Sabon Yanayi a Larza...

81 6 2
                                    

                  Alhamdulillah! Finally wannan littafin yadawo asha karatu lafiya...🤗

🅿️12

Ta jima bata ga wannan yanayin daga gun Maad ba, hakan yasata tsananin mamakin gaske da farin ciki. " Muje ko?." Ya fada tare da dan yin gaba. Murmushi tayi me sauti wanda harsai da Maad yaji sautin fitarsa, haka kawai ya tsinci kansa da maida mata da martani mara sauti batare da tasan yayi ba.

Motsin giftawan wani abu suka soma ji wanda basu iya ganin komenene. Tuni suka soma kokarin neman abunda ke faman zagayensu yana giftasu da sauri-sauri yayinda Dalia ta fidda wani sauti wanda lokaci guda haske ya bayyana gun. Hakan yayi daidai da lokacin da Maad ya kama wani abu me ban tsoro wani irin halitta tare da fitar wani irin sauti a tsorace Maad yayi jifa da abun sai dai me abun yayi nasarar cizon sa a yatsa tuni.

" Dalia me..." Batare da ya idda furta kalamansa ba ya fadi kasa warwas. A guje Dalia ta isa gabansa ta durkushe inda tashiga Kiran sunansa tana girgizawa. Ganin abubuwan sautinsu na karuwa suna kara nufo inda suke ta daga kanta tare fidda wasu irin sauti wanda yake fita kamar radi, nan take suka bace tare da Maad wanda a yanzu baisan halin da yake ciki ba. Nan take suka bayyana a fada yayinda lokaci guda yanayin Maad ya sauya yayi wani irin haske duk da dama shi din ba baki bane anma kallo daya zakai masa ka fahimci sauyin da ya samu. Bakinsa yayi fari fat gashi yana wani irin kadawa, shafa fuskarsa tayi tana Kiran sunansa jikinsa yana wani irin kyarma, banda girgiza ba abunda jikin yake a kas idanunsa a kuwa sun firfito sunyi fari fat.

Ihun Dalia ya ankarar da jama'ar fada bayyanarsu, yadda take Kiran sunan Maad cike da fargaba da tashin hankali cikin kankanin lokaci sarki Aaron da Sarauniya Zoona suka bayyana a fada. Ganin abunda ke faruwa ya tada hankalin kowa a fada. " Ayi maza a taro masu magani da matsafar duka wannan masarautar yanzun nan!." Sarkin Aaron yabada umarni. Dakyar ya isa ga Dalia ya rabata da Maad ganin idanun bayi kan abunda ke faruwa, yajima da sanin son da take ma Maad shi shaidane sai dai in hakan ya tabbata a idon jama'arsa zaisa kimarsa zubewa ace masoyiyarsa na kula da bawansa duk da Maad abokinsa ne kuma yana daga cikin wadanda ake ji dasu a masarautar sai dai yana kasansa.

A hankali Sarki Aaron ya janye Dalia daga jikin Maad wanda a yanzu yadaina jijjigar ya tsaya cak shiru sai kwayoyin idanunsa da suke nan fari sol haryanzu. Ganin haka yasa Dalia fusgewa daga jikin Sarkin tare da cire rigar sanyin daya rufa mata, ta rufa a jikinsa tare dama kanta mazauni gurin. Janyo shi tayi zuwa jikinta tana Kai hannayensa kananun lips dinta tana hurawa tare da gogga su a hannayneta duka a rikice take.

Sarki Aaron cikin wani irin yanayi ya sallami bayi kaf daga harabar fadan shima ya rage tsawonsa ya shiga taimakon ta. Ganin ba sauki yasa Dalia tashi ga whispering wasu irin abubuwa wanda baka iyajin me take fada sosai sai bakinta dake faman motsi da sautin dake fita kadan-kadan idanunta a rufe. " Wai meya same sane? Meya faru?." Sarki Aaron ya shiga jero tambayar yana kallonta yana duba yanayin Maad.

Hayaniyar jama'a ne ya tunkaro fadar Sarkin wanda ke faman kallon makusantan nasa guda biyu. " Ran Sarki yadade, ina dauke da sako maigi..." " Fice yanzu ba lo..." Shigowar ilahirin jama'a cikin fadar ne yasa Sarkin Aaron saurin gimse kalamansa musamman ganin yadda ake shigowa da mutane kamar matattu fadar. Iya zafin Kai Sarki ya shiga a wannan lokacin hayaniyar ya haddasa ma Sarauniya Zoona shiga wani yanayi me cike da fargaba da sauran bayin. Sai dai haryanzu Dalia bata dawo daidai ba bare ta bada wata taimako ko mafita.

" Meke faruwa, meya faru?." Sarki Aaron ya jero ma jama'arsa da tambayoyin cikin kidimar ganin yadda ake kan shigo da mutane. " Ran Sarki Aaron yadade. Wasu irin abubuwane masu cizo suka bayyana a  Masaautar Larza masu munin kamanni da bantsoro." Daya daga cikin mutanen yayi maganar.

" Tabbas! Ban taba ganin halitta irin wànnan ba. Farine fat bashi da jiki sai Kai sai wasu irin munan hakora, abun inya tunkaro mutum ba'a ganinsa harsai ya iso sai dai akan iya ganin innuwarsa." Wani cikin samarin ya amsa. " To Kai, Mizul kaga abunne da har kasan ana iya ganin inuwarsa." Daya daga cikin matsafan wanda yashigo fada yayi tambayar. " Koma meye a taro majiya karfin wannan kasa suje su nemo wannan abun, Kai Kuma ba wannan yasa nasa a nemo kuba ku gaggauta nemo mafita." Sarki Aaron yayi maganar yana mekarasa wa ta hanyar kallon Dalia wacce haryanzu idanunta ke rufe tana faman kada Kai tare da lips dinta dake faman mommotsawa.

*****
" Maad! Maad!! Maad!!!." Muryar mahaifiyarsa ce ta karade ilahirin dakin. A hankali Maad ya bude idanunsa akan na mahaifiyarsa dake tsaye tana kallonsa. " Katashi?." Ta tambayeshi. Cike da matsanancin mamaki yake duban ta, ' bata mutu ba? Meya kawo ta na...' " Maad, kayi maza kazo muci abinci babanka najira." Tayi maganar tare da murmusa mishi ta juya tafiya dakin.

" Meyake faruwa Dani? Mafarki nake?." Maad yayi ma kansa tambayar wacce baisan amsarta ba. " Maad!." Muryar mahaifinsa. Cikin zafin nama ya amsa tare da ficewa daga dakin. Tun kan ya kaiga karasawa yake jin dariyar mahaifinsa da alama yana cikin tsananin farin ciki a wannan lokacin. Koda ya karasa ya tarar suna hiransu ta jindadi sosai. " Karaso mana." Mahaifiyarsa ta fada, karasawa yayi ya nema gefe ya zauna inda mahaifinsa ke ci gaba da zolayar Maman sa itama tana mayar masa yayinda kowanne ke neman Maad daya goyi bayansa.

Maad ya tsinci kansa cikin wani irin farin ciki mara misaltuwa. Inda ya soma tunanin kila a baya mafarki yayi mahaifiyarsa tana raye kuma tana cigaba da zama da mahaifinsa cikin nishadi.  Suna zaune suna cin abinci Dalia ta shigo cikin shigarta ta high priestess nasu na manyan Bokayen Masarauta. Maad yayi mamakin ganin Dalia a gidansu musamman yadda mahaifiyarsa da mahaifinsa ke nuna kulawarsu gareta. " Ran 'yata Dalia ya Dade kin karaso." Mahaifiyar Maad tayi maganar tana murmushi.

" Dalia mekike a nan?." Yayi tambayar cikin rudu. Murmushi Dalia ta mishi batare da tace komai ba. " Karaso kici abinci, faranta miki daidai yake da faranta ran abun bauta Maanat." Mahaifin Maad yayi maganar tare da mata alamun inda ta karasa tana dariya ta zauna gab dashi. Sai a lokacin Maad ya soma tunanin fahm da 'yan uwansa, kusan baiga alamun su a gidan ba tun tashinsa.

