Alhamdulillah Alhamdulillah! I am alright, Aiki yayi kyau sosai anyi Nasara Inagodiya sosai da kulawarku da addu'oinku gareni Allah Ubangiji yakara mana lafiya baki daya...wannan page yana pending nace bara na sake muku kusha karatu lafiya inakara Godiya sosai🙏 Banyi alkawarin daily Post ba as I am still not that well enough inakara godiya da addu'oi.
🅿️08
“Waye?”. Dalia tayi tambayar cikin muryarta dake rawa. Dariya aka tuntsire dashi cikin wannan muryar. Dalia sake zaro idanunta waje tayi tare da hadiyar wani wahalallen miyau, lokaci guda wani irin kwarin gwiwa yazo mata tuna wacece ita. “ Koma wacece ke ki bayyana gaban Dalia inba tsoro ba!”. Dalia tayi maganar cikin karfin hali tare da daga kanta wanda ke nuni da ba tsoro a tattare da ita a wannan lokacin. Lokaci guda wata kyakyawar mace ta bayyana gaban Dalia cike da murmushi kan fuskarta cikin irin kaya masu yanayi da shigar Dalia. Cike da mamaki Dalia ta zaro ido tana kallonta.
“ Bogairah!”. Dalia tafada da labbanta dake kadawa. Yayinda wacce ta kira da Bogairah ke murmushi tana kallonta. “ Tabbas! Bogairah ce ba Dalia”. Takarashe maganar tana kallon Dalia wacce ke tsaye tana kallonta cike da mamaki. Murmushi Bogairah tayi wanda iya labbanta murmushin nata ya tsaya tana kallon Dalia. “ ki daina mamakin bayyanata gareki yar uwata, duk inda nake a duniya bani mantawa dake kina raina a koda yaushe”. Ta tsagaita maganar tare da zama gefe, wani ajiyar zuciya ta sauke me huci tare da runtse lumshe idanunta ta budesu kan Dalia.
“ Banji dadin yadda naganki ba yar uwata”. Hadiyar wahalallen yawu Dalia tayi tare da bata fuskarta ta koma ta zauna gefe tana kallonta. “ Meya kawoki Larza bayan inban manta ba anharamta miki shigowa cikin wannan daular gaba daya?”. Dalia tayi maganar cikin dakiya batare data kalla inda Bogairah ke zaune ba. Jin kalaman Dalia yasa Bogairah yin murmushi medan sauti kafin ta koma ta dake. “ Washh!”. Bogairah ta furta lokacin data tashi tsaye tare da yar mika. Binta da ido Dalia tayi da kallo cike da mamaki da damuwar abunda ya bayyana yar uwartata a wannan lokacin.“ Da alama ‘yar uwa baki farin ciki da zuwana”. Ta fada tare da wurga mata wani irin kallo. Jin haka yasa Dalia saurin dauke kanta. Murmushi me sauti sosai Bogairah tasa. “ Bari naje gurin Masoyina kila shi yana da buka…”. “ Shiru!”. dalia tayi maganar a fusace lokacin data tashi tsaye kallon juna sukai da Bogairah dake mata murmushi. “ Haba yar uwa karmuyi haka dake mana anjima ban ganshi ba nasan a matse yake ya ganni”. Tayi maganar cikin sassauta murya da murmushi dake kwance kan fuskarta tana dan kakkada kafada. Lokaci guda kuma yanayinta ya sauya ta tabe fuska. “ Natafi!”. Tana fada batare data ankaraba Dalia cikin zafin nama ta nuna ta da sandar tsafinta wanda ya fitar da wani irin haske me walwal ya tunkari Bogairah, wacce itama cikin zafin nama ta kauce suka hada jajayen idanunsu wanda ke nuna tsananin bacin rai.
Sun dan jima a wannan yanayin suna kallon juna kafin lokaci guda Bogairah ta tuntsure da wata iriyar dariya me gigita duk mahalukin dake saurare. Har wannan lokacin Dalia tsaye take tana kallonta yayinda bacin ranta ke kuma nunkuwa, inda ta kara daga sandarta dan kaima Bogairah hari a karo na biyu, sai dai bata kaiga nasaraba tajita cikin igiya a nannade. Tuni Bogairah tariga ta wannan karon. Kokarin kwace kanta Dalia ta shiga yi daga nadin igiyar me haske anma ba alamun sa’a, cikin fushi ta dago jayun idanunta tasa kan na Bogairah dake tsaye tana murmushi hannunta ayaba ne data bare tana ci. “ Karki manta Dalia haryanzu bakida karfin da zaki iya karawa dani! Eh zaki iya zama ba kamarki a karfin tsafi a Larza anma kisani nima a tawa kasar babu kamata haryanzu haka kema nafi krfinki kamar yadda nafi saura”. Tsagaitawa tayi lokacin data gutsuri ayabar dake hannunta.“ Karya kike Bogairah ba abunda zaki iya mun”. Dalia dake cigaba da struggling din kunce kanta tafada tana kallon Bogairah da jayun idanunta. Murmushi me sauti tayi. “ Zamu gani, kina batamun lokacin ganin masoyina, natafi!”. Tana kaiwa nan ta bace bat. “tsa…”. Dalia bata samu damar karasawa ba nan tashiga tsaki inda ta kara dage tsafinta dan yunkurin kwance kanta.
YOU ARE READING
Boyayyar Masarauta
General FictionHidden kingdom wato Boyayyar Masarauta labarine me cike da abubuwan ban mamaki...inda Azar zata fuskanci kalubale da dama. Azar yar Sarki Nazdal ce daya haifa tare da daya daga cikin matan da aka zaba dan zama