Cacanta

135 13 0
                                    

                   Asha karatu lafiya...Kar a manta ana comments...👌

🅿️10

“oh ni Zabyna ‘yar Babana, wannan kyau  ina zaki kaishi Malikah?”. Jin kalaman Zabyna yasa Malikah sake kallon kanta cikin mudubin tare da murmushi tana murje janbakin data shafa ‘yan labbanta. “Zabyna kenan”. Daya daga ke zaune gefe tayi maganar tana kallon Maalikah yayinda itama take gyara fuskarta. Tabe fuska Zabyna tayi da sauri tare da sake gyara kinshigidarta. “ yanzu kuma laifin me nayi Naz”. Tayi maganar cikin  dakiya wanda kedan nuna bacin rai. “ya isheku haka sarakunan fada, kunsan dai kaf ‘yan matan garin nan ba mai kyauna ko?”. Tayi maganar tare da binsu da kallo. Kallon juna Naz da Zabyna sukai tare wanda ke nuna kishin abunda ta fada. Kallonsu tayi ta dauke kai tare da murmushi ta cigaba da gyara tsadajjen awarwaron hannunta. Murmushin  yake dukansu suka soma. “dama kaf garin nan wazai iya ja dake a kyau ae babu”. Naz tayi maganar tare vda kebe baki tana kallon daya gefen.

          Tashi Maalika tayi tana murmushi cikin yanga take shafa fuskarta jin yadda suka zuzuta kyan nata. Kallonsu tayi su biyun kowa kansa na kallon wani bangaren takai hannunta tana gyara gashin kanta. “ Mamana tace yayana Maad zaima Sarki da Bokanya Dalia magana kan zancen aurena da Sarki Aaron”. Dukansu juyawa sukai gunta tare da tashi tsaye fuskarsu dauke da mamaki. Hada hannayenta tayi gu guda tana kada idanunta yayinda take yanga tana juya idanunta cikin wani irin salo dake kara mata kyau. Nan suka shoga binta da tambayoyi dan tabbatar da gaskiyar abunda take fada amma ga mamakinsu juyawa tayi ta kama hanyar fita dakin. “sai anjimanku”. Tafada batare data juyo ta kallesu ba tayi tafiyarta. Naz taso binta Zabyna ta jawota tayi mata alama data barta ta tafi amma ina tureta tayi tabi bayan Maalikah tana kwala mata kira harta taddata.

***************

Atika ce tsaye ita kadai a dan bakin jejin, banda kaiwa da komowa ba abunda take kallo daya zakai ma fuskarta ka tabbatar akwai damuwa a tattare da ita. Tsayawa tayi tana kara leken dajin tare da cinno bakin ta wanda ke nuna bacin ranta sosai. Sa hannayenta tayi akanta tare da dan ja ta tsaki tana mai busar da wani iskan hucin takaici. “ Ya Manat! Kina ganin komai. Meyasa kikayoni a dangin bayi memakon sarauta?”. Tayi maganar tare da dan bubbuga kafar. Kome ta tuna saita kama kugunta da hannunta na hagu tare da lelleka dajin. “ Wa take gani a daji haka a maimakon cikin gari haka”. Atika tayi maganar tare da yin dan ta gumi. “uhm, anya Goggon Sarki ba abunda take shi…”. Jin motsin takun Goggon ne yasa tayi saurin katsewa tare da gyara tsayuwarta. Fitowa goggon tayi sai dai kallo daya zakai mat aka fahimci bacin rai da damuwa sosai.

        “Muje!”. Tayi maganar tare da wuce Atika da sakeken baki data bude me dauke da tsananin mamakin yanayin Goggon wanda bata taba gani ba. ‘Meya faru kuma? Dafa tana fara’a’. Atika ke maganar cikin ranta. Jin ba takun Atikar bayan ta wacce ta shige cikin dunyar tunani yasa Goggon tsayawa ta waigata. “ Atika!”. Ta kira sunanta cikin dan daga murya wanda shiya dawo da ita daga duniyarta na tunani tayi saurin amsawa. “ Mekike jira a nan”. Goggon ta tambaya tana mai tsura ma Atika idanu wacce ta taho tana nuke-nuke kamar wacce aka kama tayi sata. “Atika dakata”. Goggo ta dakatar da ita lokacin data iso kusa da ita. Atika kanta a kasa yayinda Goggo ke cigaba da tsura mata ido tana kallon yanayinta. “ Atika”. Takira sunanta cikin wani yanayi take kallonta. “  Inaso kimun alakwari da Manat cewan ba wanda zaisan inda mukaje, sannan inaso ya zamana ko ‘yan uwanki ma’aikata ne ki sanar musu gun Bauta mukaje kinji”. Ta ida maganar tare da riko hannun Atika wacce jin rikon yasa tayi saurin dago kyawawan idanunta tana kallon Goggon wacce ita ma ke kallonta cikin ido.  Sunjima a haka kallon ne ya soma ma Atika wani iri ganin yadda Goggon ke binta da ido da sauri ta sauke idanunta tare da janye hanunta cikin wani irin firgici.

Murmushi Goggon tayi tare da juyawa. “ Na miki alkawari Gog…”. “kul!”. Tafada tare da juyowa cike da bacin rai. Atika a tsorace ta ja da baya cikin zaro idanu. “ Niba Goggonku bace! Ni Goggon Aaron ce kawai shike da ikon kirana wannan sunan ba kuba. Meyasa kukeson maidani tsohuwa bayan da yarintata sosai duka-dukana nawa nake da kowa zaina kirana wata Goggo harda wadanda suka girmeni?!”. Ida furucinta na karshe cikin daga murya tana kallon Atika wacce tsoro ya gama baibayeta. Ganin yanayin da Atika keciki yasa ta juya  ta kama hanya. Atika ma bin bayanta tayi cikin sanda kamar kifin da aka kamo ruwa. Sunyi tafiya me nisa kafin suka soma shiga cikin mutane wanda a hanyarsu duk wanda yagansu sai gaidata saboda girmanta a wajensu kasancewarta cikin wadanda keda fada a Masarautar uwa uba Sarauniya Goggo ga sarki Aaron kansa.

Boyayyar MasarautaDove le storie prendono vita. Scoprilo ora