" Banga su Maalikh da Maalikha ba." Cike da mamaki su duka ke kallonsa. " Suwaye wadan nan Maalik?." Mahaifiyarsa tayi tambayar. ' kodai duka amarkine nake da 'yan uwa da mamansu fahm?.' ya jero ma kansa tambayar wacce shi kansa bashi da amsarsu. Haka ya dage sukaci abinci, sai dai suna cikin ci Sarki Aaron yayi aike kan yana nemansu shida Dalia kan batun aurenshi shida ita.

Labarin ya matukar ba Maad mamaki kan tun yaushe ne ake Shirin aurensa da Dalia? Kuma ya batun soyayyarta ita da Sarki Aaron me hakan ke nufi. Kwana nawa yayi yana wannan bacci wadan har yayi dogon mafarkan?.

***
2days later...

" Nakasa fahimtar meke faruwa a Masaautar nan. Kana nufin haka zamu barsu a kwance ba magani suna numfashi kuma bawani sun mutu ba?." Sarki Aaron ya jero ma mai maganin tambayoyin. Ranka yadade ka kwantar da hankalin ka na tabbatar megirma Dalia zata samo mana mafita wajen abun bauta Maanat." Yayi maganar yana Mai nuna tsantsar yadda ga abunda ya fada.

" Nikuwa intambayeki mana." " Zaki iya tambayarki mana." Ta bata amsa. Bayin su biyu suna zaune suna gyara abun kendir wanda suke zagayen bakin bishiyar bautar. " Naji ance tunda Dalia ta shiga dakin baya bata fito ba." " Ke Atiya ki iya bakinki banso a hada dani kinfi kowa sanin ba'a zancen Megirma Dalia, Dan haka kikiyaye." Ta tsawatar mata dan su cigaba da gudanar da aikinsu.

Bokanya Dalia tsaye cikin kogon wanda banda karar zubar ruwa ba abunda kakeji tare da muryar Dalia wacce ke faman tsafe-tsafenta. A gabanta Maad ne kwance saman ruwan wanda ke zagaye cikin ramin. Tanayi tana mika hannunta wanda duk sanda ta mika hanun sai Maad ya taso sama daga ruwan sai kuma ya kuma fadawa. Wata iriyar dariyace ta bayyana cikin Dan kogon mai duhu. Dalia ta fahimci waye koda ba'a fada mata anma hakan bai hana ta fasa abunda take ko bude ido ba.

Bayyana tayi lokaci guda bayan Dalia. " Manaat yaji tausayinki 'yar uwata." Tayi maganar tare da fitar da murmushi me sauti yayinda ta soma zagayowa zuwa gun ruwan wato inda Maad yake. Lumshe ido tayi lokacin data Kai hannunta ruwan zata ta bashi. " Maad  kenan abun sona." Tayi maganar tare da yunkurin taboshi, cikin rashin sa'a Dalia tayi saurin sama dashi. Juyawa tayi ranta a bace fuskarta sai kuma tayi murmushi mai sauti.

" Maad, ya shiga cikin bacci, me mafarki me dadin da bazai so ya tashi ba." Tayi maganar tare da sake kyalkyalcewa da wata iriyar dariya. Dalia kuwa jin furucinta yasa ta bude idanunta inda lokaci guda Maad ya kuma fadawa cikin ruwan batare da ta iya tare saba. Lokaci guda Bogairah ta bace bat sai karar sautin dariyarta. Sosai Dalia ta shiga rudu tare da Kiran sunanta da bayyana ko tasan abunda ke damun Maad anma shiru ta bace dariyar ma tuni tadaina ji. Yazama dole Dalia ta nemo Bogairah kodan samun mafita ga masoyinta ga kuma Masarautar Larza.....













Mekaratu nan nakawo karshen wannan shafi kucigaba da bibiya dan jin yadda za'a karkare insha Allahu. Zandunga update biyu a Sati Insha Allahu. Kar amanta da comments and vote🤗

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: May 16, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

Boyayyar MasarautaWhere stories live. Discover now