06

311 17 0
                                    

06

        Muneera saida taji wani daban a inda Yusuf ya daura hannunsa saida ta kawar a ranta tana fad'in 'soyayya ce idan baya sona inda Nike ma bazai kalla ba'.

Idanunsa na kan 'kirjinta ya zuba mishi ido yanda rigar ta kamata ta fito da curves d'inta sosai, wuyan rigar har sama yake wanda ya sake bayyanar da shape na boobs d'inta, mayafin da ke jikinta ta nad'eshi ta d'aura a kafad'a. Gyaran murya tayi tace "you know, my eyes are up here".

Dariya yayi yace "kinyimin kyau ne sosai and ai babu laifi domin da kai da kaya duk mallakar wuya ne, da fuskar da body da mai su duk mallakina ne Kinga kuwa inada ikon na kalla ko kuwa? "

Murmushi tayi tana waiwayawa ko zataga wani na kallonsu taga babu wanda hankalinsa ke kansu, cikin murmushi ta amsa tace "you're right duka mallakinka ne amma zuwa wani lokaci, banga shigowarka ba".

Kallon lips d'inta yayi da sukayi matu'kar kyau da nude lipstick, kwalliyar fuskarta light make-up ce tayi kyau sosai haskenta ya sake bayyana. Ganin zai sake shagaltuwa yasa ya maida idanunsa nata wanda suka sha fake eye lashes da sandy eyeshadow yace "ta ina zaki ganni kina can kinata rawa. Wannan kwalliyar i fell like tak..... ". Katse maganarsa yayi ganin zai saki layi sannan ya sauya yace "dole na biya kud'in kwalliyarnan, da inada iko zance babu mai ganinta sai ni".

Kashe mishi ido tayi tace " idan kaso zakayi claiming d'ina taka a duk lokacin da ka shirya, kaga yanzu anata kiran 'kawayen amarya ina nan akwai wata group dance da zamuyi ne muje ko? "

Sai a yanzu ya sauke hannunsa daga hips d'inta ya zaro wata wrapper d'in ta 500 ya mi'ka mata yace "wannan kud'in kwalliyarki ne". Sannan ya ciro wrapper na 200 ya sake bata yace tayi li'ki dasu.

Girgiza kanta tayi tace "wanda kayimin li'ki dasu sun isa ni 'kawar amarya ce fa kuma cousin d'inta ni babu wani li'ki da zanyi, and kwalliya na biya kud'inta kyauta nayi maka ka gani ka yaba kuma ka yaba that's all I want".

Kamo hannunta yayi ya saka kud'in sannan yace " wannan ya rage gareki nidai na baki, ko kiyi kyautarsu ko ki zubar duk ra'ayinki ne, banga Hidaya ba".

Kar'bar kud'in tayi tace " since you insist nagode, Hidaya na can maybe idan mukaje zaka ganta".

Wata wrapper ta 200 ya sake cirowa yace " to wannan nata ne itama tayi li'ki dasu".

Bata mishi musu ba ta kar'ba tareda godiya tana mamakin irin wannan kyautar tashi, daga had'uwa da ita ya kashe mata more that 2million daga motar da ya saya musu zuwa laces da atamfa, gashi yanzu ya fitar da 140,000 ya bata, shi baya jin kud'i ne?

Suna komawa ta had'u da Hidaya zata fita, kamo hannunta tayi cikin sauri Hidaya ta juyo, numfashi ta sauke tace "yauwa ke nake nema".

"Hidaya ga Yusuf ku gaisa".

Kallon Hidaya yayi sannan yace " kinyi kyau sosai ai ban ganeki ba ma".

Murmushi tayi ta sauke kanta cikin kunya tace " nagode, ina wuni".

" Lafiya lau, ya taro?"

"Alhamdulillah".

Kallon Muneera yayi yaga ta turo baki, dariya yayi yace "au kishi zakiyi da twinnie d'in taki saboda nace tayi kyau? Ai duk kyan da zatayi bata kaiki ba my baby". Ya 'kare maganar yana kissing goshinta. Hidaya d'auke kanta tayi tana jin wani iri a ranta, shi ko kunyar yin haka cikin mutane bayayi? Kallon Muneera tayi taga ko a jikinta sai ma neman nane mishi da takeyi.

"Yauwa Muneera hotuna zamuyi Mama tace na nemoki, muje ko?"

Jan hannun Yusuf tayi suka tafi tare, kafin ayi hotunan saida ta fara gabatar da Yusuf a wurin Mama da 'kannenta dake wurin sannan akayi hotuna. A 'kan'kanin lokaci kowa yasan Yusuf domin yawo ta dinga yi dashi tana nunawa cousins d'inta da aunties da friends shi. Tun kafin ta gabatar dashi zancensa akeyi domin duk sunga lokacin da yayi Mata ruwan 500.

WITHOUT MY DREAMS (HAUSA NOVEL)✔️Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang