The Fear

270 16 0
                                    

             

🅿️05

" Waye a kusa?". Muryar sarki Aaron ce ke wannan tafiyar duk da bata fita dakyau saboda kukan jaririyar data karade ilahirin dakin. Kallon yar jaririyar yayi cike da tsananin tausayi da damuwa, yana matuk'ar tausaya ma yar jaririyar sosai, Dan jijjigata yake, tare da  daurata akan Kafadarsa gaba daya yarasa me zai mata tayi shiru.
        Bayyanar Dalia a d'akin lokaci guda yasa yadan ja da baya kadan. yana wurga mata wani irin kallo me cike da sakwanni. Da za'a bud'e kirjin sarki Aaron a wannan lokacin da yake bugawa cike fal da tsoro da fargabar abunda ke tafe da ita ko take shirin aikatawa kan jaririyar, kallon jaririyar hannunsa yayi tare da maida dubansa gun masoyiyar tasa.

Shiru tayi batare da tayi yunkurin komai ba musamman ganin yadda yake a gigice da irin kallon da yake mata. Dan taka kafarta tayi da alamun yunkurin karasawa gunsa amma ga mamakinta kan tayi taku nabiyu yayi saurin ficewa d'akin da sauri. Wani irin takaicine ya rufe ta amma tuna shawarwarin da mahaifiyarta ta bata yasa tabi bayansa da sauri. "Wai ina zaka kana ganina kafita". Tsura mata ido yayi daidai lokacin da wasu nayi guda biyu suka shigo fada.
           " Ran sarki ya da...". "Kumun shiru! Kuna Ina tuntuni nake kira ba wanda ya am...". " Manat ta huci zuciyar me daular Larza!". Ta katse fadan da ya rufe ido zaiyi ta hanyar Mai kirari. Cike da mamaki daga shi har bayin suka kalla Inda take tsaye. Murmushi ta mishi wanda hakan ya Kara jefashi cikin wani sabon fargaba. Kallon Inda bayin suke tayi wadanda sukai sakare suna kallonta da sauri sukai kasa da idanunsu sanin halinta.

Karasawa tayi inda Sarki Aaron ke tsaye. Ta riko hannun yar jaririyar wacce a yanzu tayi shiru sanadiyar da daya hanunta a baki tana tsotsa. Fadada murmushinta Dalia tayi. " Yar jaririya mekyau". Tafad'a tana murmushi tare da wasa da hanun jaririyar. Sarki Aaron kam kasa Koda kwakwaran motsi yayi, Jin yayi shiru yasa Dalia ta Kuma dagowa cike da fara'a fuskarta ta kalleshi. "Meye Sunanta?". Ta tambaya.
          Sai a lokacin ya kalleta tare da shock. " Am...uhm...Ina zansan sunanta". Ya furta lokaci guda tare da kau da kansa yana ko'karin sassaita kansa. Dariya tayi me sauti wanda hakan yasa Sarki Aaron maida dubansa kaf kanta yayinda take dariyar tana rufe bakinta da hannu sosai hakan ya masa kyau. Babu abunda ke kwantar mai da hankali yaji yana kara sonta irin wannan yanayin.

Ganin ya shagalta da kallonta yasa ta sassauta dariyar tata. " Ina zaka sani? Dole zaka sani mana tunda tare ka kwana da ita dakinka jiya. Kaga inma baka sani ba saika saka Mata ko". Tayi maganar tare da cigaba da murmusawa tana wasa da hanun jaririyar.

Daya daga cikin Bayin murmushi tayi tare da tabo yar uwarta da sauri tana nuna mata Dalia. Da sauri ta cire hanun dayar tare da hararta saboda tsoron abunda zai iya biyo baya. Sake Kai hannu tayi zata tabata a karo na biyu Inda dayar ta janye da sauri, hakanne ya jawo hankalin Dalia kansu inda cikin kankanin second ta hade fuska kamar ba ita ke dariya ba. "Kuna iya tafiya ku kawo Madara a nan zan bata". Tayi maganar cikin murdewa.
         Mamakine sosai ya Kara kama Aaron zata bata?. Su kansu Bayin Saida suka kalla juna. " Me kuke jira!". Tayi maganar cikin daga murya da son abi umarninta cikin sauri da zafin nama suka juya. Ganin sun tafi yasa tadan yi siririn tsaki ta juya kan Sarki Aaron tare da daura murmushi Kan fuskarta. Still har wannan lokacin ita yake kallo. Mika hannu tayi tana ko'karin daukar jaririyar jin alamun motsi yasa yayi saurin janyewa.

"Mezakiyi?!". Ya furta da sauri yana kallonta a dan razane. Murmushi tayi tare da kai hanunta ta rufe lips dinta sai dai bata jima ba ta sauke hannunta tare da saita kanta. "Bakaji nace a kawo Madara ba zan bata ne". Ta Ida maganar tare da matsawa gab dashi.
           Yana ko'karin magana Maad da wasu daga cikin 'yan rundunarsa suka shigo. Hakan yaba Dalia damar daukar yarinyar da sauri, sai dai bata Kai ga komai ba ta jaririyar ta sake mata fitsari a jiki. Cikin fushi Dalia ta saki yarinyar cikin gaggawa dake idonsa nakai ya tarbeta. Dalia kuwa tuni ta bace a Fadar. Maad yayi matuk'ar mamakin hakan ganin ta da jaririyar sai dai bai fahimci abunda yasa ta bace ba. Murmushi sarki Aaron yayi kasancewar shi yagama shan wannan duk da ya tsorata nan yake shaida ma Maad abunda tama Dalia.

Boyayyar MasarautaWhere stories live. Discover now