41

58 8 0
                                    

WITHOUT MY DREAMS

41

Duk yanda Muneera taso ta tsaida zuciyarta ta kasa, comparing kanta take da Muneera musamman a yanzu da aka kawo mata wannan matsiyaciyar kyautar, tana budurwarsa ya rasa me zai kawo mata sai kifi da Apple? Wacce irin kyauta ce haka? Gashi a kunnenta taji yana fad'a ma mamanshi ta ari 2k idan yaje zai biya, sa'banin mahaifiyar jawad wadda da kanta ta yiwa Hidayatu kyauta ta sama da 200k, ta ina zata samu irin wannan kyautar daga mahaifiyar Aaseem wadda dubu biyu ma sai ta tambayi d'anta, sam ba irin wannan mijin take mafarkin aure ba, ba wannan rayuwar take so ta koma ba bayan wahalar da ta sha a baya, tana burin ta auri wanda ya ninka yusuf kud'i yanda yusuf zaiyi nadamar wula'kantata da yayi, tana burin ta auri mijin da zai wanke mata damuwar da ta shiga a baya, tana burin ta auri mijin da Mahaifiyarta zata yi farin ciki tayi alfahari dashi, tana burin tayi auren da zai wanke zuciyar mama saidai bata tunanin akwai wannan qualities d'in tattare da Aaseem, ta ina zai share mata hawaye yana fama da iyayensa da lecturing? Me ya samu me zata samu har ta sanya mahaifiyarta farin ciki? Dole tabi umarnin mama ta yanke Aaseem daga rayuwarta tun kafin ya fara sanyawa ransa false hope dama can tana kulashi ne sanadiyyar nacin Hidaya.

Tashi tayi daga kwancen da take a daidai lokacin da Hidaya ta shigo sa'kale da jakarta ta makaranta a kafad'a, maroon hijab ne a jikinta da facemask da glasses ba zaka ta'ba gane fuskarta ba idan ba cire mask d'in hancinta tayi ba. Cire hijabin tayi da mask d'in da glasses d'in tana maida numfashin gajiya tace "twinnie ya result d'in naku yau ma saida baba ya tambaya result d'inku ya fito nace ban saniba". Turo baki Muneera tayi tace "ai tunda kikaji nayi shiru na samu matsala ne twinnie, inada matsala course d'aya naje kuma na sami malamin bai shigar min da C.A bane amma kinsan dole saidai na ha'kura nayi carrying d'insa, but still inada 3.0CGPA". Murmushi Hidaya tayi tace "zaki gyara shi cikin sau'ki in sha Allah, ki fad'awa baba ko hankalinsa ya kwanta". Kallon hidaya Muneera tayi tace "banaso na fad'a mishi 3.0 gareni kina da 4.8". Dafa ta Hidaya tayi tace "Muneera what matters shine kinyi passing and with more effort zaki iya samun duk point d'in da kikeso, ki fad'awa baba zai baki words of encouragement da zasu 'karfafa miki gwiwa". Tashi Muneera tayi tace "to zan fad'a mishi, yauwa Aaseem...Hidaya I can't be with him...ki fad'a mishi kar ya sake zuwa". Bata jira maganar da zata fito daga bakin Hidaya ba ta fice daga d'akin, binta Hidaya tayi da kallo tana jin zuciyarta tayi mata nauyi, tunda Muneera ta fara comparing kanta da Hidaya Hidaya ta fara lura da sauyi daga gareta, addu'a take da fatan Allah yasa kar abinda ya faru a baya tsakaninsu ya sake faruwa, duk abinda zai shiga tsakaninta da twinnie d'inta tana 'ko'karin kawar dashi gefe fatanta itama Muneera ta aikata hakan ko da abin a cikin zuciyarta yake.

Muneera na shiga part d'insu Mama ta lura da fuskarta babu dad'i, kiranta tayi ta zaunar da ita tace "Muneera menene ke damunki naga fuskarki duk babu dad'i haka?" Sunkuyar da kai Muneera tayi tace "Mama babu komai". Dafa hannunta mama tayi tace "Muneera kinada wanda zaki fad'awa damuwarki ne bayan ni? Ki tuna Muneera duk wanda zai soki ya kuma wanke miki zuciyarki da damuwarki a bayana yake, ki fad'a min abinda yake damunki ni kuma da yardar Allah zan miki maganinsa tun kina ciki nake maganin matsalarki Muneera". Dogon numfashi Muneera ta ja sannan tace "mama nayi abinda kikace, na fad'awa Hidaya ta sanar da Aaseem kar ya sake zuwa tunda ita ta had'amu dashi tun farko". Murmushi ne ya bayyana a fuskarta mama tace "yauwa Allah yayi miki albarka, Muneera banida burin da ya wuce farin cikinki, kina gani dai mahaifinku tsufa yake kuma samunsa na yanzu ba kamar na da ba, gaba d'aya 'ya'yana maza an lalata musu rayuwa, khalid da mus'ab babu ta inda zan moresu, halim kuwa mahaifinku shi ke juyashi yanda yakeso, a yau idan mahaifinku ya dena kasuwanci halim bashida wani sauran mamora, abdurra'uf kina gani da 'kyar ya fara kasuwanci kuma har yanzu babu wani abin arzi'ki da ya samu banda kud'in kashewa da yake samu, a sakar mishi ya wataya ma an'ki, ke kad'ai ce sauran hope d'ina Muneera, a yanzu surukin kirki kad'ai ne zai iya wankemin damuwata shiyasa nake miki burin auren mai arzi'ki, kiyi auren da zaki huta nima na huta Muneera , bana son auren 'karma-'karma domin ke ba matar matsiyata bace, ki dubi kyawun da Allah yayi miki kuma kin fito daga babban gida, sunan mahaifinku babu inda zaki d'aga shi ba tareda an san waye shi ba a garinnan, kar ki wula'kanta alfarmar da Allah yayi miki ta hanyar auren kasasshen namiji, ni zan taimaka miki naga kin samu hamsha'kin mai kud'in da zaki aura ki samu kwanciyar hankali da wadata da nutsuwa, kawai abinda nakeso daga gareki shine had'in kai, duk abinda na sakaki Muneera kar ki kin musu ki sani ba zan ta'ba yin wani abu domin na cutar dake ba". Jikin Muneera yayi sanyi da jin kalaman mama domin tun tana 'karama wad'annan maganganun ke fita daga bakin mama, tana jin zafin ganin mama cikin damuwa saboda haka tayi alwashin bin umarnin duk abinda mama zata fad'a mata ko menene shi, domin babu wanda zai soka ya kula da kai sama da uwa mahaifiya, babu mai burin farin cikinka fiye da kai kanka sama da mahaifiya, wannan dalilin ya sanya Muneera ta amince da umarnin Mama tace "in sha Allah mama bazan miki musu ba akan duk abinda zakiyi na san farin cikina kike buri".

WITHOUT MY DREAMS (HAUSA NOVEL)✔️Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang