48

57 9 0
                                    

WITHOUT MY DREAMS

*AYYIRIRIRI AHAYYE CHAS 💃🏼💃🏼💃🏼 sunan wata waƙa wai ita LUWAI*
_Ana tayi muna tayi manyan mata dai da gaske sun dage sai sun zama kalar gaban mota kalar camera tare da gudummawar Mg's skin care Hajia ta kina ina ake ta wannan harkar arziƙin mata nata glowing suna faranta zuciyar mazajensu da laushi da santsin fatar su ke kina nan kina fama jiki duk kirci😱😱?_
   Ah haba madam yunƙuro ayi tafiyar nan dake ki shiga ki wataya acikin shahararrun matan nan da ko'ina ake fatan gani  dan an daɗe ana jin su watau *team glow by Mg's*
   Macen da ta isa itace mace karki bari ki zama cikin irin muna matan nan da suka rako mata duniya kuna tafe da mijinki yana kallon wata har miyau na zuba tsabar haɗuwarta da kyan fatarta
Mg's skin care sune sirrin duk wata macen da ta isa a ɗaga kai a kira da suna mace wacce ba'a jin kunyar shiga taro da ita daga nan har villah kizo/kuzo mu haɗe a wannan ƙasaitacciyar tafiyar ta Mg's skin care domin sune na gaban gaba sune suka ciri tuta indai a harkar gyaran skin ce hajiata kiyi wani fresh  kiyi smooth wow🥰🥰🥰kina tafe kina walwali idan fa kina amfani da *Mg's skin care* ba kya buƙatar ko wanne irin mai product ɗinmu katt ne duk matsalar fatarki muna da maganinta uhmm inata miki labari  nace  ba sister shin  meye matsalarki ta gaban goshin ƴallaɓai?
Acne?, pimples? spot?, strech marks?, sunburn?.
to hutas bi'izinilLah muna da maganin matsalarki kina ganin mata a tiktok fuska luwai lumus kice dama ni ko? to in dai kina tare da *Mg's* matsalarki tazo ƙarshe  bama cika baki gaskiya itace takenmu haka nan kuma siyen nagari mai da kuɗi gida *MG's skin care gagarabadau*
Price ɗinmu daidaitacce ne  sannan kuma dai dai da aljihunku

*Soap price:4k*
maiso yy mgn
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391
Instagram:glow_with_mgs
Facebook: mg's skincare
 
Masu bukatar cream Shima munadashi harda ma complete set nagyaranjiki
Small 12k
Medium 14k
Babba 20k

*BE PART OF THE GLOW TEAM KARKU BARI A BAKU LABARI*

48

Zuba idanu Muneera keyi cike da fargaba ganin Baba da Halim a tsaye a parking lot d'insu suna magana kuma ga dukkan alamu doguwar magana sukeyi ga Kamal ya sanar mata yana gab da 'karasowa. Gabanta ne yayi mummun fad'uwa jin an doka horn a 'kofar gida bayan d'an lokaci mai gadi ya kira wayarta ya sanar mata da zuwan kamal, saida ta had'iyi wani mugun yawu sannan tace "eh ka barshi ya shigo". Komawa cikin part d'insu tayi tana duba kanta a console d'in dake 'kofar palonsu, cikin sauri Mama ta fito tace "au inata dubawa na d'auka kin tafi ne ai, maza shafa wannan turaren". Tsiyaya mata mama tayi a hannu Muneera ta kai hannun hancinta ta shinshina, shafeshi tayi a jikinta tace "mama ki sayo humrarnan da yawa tana da dad'i". Murmushi mama tayi tace "to shikenan zan saka a had'a miki babbar roba, maza jeki kar ki barshi yana jira". Kallon Mama Muneera tayi tace "Mama baba yana tsaye ba zai ce komai ba ko?" Tsaki mana tayi tace "me zaice? Jeki kawai".

Fitowa Muneera tayi tana taku d'ai-d'ai taga Halim ya zubawa motar kamal idanu, sport car ce 'kirar ferrari red mai azabar kyau irin mai doguwar 'kofarnan, tana fitowa murfin motar ya d'aga da kansa yayi sama tamkar fukafikin tsuntsu, tunda kamal ya shigo ya sami su baba a tsaye baiyi yun'kurin fitowa ya gaidasu ba saida Muneera ta fito, fitowa yayi daga motar cikin 'kasaita ya danna wani 'karamin remote murfin ya sauka motar ta rufe kanta, da sauri Muneera ta 'karasa inda yake tace "Ga babanmu can fa ku gaisa". Kallon baba yayi da Halim yace "I thought...never mind muje". Ya 'kare maganar yana murmushi, suna 'karasawa wurin ya kame ya tsaya ko jira yake su fara gaidashi oho, mi'ka mishi hannu halim yayi ya amsa cike da 'kasaita sannan ya d'an sunkuyar da kansa yace da baba "barka da yanma". Cikin mamaki baba ya amsa da "barka dai". Yana kallonsa domin ba'a ta'ba kawo wani saurayi da ya gaidashi a tsaye ba sai wannan, baba yana amsawa kamal yace "ma sha Allah". Ya juya Muneera ta bishi a baya, duk yanga ta mace saida Muneera ta wuce Kamal dukda a bayansa take, ko a wurin zama saida ta kusa sakin baki ganin yanda ya d'auki lokaci tamkar wanda aka dannawa slow motion sannan ya zauna. Zama tayi tace "sannu ko?" Kallonta yayi sai a lokacin ya koma mutum ya fad'ad'a murmushinsa yace "sannu Muneera ya gajiyar kwana biyu". Kallonsa tayi tace "ashe kana iya bud'e bakinka sosai na d'auka baya bud'uwa". Dariya yayi sosai sannan yace "a yimin afuwa wasu...lokutan ne....na kan...manta da normal civilian nake magana saboda...kinsan a...fada komai sai ka yishi da 'kasaita, kuma...emm...hakanan nake". Ran Muneera ya fara 'baci domin ta'ki jinin namiji mai ji da kansa wanda hakan ya bayyana 'karara a tattare da kamal, sarauta ba 'karya bace amma ko sarki yana sakewa matu'kar ba a fada yake ba balle shi yarima.

WITHOUT MY DREAMS (HAUSA NOVEL)✔️Donde viven las historias. Descúbrelo ahora