Ikrarin Dalia

284 24 3
                                    

             Ba lallai na dunga Updating wannan Novel akan Lokaci ba duba ga Azumi na Matsowa and that's why Sai bayan Sallah zan Fara sakinsa yadda yakamata insha Allahu so bear with me.

🅿️02

Wani dan kogo ta hango can gaba da ita wanda bishiyu suka zagaye. Dakyar ta jawo wani karfi ta nufi kogon tana ko'karin shiga taji anfusgo hannunta tana yunkurin ganin waye taji an matse ta nan wani irin duhu ya mamayeta bata gama ankara ba ta daina gani da Jin komai kamar andauke wuta.
A hankali ya karasa sauke ta kasa tare da zame goyon dake bayanta ya ajiye jaririyar agun duk da ruwa na iya tabata wanda hakan yakara ba yar jaririyar daman tsandara wani irin ihu Wanda saida dajin gaba daya yadauka tare da da wani irin giggitacciyar walkiya wanda lokaci guda duhu ya mamaye dajin.

Bayan 'yan dakiku dajin ya dau shiru ba abunda kake iya ji. "Ga jaririyar!". Muryar daya daga cikin masu neman matar ne ya mamaye gun.
Da sauri sauran Suka hanzarta Suka karasa bakin kogon. "Anya tana raye kuwa bata mutuba?". Nan suka Dan tsorata daya ya karasa inda take kwance yanzu ba ruwan Sai digo dis-dis dake diga.

"Dakata karka tabata anya bil'adama ce kuwa? Ina nabarta?". Daga daga cikinsu yayi tambayar a dan rude.
"Dallah Maad kacika tsoron tsiya Kamar ba Namiji ba, hm!". Ya karasa abunda yayinda Wanda yakira da suna jabi yad'an ja da baya sakamakon walkiya da akayi me tsananin haske wanda yatafi tare da hucin muryar mace. 'Azar...'. akafada a hankali tare da jan sunan cikin wani irin sanyayyen murya tare da yar gajeriyar dariya batare da sunga kowa ba sai iska.

Dukansu ba wanda bai firgita cikinsu ba sai dai rashin aikata bukatar Dalia ba karamun fitina bace agunsu.
Cikin karfin hali yakai hannu. "Nafada maka karka taba ba mutum bace bakajiba mur...".
"Shhh! Yishiru dallah muyi mubar dajin nan kafin muzama naman aljanu kunfi kowa sanin wannan wani dajine a Kasar Larza!". Yafada da sauri tare da daukar jaririyar cikin yanayin jarumtaka.

"Muje kam, kila uwarta ma sungama da ita muje". Jiki na rawa na ukun yayi magana.
"Tana raye!". Yafada tare da kura Mata ido daidai lokacin da walkiya ta Haska mishi fuskarta, me dauke da murmushi me kyau duk da a rufe idanunta suke kyakyawace sosai Nan ya so ya shagalta cikin duniyar kallonta.

"Maad muje inka gama iyayin kanayi Kamar kafimu sanin komai bayan Kaine dan kankani cikinmu, Dan dai Dalia ta da'ura kane dake kaima yarone kusan sa'anta shi...".
"Rufe mana baki karka jawo mana musiba kasan irin zancen da zakai da wanda kake zance kafi kowa sanin ba abunda ke buya a idanun Dalia". A bashi amsa a tsorace da sunan wacce ya ambato.

"Fada masa dai bani cikin wannan sabon naka, Ubangijiya Manat kitsareni da tsarewarki daga shiga cikin wani hali". Osan yafada a tsorace tare da daga hannayensa sama.
Maad ne ya shiga gaba ganin zasu bata Masa lokaci Suka bar gun da sauri dan dare sosai ya soma yi ga wani irin iska da ake da walkiya duk da an dan Jima da ruwan ya tsaya.

Suna kwance a daki suna romancing din junansu Dalia ta soma jin wani irin Kara a kunnenta me matuk'ar a zaba, idanunta ne suka sauya take zuwa ja tureshi gefe tayi ta tashi tana Kai hannayenta zuwa kunnenta dakyar take iya hango kayanta data cire ta Soma dauka tana mayarwa. "Lafiya meya faru?". Ya watso mata tambayar sai dai bata wani jinshi sosai.
Haka ta cigaba da maida kayanta da sauri ta fita daga d'akin ganin haka yasa sarki Aaron tashi da sauri ya shiga maida suturarsa shima tare da bin bayanta.

"Dalia Dalia! Lafiya kalau kuwa? meyake faruwane?". Juyowa tayi da jajayen idanunta duk da bata iya jinsa sosai jikinta na kadawa Kamar zata fadi, dakyar ta iya bud'e bakinta. "Ina zuwa bari na duba gurin bauta nadawo". "Amm...". Bai Kai ga idawa kota saurareshi ba ta bace tabarshi tsaye.

Wani dan tsukukun daki ta bayyana gaban wata dattijuwa me baka'k'en Kaya wacce tana ganin Dalia ta shiga sheka dariya.
Kallonta Dalia tayi da jayun idanunta. "Nasan kinsan meke faruwa dani goggona abun sona, kimun bayani azabar tayi yawa lokaci daya Kuma Ina zuwa nan nadaina Jin komai. Meyake faruwane?". Ta jero ma dattijuwar tambayoyi wacce ke kallon zagayen wutan batare d ta waiga ta kalla Dalia ba.

"Tana nan, nasan da isowarta tabbas wacce zata rusa kasar Larza da duk abunda ke cikinta, wacce zata kawo sauyi da banbance-banbance a wannan kasa harma addini wacce zata zamo mace tafarko da zatai Mulki me kyau da adalci girmamawa a Kasar Larza, Wacce har Makofta Larza Zasuyi sha'awar kasancewarta shugaba a gare...".

