09

277 15 6
                                    

09

        Daga yanda yanayin Baba ya sauya lokacin da ya bud'e wayar Muneera ya tabbatar ma Hidaya akwai matsala babba.

Bud'e wayar Hidaya yayi itama sannan yaci gaba da caje wayoyin biyu yace da Hidaya ta kirawo su Mama.

Bayan shigowarsu ya mi'kawa Mama waya yace "da saninki 'yarki take aikata wad'annan abubuwan?"

Kar'bar wayar tayi ta duba taga irin hirar da Muneera keyi da Yusuf, kallon Muneera tayi tace "wallahi Alhaji bansan tana aikata haka ba, ta yaya zan sani kuma na barta? "

" Ke ba mahaifiyarta bace? Ya kamata ace duk motsinta kina sane dashi, sannan waye ya bashi damar zuwa wurinta? Meyasa har ya kawo mata waya kika bari ta amsa ba tareda an sanar dani ba? "

" Alhaji lokacin da sukayi hatsari ne ya kawo mata wayar a cikin kayan dubiya nikuma banyi tunanin wani abu ba na barta tayi amfani da ita. Nasan nayi kuskure da na barta tana sauraronsa ba tareda izninka ba amma Alhaji kayi ha'kuri".

" Wani irin ha'kuri zaki bani bayan yarinya ta gama lalacewa kuma kece sila, a matsayinki na uwa da take tare dake a kowane lokaci ya kamata ace idanunki na kanta, ita kad'ai ce 'yarki mace ace tarbiyyarta ya gagareki? Kaltume tun tasowar yarinyarnan bakya bada muhimmanci akan tarbiyyarta, gashi yanzu ta janyo mana abin kunya me kuma zaki cemin? "

Mama shiru tayi yayin da Muneera jikinta ke ta rawa ga wani gumi dake zuba. Kallonta Baba yayi yace "tunda abinda kika za'ba kenan aurar dake zanyi, ki fad'awa shi wannan yaron yazo ya sameni gobe a tsaida maganar aurenku, a cikin wata biyu nakeso na cireki daga idanuna, kema Hidaya idan har akwai wani ki gaggauta sanar dani domin idan na gano kina kula wani sai na hukuntaki".

Fashewa Muneera tayi da kuka tana bawa Baba ha'kuri amma bai saurareta ba ya sallamesu. Su Mama su suka fara tashi suka fita bayan fitarsu Muneera tace da Hidaya "burinki ya cika kin had'ani da Baba kin had'ani da Mama sannan kin had'ani da Yusuf, Hidaya me na tare miki a rayuwa? Meyasa sai a yanzu kike nunamin ba'kin ciki da rayuwata?"

" Muneera kinji na bud'e baki na fad'awa Baba abinda ke faruwa? Muneera bana ba'kin ciki da rayuwarki inaso na kareki ne daga sharrin zamaninnan".

" Babu wani sharrin zamaninnan saidai nace Allah ya kareni daga sharri irin naki magulmaciya kawai, sai ki zuba ruwa a 'kasa kisha burinki ya biya".

Baba ya kar'be wayar Hidaya da Muneera sai a wayar Mama Muneera ta kirawo Yusuf ta sanar masa Baba yanason ganinsa, a tsorace yace "lafiya dai ko?"

"Lafiya kalau dama nace maka idan muka gama exams zan yiwa Baba maganar da kayi ta zaka zo gaidashi? To shine na mishi yace kazo gobe".

" Gobe kuma? Gobe inada aiki sosai".

" Luvly sau nawa kana kashe aikinka saboda kazo ka ganni? Goben ma will be the same shi baba bayason 'bata lokaci ne amma kawai gaisawa zakayi ku tafi".

" To shikenan zanyi squeezing nazo insha Allah, ba dai wasu tambayoyi zaiyimin masu tsauri ba ko?"

" I don't know luvly amma zasu iya yin tsauri so kazo da shirinka, nidai inaso ka min al'kawari no matter what bazaka kujeni ba".

" I promise you babyna, na tura miki sa'ko ta whatsapp kin duba kuwa?".

" Ai luvly waya bata hannuna Baba ya 'kwaceta, so Kar ma ka turo kowane sa'ko ko kuma ka goge shi ma idan ka turo, sai goben". Ta katse kiran.

Washegari tana ta zuba ido sai 5:40 Yusuf yazo Baba ya saka aka rakashi wurinsa, tamkar mutumin arzi'ki ya sunkuyar da kai ya gaida Baba.

Amsawa Baba yayi sannan yace mishi "Yusuf kake ko? Inaso na maka tambaya d'aya tsakaninka da Allah auren 'yata kakeso kayi ko kuwa kazo ne ka lalata tarbiyyarta?"

WITHOUT MY DREAMS (HAUSA NOVEL)✔️Onde histórias criam vida. Descubra agora