FADILAH KO SAMHA
writing by
Oum.... now and oldDedicated to ummu hairan
p 1
ASLM ALKM BRK DA WANNAN LOKACI KUMA INA MAI YI YAWA KOWA MURNAN SABUWAR SHEKARAR 2021 INA FATAN YARDA MUKA GA FARKON TA ALLAH YASA MUGA KARSHEN TA LPY
DA WANNAN ZANYI AMFANI GURIN MIKA GDY TA GA DUMBIM MASOYA LITTAFINA NA SANADIN MATAR UBA GSKY NAJI DADIN SAN DA KUKA NUNAWA LITTAFIN KUMA INA GDY
Kyakyawan saurayi nehh wanda bazai wuce 25years ba acikin wata mota kirar Prado yana tafe yana sauraren music din DJ Ab a cikin wakarsu ta DA SO SAMU NE a nutse yakebin wakar ko kalma DAYA bata wuce shi kai kace dama chan shi ya buga wakan
Salim ahmad turaki kenan abban sa alhaji ahmad turaki asalin sa dan gidan sarauta nehh achan kasar agadas kasuwanci nehh ya kawo shi nigeria ya hadu da hajiya harira wadda suke kira da mom aiko allah ya hada jinin su ba yarda iyayen alhaji ahmad turaki basuyi dashi ba akab ya rabu da harira ya taho gida ya auri yar uwarsa amma yaki yarda daga karshe suka zuba masa ido suka aura masa ita allah yayi da rabo inda Allah ya azurtasu da Ahmad suke kiransa da Salim sabida kara tun daga nan alhaji Ahmad bai kuma samun haihuwa ba saida Salim ya kai shekara Tara sannan Allah ya azurtasu da hanan daga wadda har yanzu itace auta
Allah ya sawa Salim San hanan dan idan yana tare da ita ko abinchi bata iya ci idan kuwa tana KUKA to fahh shima ya kamayi kenan saidai a hada su baki daya a hau aikin lallashi idan ko dare yayi hanan na gefen sa a dakin sa saidai idan yayi bacci Hajiya harira da suke kira da ammi taxo ta dauke ta
Salim ya kasance mutum mai kokari da sanin ya kamata Dan tunda aka sashi a makaranta tun daga aji DAYA yake daukan na 1 har kawo lokacin da akayi masa kanwa a lokacin yana primary 4 hakan ba karamin dadi yake wa alhaji Ahmad ba dan yana San yaga dan NASA yayi karatu dan haka nehh ya dage a kansa
Shekarar hanan 5 aka sata a makaranta a lokacin kuma Salim s s 1 lokacin da aka sa hanan a makaranta sai ya zama cewa Salim ya zama malamin ta a gida bata da wani sukuni sai na karatu ko yaushe karatu wani lokacin har gajiya takeyi tayi ta masa kuka shikuma ya sata a gaba yayi ta kallo yana mata dariya daga nan karatun ranan ya lalace dan hanan akwai zuciya tafiso idan tana kuka a lalashe ta idan ko aka ci to fushi kam za'a shashi
Hanan na primary 4 a lokacin tana da shekara tara shikuma Salim a lokacin ya daga zuwa kasar us dan abban sa yace bayason karatun sa anan haka ya tafi ya barsu da kewa
Bayan 6month ya dawo da kwalin degree dinsa alhaji Ahmad yayi murna a lokacin Salim nada shekara ashirin da biyar ya girma yayi kima GA wata kasunba daya tara
A lokacin da ya dawo ba irin kiran da baiwa hanan dinsa ba amma ba ita alhaji ya tura India achan take karatun likita inda shikuma Salim ya karanci business
Bayan sati daya da dawowar Salim alhaji ya bashi 5million akan ya zabi duk kasuwancin da yakeso ya yi nan da shekara zai bashi kudinsa nan Salim ya amince ya fara shigo da kaya daga kasar us zuwa Nigeria inda a shekara dayan ya zama millionaire a kasar Nigerian dan indai kanason kayan daki Dana kitchen da kujeru da sauransu ko kayan sawa na mata Dana mazato idan kaje hanan and Salim furniture and enterprises to ka samu duk abinda kake bukata
A cikin 1month ya bawa alhaji kudin sa ya ci gaba da juyawa da NASA inda yanzu ya zama hamshakin mai kudi a garin Kano ta dabo tunbin giwa ko dame kazo an fika
Salim ya kasance saurayi Dan kwalisa mai ji da kuriciyar sa kana ganin Salim kasan yana da kwanciyar hankali ta ko wanne fanni domin komai NASA a nutse yakeyin sa hatta tukin sa a hankali yake tafiya kai kace bayason taka motan nehh
A kofar wani katafaren Gida naga yayi parking na mota din tare da danna Horn a hankali kamar bayaso nan da nan mai gadi ya taso ya bude masa kofah ya cinna hancin motar sa cikin gidan masha Allah nikam bazan CE komai ba dan tsaruwar gidan baza'a iya misalta shi ba komai dai yaji tako ina part biyu nehh a gidan sai parking space sai wani katon swimming pull ta gefe guda kuwa wani gaton gadin nehh Wanda ke dauke da tsuntsatse kala kala kowacce sai shawagin sa yakeyi abin gwanin sha'awa
