KAZAMAR AMARYA Completed
Sanin labari sai an shigo daga ciki
Rayuwar auren masoya biyun na tafiya daidai yanda suka tsara tun farkon fari, kwanciyar hankali da son juna ya kafu a cikin gidansu wanda hakan yasa suka zama abun burgewa ga jama'a da dama har wasu suna fatan ina ma su ne! Suna tsaka da wannan jindaɗin ne rayuwarsu ta canja salo wanda hakan yayi sanadiyyar bankaɗuwa...
Murya Babu amo ta ce "Ai kuwa zan yi dukkan iyawata na kubutar da ke, ba zai yiwu ki zabe ni, ki mutunta ni, ki taho wajena sannan na kasa yi miki adalci ba, sai idan abin ne yafi k'arfin azancina". Tana rufe baki sai ganin Bulkachuwa na yi, ya fito daga cikin kicin dinta da yake falon. Take na tuna dangantakarsa da B...
Rashi ba shi kaɗai yake samar da giɓi a rayuwa ba. Wani yana doron ƙasa amma dalilai kan sa wanzuwarsa ta kasa amfanar da makusantansa. Me zai faru da rayuwar ƴaƴan da su ka zaɓi zama da giɓi a gurbin da mai cike shi yake da rai da lafiya? RAYUWA DA GIƁI...
Labarin Yarinyar da ta tashi a tsakanin yayyenta maza, da suke shirye da aikata ko menene saboda ita, ba ta san tsoro ba, rashin ji ya kaita ga haɗuwa da ƙaddararta, ko wace iri ce ƙaddarar ta ta?
In ya kalli FA"IZA sai yaji Fiye da madaukacin Takaicin daya ke ji in ya tuna itace yau MATAR SA..Fa"iza ba mafarkin sa bace a irin Rayuwar ISHAQ KABIR KAROFI..Sam Fa"iza bata dace ko kada'n da Tsarin Rayuwarsa ba, kowa yasan Ishaq dan gayu ne mai ilimi ne,kyakyawa ne dan Fafane dan Alfahari ne Duniya tasan da zamansa...
_*" YA SAKE NI..YA SAKE NI..Yaya Saifuddeen ya sakeni na shiga uku na..!*_ _*Take fada kafin tayi zaman yan bori saman cafet din daya malale Dakin Mami dake saman Darduma tana lazimi ta mike a Firgice gabanta na fadi Hajiya zuwaira data fara barci sama sama sai da ta tashi a Firgice gabadayansu suka yi kan Majeeda sun...
labarin Sajeeda da ta ga jarrabawar rayuwa,ta wayi gari cikin tsananin ciwon da bata san ya akayi ta same shi ba,duk halin da take ciki makusancinta ya jefata a ciki
Akwai son zuciya me sanya mutum a tarkon nadama, zalunci mai kunshe da keta, zawarci mai sanya kunci, mutuwa mai dauke da yankan kauna. Nadama mai sanya kukan zuci gaba daya duk a cikin labarin DA WATA A ƘASA.
Labarin Soyayya, Sadaukarwa, Yaudara, Tuggu da Makirci.
Rayuwa gaba daya ta canzawa Rabi a dalilin kishiya, duk wata dama da ta zata kauna ce ta sa ya hanata yanzu ya bawa amaryarsa wannan damar; harma ya na kafa mata hujja. Bata taba zaton zai yi mata haka ba ko mata nawa zai aura.
_*AMINA Yanzu abunda kika Zabama rayuwarki kenan..?So kike kamar yadda kika saka ma ABA dinku Hawan jini nima ki sakamin ko..?Gidan Uban wa kika je bayan an tashi makaranta..?Duka Sauran yan"uwanki sun gaji da nemanki sun dawo..Saboda ke kin FITA ZAKKA agidan nan sai abunda kika dama kike yi ko Amina..?Bin Maza kika f...
Akwai ƙalubale me tarin yawa a cikin wannan Hikayar, bance babu soyayya ba sai dai akwai ababen ban mamaki da zasu faru, domin ya tattaru da manyan damuwa, kunci, rikici, abin tausayi, sai soyayya da yake a matsayin madubin labarin.
Yadda ya daga kai yana kallonta ne yasa ta shiga taitayinta babu shiri. Ya fara dumfararta gadan-gadan, kamar wanda yake shirin cinyeta danyarta. Duk dauriyarta kasawa tayi, ta fara ja da baya a rikice, idanunta sun fito waje kuru-kuru, dankwalin dake hannunta ta sanya tana kare fuskarta kamar shi zai kwaceta daga han...
Tabbas akwai ciwo a rayuwar da baka san karshenta ba, akwai tsoro a mafarkin da ka gagara farkawa! Ta ina lamarin ya fara? Ina tsakiyarsa da karshe? Yaushe damuwar zata wuce? Yaushe bakincikin zai gushe? Sai yaushe hawayen zasu tsaya? Zuwa yaushe ne kuncin zai yanke? Ashe a cikin rayuwa akwai wata rayuwa? A cikin ray...
Allah ya halatta aure ga kowanne dan adam mai lafiya, suma ZABIYU (ALBINOS) 'yan adam ne kamar kowa amma meyasa ake kyamatar su musamman ta fuskar auratayya? Da gaske ana gadon ALBINISM a cikin jini amma akwai wadanda halittar Allah ce ta samar da su a haka kamar HANSNA'U. Hasna'u kykkyawa ce amma ZABIYA ce....shin...
Ka da sunan ya sa ku yi tsammanin zallar soyayya za ku samu a ciki. Ka da sunan ya ba ku wani tabbaci na ba zai taba zuciyoyinmu ni da ku ba. Sunan wani jigo ne, na yadda kaddara ta hau kan rayuwar malabartan, ta yi shimfidarta ta kwanta ba tare da sanin ranar da za ta kama gabanta ba. Labarin zai dora zuciyoyinmu a w...
A lokacin da abinda kake tsoro yake tare da kai...! #AyshaShafi'ee #FikraWriters #FararWuta
Daada, Ku saka mata Munawwara, ku kira ta da Madina. Watakila albarkacin sunayen biyu rayuwar da bata da zabi a kanta ta zo mata da sauki ko yaya ne. Zan so kaina a karo na biyu, ku fada mata mahaifiyarta ta sota a watanni taran zamanta a cikinta, ko ba zata yarda ba Daada ki fada mata ta yafe mun, ki bata hakuri na y...
Labarin TSINTAR AYA, labarine daya shafi b'angarori da dama na rayuwar damuke ciki a yanxu, musamman b'angaren sayafi kowanne wato b'angaren auratayya. Abubuwa sosai masu zafi da ilmantarwa, fad'akarwa tare da nishad'antarwa suna cikin wannan faifan. Daure ka bibiyi wannan littafin domin samun abinda ya dace kada ku...
***Labarin WAIWAYE... #Dandano *** Na baku labarai kala-kala, a cikin su na baku labarin soyayyar data qullu a WATA BAKWAI, na zo muku da labarin tashin hankalin daya faru AKAN SO, kafin muyi tafiya a cikin RAYUWAR MU in da mukaga labarin Labeeb, ban gajiya ba wajen warware muku ababen da ALKALAMIN KADDARA ya kunsa...
Taya zai kalli idanuwan Abbu bakin shi yayi shiru? Ta ina zai hada idanuwa da Abbu kamar bai ci amanar daya bashi ba? Ana mutuwa sau daya, shine yardar kowa, amman a tsayin satikan nan, ya mutu a duk ranar da zai tashi daki daya da Rayyan, ya ga Rayyan yayi mishi murmushi, numfashin shi daukewa yake yi Ba zai iya ka...
Aƙida kan iya zama linzami akan tafarki na Rayuwar Ɗan Adam Aƙida kan iya zama linzami da zai ja kansa da kansa ?? ( yayi jagora a fagen tafiyar rayuwar Ɗan Adam ) . Ba koyaushe Ɗan Adam yake da zaɓi ba akan aƙidar sa . A hankali aƙida take sanɗar Ɗan Adam har ta shiga ta saje da halayyarsa da kafin ya farga tayi masa...