The Name Azah/Azar

249 21 7
                                    

                     Asha karatu lafiya🙏 Juma'at Mubarak.




🅿️06

Cikin sanyin jiki Maad ya karasa Inda suke tsaye suke tattauna wa ganinsa yasa sukai saurin fadada fara'arsu kamar basu ke sukan saba. "Gaskiya Maad kaji dadinka Kai kam". Ya fada tare da daura hannunsa Kan kafadar Maad yayinda yake ma Daya daga cikinsu ido yana nunasa ta baya. Murmushi Maad yayi me sauti tare da dan janyewa daga rikon yana gyara rigarsa.
         "Muje". Ya fada tare da tafiya yayinda su Kuma suka kalla juna Suna turo baki. Cikinsu ba Wanda bai girme ma Maad din ba. Amma hassada da kyashi ya musu yawa akansa. Waigawa Maad yayi jin baiji takunsu ba a bayansa. "Kodai Kun ganine?". Daga mishi Kai sukai. "To kuyi zaman ku nima inaga saina je gida nayi wanka". Ya fada tare da dan shafa kansa. "To kaje kawai karka damu zamu hadu anjima". Daya daga cikinsu ya fada yana kallonsa.

Murmushi Maad yayi mara sauti. Sai dai murmushine me matuk'ar Kara bayyana kyawunsa duk sanda yayi ta ba ga Mata kadai ba har maza inyayita Sai sun kalleshi sun Kuma. Tsura mishi Ido su duka yayi yayinda Maad ya juya yayi tafiyar sa. "Oh ya Manat! Kaga wani irin murmushi da yayi kuwa". "Nagani!". Dayan ya fada cikin kosawa tare da juyawa. "Gaskiya Manat tayi halitta a Kan Yaron nan ka duba kaga yadda bakinsa ke lotsewa inyayi dariya woh! Ya hadu! Nayarda dole Mata da mazan garin nan su dunga sonshi". Ya karashe fada yana kallon hanyar da Maad yabi.
       Waigawa yayi yaga wayam hakan ya tabbatar masa tuni abokinsa da abokan tafiyarsu suka watse suka barshi. "Kujirani!". Ya fada da k'arfi tare da yin kwana a guje.

Fitan su Aaron shiru yayi tare da rufe fuskarsa da tafin hanunsa. "Ran...". "Ban son ganin kowa yanzu!". Ya fada da k'arfi cikin fushi ba tare daya bud'e idanunsa ba. "Nasan za'a rina tunda naji ance kuna meeting da Maad". Datijjuwar matar tafad'a tare da karewa da murmushi. Da sauri Aaron ya bud'e fuskarshi tare da tashi daga Kan kujerarsa lokaci guda ya fadada murmushinsa ya nufi inda take tsaye. "Goggona sannu da zuwa". Ya fada tare da riko hannayenta yasa kansa ya sumbaci tafukan hannayen tana mishi murmushi.
         "Muje ciki kaci abinci, nasan haryanzu baka karyaba". Gyada Mata Kai da sauri tare da bin bayanta da kallo ganin bayinta rike da baskets wadanda kana gani kasan kwanukane  ciki. Bai saki hannunta ba suka nufi wata kofa Kan ta shigane ta waigo tama bayin umarni dasu shirya komai Kan su kawo. " Haryanzu kana jin wani abune tattare da Maad?". Ta mai tambayar tana kallonsa yayinda suke shiga falon me dauke kayayyakin alatu komai kagani gold ne a kayan decoration din d'akin.

Zaunar da ita yayi bakin kujera tare da kai gwiwowinsa kasa ya cire hular sarautarsa ta mulki ya ajiye a gefe ya karasa ma kansa mazauni gabanta. Cike da so take kallonsa idanunsa kuwa suncika kamar me jiran abu kadan su zubo. Kwantar da kansa yayi akan cinyarta tare da lumshe idanunsa lokacin data shigar da hanunta cikin sumarsa.
       "Na tambayeka baka ban amsa ba". Ajiyar zuciya ya sauke nannauya tare da bud'e jajayen idanunsa. " Goggona". Ya Kira sunanta cikin wani siga me wuyar fassarawa. "Uhm, inajinka". Ta bashi amsa tare da leken fuskarsa. "Haryanzu nakasa banbance me nake ji game da Maad. Sau tari nakanji kamar ina kishi akan yadda Dalia ke nuna Kulawa kansa ne Sai dai...". Katsewa yayi tare da yin wata siririyar murmushi me sauti wacce ya idda da hadiyar wani daddacen miyau. Tana kallonshi.

" Koda wasa bazan taba yadda nayi kuskuren da mahaifina yayi ba wajen son jinsin sa. Nataso naga yadda mahaifiyata ta Kasance cikin bakin ciki wanda haryanzu duk da tana raye bata da maraba da matacciya ban sama gatan da da ke samu gun uwaba da bake bansan yadda zan kasance ba Goggona". Ya karashe tare da dago Kai yana kallonta yana wasa da hannunta. Idonta tuni suka cicciko.
          "Bazan taba bari irin wannan abubuwan su Kasance a wannan Masarautar ba, saboda irin barnar da hakan yaja a lokacin mahaifina". Ya karashe tare da kwantar da kansa cikin tafin hannunta. "Aaron". Takira sunansa cikin sanyin murya me cike da dumbin tausayi. " Karka bari zuciyarka ta dunga sanar maka da abunda yake ba haka ba. Karka manta Maad tare kuka taso Amininka ne shakuwa da so irin ta abota musamman Wanda kuka taso tare dolene, bana jin kulawarka gareshi Wani abune daban". Ta karashe tana kallonshi shima itan yake kallo.

Boyayyar MasarautaWhere stories live. Discover now