana bazata sauya hakan ba kiyi mata addu'a kawai.... Ke Kuma Muneera Allah ya shiryeki, gobe dai za'a d'aura aurenki da yaronnan kije can kiyi rayuwar da kikaga dama".

Tafiya Baba yayi ya bar Muneera tana ta shesshe'kar kuka itama Mama wani kallo ta watsa mata tayi tafiyarta, jiki a sanyaye ta shiga d'akin Hidaya tareda aje rigarta.

Kallonta Hidaya tayi alamun gajiya da bacci sun bayyana a fuskarta, girgiza kai tayi ta d'auro alwala ta kwanta ta juyawa Muneera baya. Haka Muneera tayi kwanan ba'kin ciki tana jin tamkar ta janyo gobe a kaita gidan Yusuf ko ta huta da masifar gidansu.

Duka kayanta suna d'akin Hidaya kasancewar nasu part d'in akwai mutane, har suka gama shiryawa babu wanda yace da wani 'kala. Ko da taje gaida Mama sama sama ta amsa mata, Aunty ce kawai ta sakar mata fuska Hidaya kuwa tun safe idonta ya fara sauyawa tana jin kewar Muneera ta fara taso mata dukda basa good terms a kwanakinnan.

An d'aura Auren Muneera abdulmutallib da yusuf Bala Nayaya, 11:30 Muneera ta hau status d'inta ta d'aura _officiallymrsyusuf💕_ mutane da dama sun tsokane ta akan ta rage zumud'i saidai tayi murmushi ta musu reply.

Shima ango tunda aka d'aura ya fara mata messages tun tana amsawa dan kanta saida ta gaji ta aje wayar a gefe ta Shiga sabgoginta.

Azahar kafin Baba ya fita ya kirata ya mata nasiha mai ratsa zuciya, ta d'an matse hawaye kamar gaske amma kafin 1 hour ta koma sabgoginta.

5:00pm masu d'aukan amarya suka 'karaso, Muneera sai rawar kai take ita amarya tana shige da fice tareda warning kar a manta mata wani abun a gida. Bayan ta shirya aka turata wurin Mama da Aunty su mata fad'a, kusan fad'an aunty ce ta mata shi Mama tace batada sauran fad'an da zata mata, "duk fad'an da zanyi miki na riga da nayi Muneera amma ko d'aya a ciki baki d'auka ba, inada tabbacin idan nayi yanzu ma zai tashi a banza ne saboda haka kije saidai nace Allah ya bada sa'a".

" A'a Yaya karkice haka, kar a kaita gidan miji kina fushi da ita".

Rai a 'bace Mama tace " ita ta damu da 'bacin ran nawa? Kuma ina mata fatan alkhairi a duk inda ta tsinci kanta fad'a ne dai na gama mata shi, gata ne ma ka samu wanda zai maka fad'an, watarana ke da kanki zaki dinga neman mai fad'a miki gaskiya ki rasa".

Muneera na kuka ta d'aura kanta a cimyar Mama tace "Mama nasan na 'bata miki rai Amma dan Allah ki yafemin insha Allahu bazan sake ba".

Kuka take mai sauti wanda yasa Mama itama zuciyarta ta d'an karaya ta mata addu'a aka fita da ita. Hidaya na kuka sukayi sallama ta ri'ke muneera tamkar bazata rabu da ita ba, Har aka saka Muneera a mota tana kwarmata ihu wasu na mata dariya wasu tana basu tausayi.

Abin mamaki duk kukan da takeyi babu ko d'igon hawaye a idonta sai tsabar ihu da takeyi, bayan an kaita anyi mata addu'a duk manya sun watse ya rage daga ita sai 'kawayenta.

Akwatin nightwear d'inta ta d'auko ta bud'e domin su za'bar mata wanda zata ma mijinta kwalliya dashi, gwadawa ta fara yi duk wanda ta saka tayi juyi suce "wow". Sannan ta cire ta saka wani.

Hidaya sai binta da ido takeyi tana tunanin abinda take aikatawa, ganin babu wanda zai fad'a mata gaskiya yasa Hidaya tace "twinnie bai kamata ace Yusuf ya shigo ya sameki da nighties ba ko kuwa? Tunda naji ana cewa kunyar ranar farko ga amarya na d'aya daga cikin abunuwan dake d'aga darajarta a wurin miji. Ko zaki saka nighties sai ki bari sai daga baya".

Muneera na gyara mad'aurin rigarta tace " wannan zamanin jahiliyya kenan twinnie. Kayi auren soyayya da mutum kawai ku zauna kuna wani 'kunshe 'kunshe? To ki ma bud'e kunnenki kiji wallahi kikaje gidan miji kikayi wannan 'kauyancin kallon wawiya zai miki".

Girgiza kai Hidaya tayi tace " Muneera kunya fa adon 'ya mace ce kuma duk yanda mijinki zaiso ki sake dashi at this point sai kinfi birgeshi idan kinzo da kunya".

" Hidaya......dan Allah ki dena wannan shirmen, wad'anda suka waye suka san me sukeyi sun aje wannan kunyar ta rashin ilmi da rashin sani a gefe yanzu sakin jiki ake a mori juna". Sofie ta fad'a tana kallon Muneera tareda mata alamar kayan jikinta sunyi.

Dukkansu sun yarda da maganar Muneera da Sofie mutum d'aya ce ta yarda da Hidaya. Wadda take cousin ce ga Hidaya mai suna zainab. hakan ya kawo debate sosai domin zainab nada kafewa akan ra'ayinta, ita kuwa Hidaya ba ma'abociyar cacar baki bace wanda yasa taja baya tayi shiru. Zainab ta kawo musu point da dama amma duk suka take suka ce tana ganin haka ne kawai saboda tana bafillatana.

Ri'ko hannunta Hidaya tayi tace "zainab kiyi shiru dan Allah".

_"firtam!"_ zainab ta fad'i a fusace. _"wadu miyal"_ Hidaya ta furta tareda d'auke kanta daga wurin zainab. Itama zainab d'in shiru tayi saidai ranta a dagule domin ta'ki jinin ayi defeating d'inta kan abu. Itama ta gama secondary kamar su Hidaya wanda take Shirin dawowa Kano wurin Aunty domin ta cigaba da karatunta.

Bayan Muneera ta za'bi kayan da zata saka ta shiga toilet tayi wanka sannan ta d'auki kayan da kowa yace sunfi mata kyau ta aje a gefe ta fara turara jikinta da turarurrukan da dangin mamanta suka had'ota dasu.

Har 9pm angwaye suka shigo babu wani 'bata lokaci aka d'auki 'kawayen amarya aka kaisu gidajensu aka bar ango da amaryarsa. Cire babbar riga yayi yace "to Muneera yau dai Allah ya kawomu gani gaki rowa kuma ta 'kare".

Murmushi tayi tace " luvly ai ba rowa nake maka ba adani kawai nakeyi maka yanzu ma I have a surprise for you". Bata jira amsarshi ba taje ta sako night wear da ta ajiye, tana fitowa ya tashi tsaye yace "wow, wow, wow..... Muneera you look amazing".

Juyi tayi tace " really?" Tareda bud'e top d'in jikinta sannan ta maidata cikin sauri ta rufe tana dariya. Numfarta yayi suka fara tsere suna zagaye a parlour, cire top d'in tayi tareda wurgi da ita kan kujera ta tsaya wurin da take tareda ri'ke 'kugunta tana mishi wani irin kallo.

********
Nasani it's too short kuyi ha'kuri sai gobe insha Allah 🤭🤭

WITHOUT MY DREAMS (HAUSA NOVEL)✔️Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang