Shirin Fahm; Matar Mahaifin Maad.

232 10 0
                                    

                 Asha karatu lafiya....inamai ma Fans addu'ar Allah yabiya mana dukkanin bukatunmu na Alkairi Daya tsare mu da dukkan sharri Ameen🤲 Kuma Inagodiya da soyayyar da kuke nuna mun a Koda yaushe...🙏




🅿️07

Maad tunda ya shiga gidansu bai hadu da kowa tsakar gidan ba. Tabe bakinsa yayi Kai tsaye ya nufi dakinsa yana shiga ya kwabe igiyoyin takalmin kafarsa ya cire gefe tare da ajiyar zuciya. Lumshe idonsa yayi lokacin daya tashi daga sunkuye yana hucin ajiyar zuciya tare da shafo sumar kansa da hannu. Shiru yayi na tsawon lokaci batare daya bud'e idonsa ba.
         Wani matashi na hango zaune da bazai wuce shekaru sha biyar ba 15yrs Kan gadon Maad kafarsa a tankwashe hannunsa rike da nama, haka bakinsa ma duk maiko da alama bakinsa cike yake da nama shima. Idanunsa gaba daya akan Maad suke ba alamun motsi tattare dashi cinyar kazar dake hannun sane ta subuce ta bugi dan kwanon dake gabansa wanda shima nama ne ciki cike makil.

Motsin ne ya dawo da Maad hayyacinsa yayi saurin bud'e idanunsa tare da zaro wukarsa, cikin zafin nama yakai sara kan matashin Wanda idonsa ke zare tun ganin reaction din Maad. Cikin gaggawa yayi wani irin tsalle ya dire kasa daga Kan gadon. Yayin da Maad baiyi nasarar samun saba. Maad na shirin Kai wani saran Matashin ya rungume Maad ta baya tare da shigar da hannayensa duka biyu cikin jikin Maad wajen rungumarsa.
           "Nine nine!". Jin muryarsa yasa Maad dake ko'karin kwacewa ya tsaya cak tare da runtse idanunsa duka lokaci guda cike da takaici. Sun Jima a haka kafin Maad ya ruko hannun Matashin duka da k'arfi yake cire su daga jikinsa. Cikin sa'a kuwa ya samu ya zare su duka. Murmushin Matashin yayi tare da zamewa daga jikin Maad din. "Yaya meyasa baka da sauki koya...". "Meya kawo ka dakina bayan kasan bana so". Maad yayi maganar cikin dakiya me nuna ba wasa a tattare dashi.

"Yaya!". Matashin ya Kira sunan Maad cike da yanayin na shagwaba. Sai a lokacin Maad ya juyo ya fuskance shi, ba fara'a Sam a Kan fuskarsa. "Yaushe kadawo Larza?". Maad yayi tambayar tare da dauke idonsa yana maida wukarsa. Murmushi matashin yayi. "Yaya kayi rashina ko?". Kada Kai Maad yayi cike da takaici ya juya ya zauna Kan gadonsa Wanda sai a lokacin ya kula da kwanon da kekai. Zaro idanu matashin yayi ganin inda idon Maad din yake.
          Cikin sanda ya karasa bakin gadon yana satar kallon Maad wanda yana jinsa anma bai tanka saba. Daukar kwanon yayi yana Murmushin yake tare da hadiyar dataccen miyau. Harya dauka Maad bai tanka mishi ba ya koma gefe kiss da kofar ya tsaya. "Ahm Yaya da...". Shiru Yayi sanadiyar kallon da Maad ya jefa mishi ya sunkui da kansa. " Maalik Maalik!". Muryar mahaifiyarsa ne ya karade gidan. Shiru yayi batare da ya amsa ba yana kallon Maad dake zaune idonsa ke kasa. Wani irin ajiyar zuciya Maad ya furzar tare da dago kyawawan idanunsa akan kaninsa Maalik dake tsaye yana kallonsa.

" Kaje tana Kira". Ya fada tare da nuna ma sa kofa da idanunsa. Batare da ya musa ba ya kama hanya ya fice d'akin cikin sanyin jiki ynayi yana waige. Sai dai Maad baiko kalla inda yake ba harya fice. Maad furzar da wani irin huci yayi tare da ajiyar zuciya, dago kyawawan idanunsa yayi yabi kofar da kallo tare da murmushi yana girgiza kansa.
         Ya koma yana ko'karin kwanciya ya tuna yadda ya tadda Maalik da kwano akai. Tashi yayi da sauri. Inda abunda Maad ya tsana a rayuwarsa bai wuce kazan ta ba, bai koma ya kwanta ba saida ya tabbatar ya gyara komai na d'akin nasa. Kwanciya yayi dauke da murmushi Kan fuskarsa, kaf gidan ba Wanda ke kula dashi yake sonsa cikin 'yan uwana da suke 'yan uba kamar Maalik ya masifar damu dashi sosai shiyasa yake matuk'ar kaunarsa duk da yana dan janyewa saboda mahaifiya shi Maalik bata son Maalik na mu'amula dashi Sam.

Maalik yana fita yaci karo da mahaifiyarsa tana shirin shiga dakin ta. Tabe baki tayi ganin daga inda ya fito. "Uhm". Tayi tare da wurga mishi harara ta watsar dashi ta hanyar kau da kanta ta shige dakinta. Yana ko'karin mata magana ganin kallon data masa ta shige yasa yayi shiru tare da girgiza kansa yabi bayanta zuwa cikin d'akin.
        "Sannu da dawowa Umma". Ya fada lokacin daya shiga d'akin. Bakin gadon ta karasa da sauri tashiga nunke tufafin dake gefe cikin fushi take aikin nata. Ganin yanayin ta yasa yaja bakinsa yayi shiru ya nemi guri ya zauna yana kallonta. " Ba abunda zanyi na kyauta musu a wannan gidan Koda abun kirki ne narasa ya akayi Manat tayi ni cikin irin wannan mutanen!". Cikin fushi take maganganun wanda ko numfashi bata tsayawa taja.

Boyayyar MasarautaWhere stories live. Discover now