14

291 25 0
                                    

Sooo you guys are reading without voting 🙄 babu update again har sai votes ya kai rabin ya kai rabin reads.

14

        Dariya Muneera tayi harda ri'ke ciki sannan tace "wallahi luvly kanada abin dariya, to mene dan kawai nace inada ciki as if nace maka mutuwa zanyi? "

'Dago kanta yayi daga cinyarsa yace " my Queen lokacin wasa ayi wasa are you serious? Da gaske kike you're pregnant? "

Turo baki tayi tace " to nima dai ban saniba kaga cikina har yanzu flat ko?" Ta d'aga rigarta tana shafa cikinta sannan tace " amma  kuma tunda akayi bikinmu fa banyi period ba kaga second month kenan ko?"

Tashi yayi cikin sauri yace " bari na amso miko PT strip ki duba kigani".

" A'a ba yanzu ba luvly mu d'an 'kara jira ko? Kaga fa babu abinda nakeji babu laulayi maybe ma ba cikin bane lateness ne kawai but thinking about being pregnant makes me happy, luvly I can't wait to have a little you growing inside me".

" Ni duk ba wannan ba bari naje na kar'bo miki nan shagon adekunle the sooner we knew the better".  Fita yayi tabi 'kofar da kallo tana murmushi tareda fad'in "luvly kenan daga zancen babies duk hankalinsa ya tashi, Allah dai ya tabbatar mana".

Bai jima ba ya dawo da PT strip guda 6, kallonsu tayi tace " luvly wannan fa?"

"Fitsari zakiyi a kansu dukka saboda a tabbatar, idan ma wani zaiyi 'karya sai a gani a wani".

" To banda abinka luvly nifa naji ance fitsarin safe ne ake ganin ciki ka bari gobe first thing in the morning nayi nagani, dukda I'm 60% sure I'm pregnant".

" Da fitsarin safe da na yamma da na dare duk sunanshi fitsari kuma yanzu fa 12 tayi dan Allah tashi ki gwada". Tana dariya ta tashi tace " kaidai luvly da zumud'in ganin babynka, Allah yasa idan na haihu kar ka zama mai rowar babies ka hana kowa d'auka".

Bai tanka mata ba ta shiga toilet tayi fitsarinta ta dawo, a ciki guda biyu basu nuna koma ba amma hud'un duka sun nuna.

Positive
Positive
Yes
Positive

"Nifa luvly ban gane kan abinnan ba ta Yaya ake gane akwai ko babu? "

" Gashinan my Queen alamun akwai kenan fa, gashinan positive ya nuna? Nan bakiga yes ne yayi alama ba? Gaskiyar magana you're aborting this pregnancy".

" Ban gane abortion ba luvly". Ta furta tana cike da mamaki, zama yayi a 'kasa tana kan kujera yace "Ina nufin zubar da cikin za'a yi tun kafin ya girma".

Girgiza kanta tayi tareda dafe cikin tace " haba luvly Allah yayi mana kyauta sai mu zubar? Mutum ne fa a cikina ba dabba ba ba kuma kaya ba. Allah ya azurtani da lafiya kaima kana da yanda zaka kula da 'ya'yanka kawai sai mu zubar da ciki? "

Cikin lallashi yace " my Queen abinda yasa nace haka kin kusa fara zuwa school fa, to karatu da aure ma ya aka 'kare balle da ciki? Sannan ina tausayinki you're too young to experience this hardship,. Kinsan kuwa yanda mata ke shan wahala wurin laulayi? Sannan azo ciki yayita girma wanda ke 'kugunki ma bai isa d'aukan baby ba, kayi ta fama da nauyin yaro a cikinka sannan azo haihuwa mata da yawa mutuwa ma suke saboda azaba balle ke 'karamar yarinya, sannan azo taking care of the baby, ke kanki har yanzu 'kar'kashin kulawa kike balle abinda zaki Haifa, banason kisha wahala shiyasa ma kikaga bana barinki yin ko da girki a gidannan".

Shiru tayi sannan tace " luvly ni gani nake zan iya fa ko? Ko na guji wahalar a yanzu dole gaba zan yita kuma I'm already 18, yara 15 years ma har 'kasa da haka ke d'aukan ciki su haihu?"

D'aukanta yayi ya d'aura a cinyarsa sannan yace "my Queen bazaki gane ba, amma tunda na fad'a miki bazaki iya goyon ciki ba ki yarda dani shekarunki sunyi kad'an ki d'auki ciki ga karatu, kuma ni banason kisha wahala I love you so much to see you suffer, Kinga yanzu babyn baiyi girma ba bai ma zama mutum ba jini ne kawai, so aborting d'insa babu laifi kawai a zubar dashi idan kika 'kara girma sai ki samu wani muyi rainonsa tare kinji? "

WITHOUT MY DREAMS (HAUSA NOVEL)✔️Onde histórias criam vida. Descubra agora