"Wacece?!".
Dalia tayi maganar cikin daga murya da zafin rai tare da bugun bagon d'akin wanda harsaida ya girgiza.

Murmushi Goggon nata tayi. "Ba'a bani dama da ikon sanar miki wacece ba amma idan lokaci yayi zaki san wacece". Tafad'a tana murmushi.
"Karki fadamun kinmanta irin azabar da kikasha sakamakon ko'karin sauya tsarin addini Wanda haryanzu kike ciki, kina ganin har wata can da ba'asan wacece ba zata iya nasarar abunda Kika gagara shekara da shekaru?". Dalia tayi tambayar cike da isa da tinkaho ta cigaba da magana.

"Ba wata mace da zatai shugabanci a Kasar Larza saini Dalia! Dalia!! Nice dai!!!". Tafad'a cikin daga murya Wanda hakan yayi dai-dai da saukar wani irin tsawa me girgiza me sauraro tare da Hasken walkiya me haska komai kamar rana. "Ki sani ba wata Bokanya da zatai suna da Mulki kamarni Dalia a wannan kasa". Ta k'arashe maganar tana nuna kanta.

Murmushi goggonta ta Kuma me sauti wannan karon tare da tashi tsaye Sai a lokacin ta juyo suka fuskanci juna. "Zauna na duba ki bazaki Kuma Jin radadi ba". Goggon nata tayi maganar tare da dauke kanta.

Batare da tayi musu ba ta kalleta da jayun idanunta ta nema guri ta zauna tare runtse idanunta maganar Goggon nata ke Mata yawo ta tsorata matuka dan goggonta Bata tab'a fadan abunda bai faruba ko ba haka ba tunda suke.
Nan ta Soma tunanin ko wacce Sarkinta masoyinta zai aura ne zata maye gurbinta har ta zama hakan 'ya Zama Dole na zaba Mai Mata tunyanzu'. Tafad'a a ranta Wanda ada sam bata kaunar ace zaiyi aure sam amma Jin wannan yasa ta soma tunanin yadda zata Kare duk wata kofa da Aaron dinta zaiga mace harya aura tasama Mulki muddin ita ta da'ura ta tabbatar ba makawa Sai abunda taso matan zasuyi shiyasa takeda burin zaba mishi marasa wayo a cikin matan kasar, Wanda bazasu iyaja da umarninta ba.

Fadar Sarki Aaron...

Dalia na fita su Maad suka shigo dauke da jaririyar.

Sarki Aaron na ganinsu ya taso ya nufosu baijira sun iso gabansa ba ganin abunda ke dauke a hanun Maad. "Kunsamota?".
Zubewa sukai a kasa gabansa. "Ayi Mana rai ran sarkin Lar...".

"Dakata wannan jaririyar fa?!". Ya Kuma tambayarsu. Kallon juna sukai su duka tare da sauke ajiyar zuciya saboda tsoro da fargabar rashin samun uwar.
"Ba...b..bamu sama damar samun maman ba sai ita...". Ya karashe maganar a dan firgice saboda kallon da Sarki Aaron ke binsa dashi.

Mika hannu yayi "muganta".

Maad a tsorace ya tashi ya mika ma Aaron jaririyar ya koma baya ya zube Kan gwiwowinsa  suna cigaba da rokonsa gafara Amma Sam baya jinsu,  haryanzu idanunta ke rufe.
Buda fuskarta da ke rufe yayi Wanda hasken fitulu Dake fadar take Suka haska mishi ita, baisan meyasa ba tunda ya dauketa yaji wani irin sanyi kallonta lokaci guda yaji jaririyar ta shiga ransa.
Dan motsata yayi amma sam ba alamun mosti tattare da ita kallonsu yayi a firgice. "Ta mutune?!". Ya tambaya cikin firgici.

Girgiza Kai Maad yayi. "Aa sakamakon ruwa da tash....".

"Me kuke jira akawo me magani yanzu yanzu!". Da sauri Suka Mike yayinda ya koma ya ajiye jaririyar Kan gadon mulkinsa hankalinsa atashe yanayi yana lekenta.
Tun Yana yaro Allah yamishi son kana Nan Yara Kasancewar yataso cikin tsananin kadaici baida buri irin na yasama dan uwa.
Kan kace me fada ta rude hankalin 'yan fada yayi dubu ya tashi cikin banda maganganu da mamaki da gulmace-gulmacen ma'aikatan Fadar ba abunda kd tashi Kasancewar su suka kashe uban Jaririyar da wasu naganin ankashe uwar to meyasa ya damu da yar.

Cikin kankanin lokaci Mai magani yazo baiyi wahala ba wajen ceto rayuwar Jaririyar Aaron yayi farin ciki da murna kwarai.
Inda yasa aka nemo Kaya aka shiryata.
Bayan ta farfado yasa aka shayar da ita Madara sakamakon kuka da take daga nan ya amsheta duk abunda zakai Mata Sai a idonsa banda dariya ba abunda yake mata yana mata wasa abunda yake ba kowa mamaki kenan labari ya gama yaduwa har wajen Fada sai dai Dalia bata da wannan labarin.

Shima Sarki Aaron a yanzu damuwarsa baiwuce yadda zasu Kaya da Masoyiyar tasa ba ya tabbatar taga yarinyar sawa zatai a kasheta, shikuma bazai iya ganin wannan rashin Imani ba.









                     Tirkashi koya wannan lamari zai kasance... Wacece wannan wace ake jiran zuwan ta..? Shin Dalia zata bar wannan Jaririyar...?.

Boyayyar MasarautaWhere stories live. Discover now