Kai tsaye parking space ya nufah ya ajiye motar sa ya nufi cikin babban falon gidan da sallama ya shiga ammi dake falo CE ta amsa masa tare da fadin a a Salim Kaine har ka dawo kenan to sannu da zuwa koh
Y amsa da yawwa ammi wlh ja gaji da yawa ammi
Tace sannu kaje ka dan huta zuwa jimawa abinchi yana jiranka yace ammi ai hutun bazai yuyuba abinchin shine mai muhimmanci ya fadi hakan tare da hayewa sama dan anan part din sa yake bandaki ya shi GA ya watsa ruwa sannan ya tare da yin brush bayan ya fito yabi fatar ya share ta tsam da mai sumar Kansas ya taje wadda taji gyara baka ce wulik sai a WANNAN lokacin na samu damar karewa Salim kallo tun daga sama har kasa
Tabbas Allah yayi halitta agun nan dan komai na Salim yayi dai dai da tsarin jikin sa ba Dogo bane ba chan amma yana da fadi ba sosae ba kirjinsa ya kasance mai fadi cike da gashi da yasha gyara abin gwanin sha'awa yana da mirdewar jiki da ka gansa kaga kakkarfah kuma da gani xa'aji maza sosae idanun sa sun kasan ce dara dara yana da dan karamin baki mai dauke da siririn hancin sa ya kasance fari tass kamar ka matsa fatar sa jini ya fito
Haka ya gama taje Kansa ya dauko milk din jallabiyya ya saka ya sauko kasa ya nufi diningda Kansa yayi serving din Kansa dan bayason wani ya sa masa Abu inba ammin sa ba dan yana da kyankyami sosae bayason Kazan ta ba jimawa ya gama cin abinchin ya koma sama jallabiyyar ya cire ya zama na daga shi sai gajeren wando da best wayar sa ya dauka ya hau WhatsApp dan ganin sabbin kayan da abokan sa na kasar us suke San turo masa dashi Nigeria ya
Yana cikin dubawa nehh wata bakuwar number ta masa sallama ko kallon ta baiba dan baya mgn da Wanda bai sani ba dan haka yaci gaba da safgar gabansa kawai ya gama ya kashe wayan sa ya mike sakamokon kira ye kirayen sallan da tayi na magrib
Alwala ya dauro ya saka wata koriyar jallabiyya wadda ta matukar yi masa kyau ya nufi masallacin unguwansu bayan an idar da sallan nehh ya zauna ya dauko al kur'ani mai girma ya hau tilawa bai fito a masallacin ba saisa akayi sallan isha yana fitowa sukayi kicibus da abbann sa
Har kasa ya tsuguna ya gaishe dashi abbansa ya amsa cike da jin dadi tare da sa masa albarka jerawa sukayi suka nufi hanyar gida amma sam Salim bai yarda suka jera tare ba abban na dan gaban sa shikuma yana binsa Kansa akasa kamar daga sama yaji abban sa na fadin
Am Salim yanzu dai ka gama karatun ka ka shiga kasuwanci gadan gadan kuma Allah ya dafa ma yanzu ba abinda ya rage ma sai aure dan shine kadai abinda ya kamata kayi to sabida haka akwai wata yar aminina sunan ta SAMHA baban ta alhaji muktar babban abokina nehh na kasuwanci dan tare muke gabatar da komai to shine mukayi tunanin hadaku gobe idan ka gama duk wani abinda kake yi da yamma driver xai kaika gidan su dan kuga juna ina fatan ka fahimceni
Kansa a kasa yace na fahimta Abba Allah yasa hakan shi yafi alkhairi a gareni
Abba ba karamin dadi yaji ba dan dama yasan baida matsala ta fannin dansa dan haka yayi ta sa masa albarka har suka isa gida tare
Kai tsaye Salim bangaren sa yanufah dake sama ya fada gado ko jallabiyar bai cire ba a fili ya furta aure abba aure fahh yanzu har na kai amin aure tashi yayi ya nufi bakin mirror ya cire jallabiyar sa yayi wulli da ita ya fara kallon kansa yana fadin duka nakeda za'a yimin wani zancen aure 26years fahh kachal gsky Abba da sake amma zanje naga yarinyar amma fahh tun yanzu na fada bazan aureta ba bana santa haka yayi ta surutun sa shi kadai da kyar yayi bacci ranan.............
TOM WANNAN KENAN KUBIYONI FANS LITTAFIN FADILAH KO SAMHA YANA DAUKE DA ABUBUWAN AL'AJABI DA BAN MAMAKI KUDAI MUJE ZUWA
more comment more type
Pls shared
YOU ARE READING
FADEELAH KO SAMHA
عاطفيةLABARIN FADEELAH KO SAMHA LBR NEHH AKAN WANI SAURAYI DAYA FADA TARKON WASU TSALA TSALAN YAN MATA GUDA BIYU DAYA DAI HAIFANTA SUN KASANCE BASU DA KOMAI SAI RUFIN ASIRIN UBANGIJI DAYA KUWA IYAYEN TA MASU HALI NEHH SHIKUMA SAURAYIN YA KASANCE SHIMA MAI...