Asha karatu lafiya... karku manta ga masu son Logo, flyer's, edition na Graphics zai iya contacting din Mimsqueen Graphics...I am sure mutum zai sama abunda takeso a farashi mesauki👌 just like Wanda kuke Gani a sama ko finsa.
🅿️09Ya jima a haka kafin daga karshe ya sauka a daga kan dokin a hankali. Bin kofar da kallo yake yayinda kirjinsa ke bugawa kamar zai fito waje. Wannan ba shine karo na farko da hakan ke faruwa da Sarki Aaron ba duk lokacin da yazo ganin mahaifiyarsa yana shiga wani irin yanayin na ban tausayi kamar ba Sarki ba. A hankali yake jan kafarsa ya isa bakin Gate din wanda yana tabawa ya wangale gaba daya. Shiru harabar gun ba komai harabar haka babu alamun mutane sam a ciki. Waige-waige ya soma kozai hango mutum sakamakon bugun zuciyarsa dake karuwa kamar zaiyi tsalle ya fito daga kirjinsa. Wasu suntsaye ne sukayo kansa dayawa suna kuka, a storace sarki Aaron yasa hannayensa duka biyu yana tarewa yana korarsu daga hawa jikinsa. Kallo daya zaka mas aka fahimci halin da yake ciki me cike da dumbin tsoro.
Lokaci guda wata iriyar dariya ta karade gurin yayinda tsuntsayen sukai sama suka bace but. Zuru Sarki Aaron yayi yana dubu-dube dan ganin me dariyar. “ Tabbas! nayarda kai din ba komai bane kamar Mahaifinka. Uhm uhum! Wayace Sarki kamarsa zaitaba haifan matsoraci irinka, na tausaya masa da yana raye”. A bayansa ta bayyana tare da shafosa ta baya wanda hakan yasa Sarki Aaron saurin juyawa yayinda ta kara bacewa batare da yaganta ba ta cigaba da dariya. “ Amma a wani fanin kaso gadon Mahaifinka duk da kana boyewa nasani hahah”. Ta kuma furtawa har wannan lokacin Sarki Aaron banda wurga ido da juye juye duk inda yaji muryata tabi ba abunda yake. “ Nasan me kakeji game da Maaaaaaaaaaaaad”. Ta rada mishi a kunne tare da jan sunan.
“ Waye! Kibayyana gareni!!”. Sarki Aaron yafada a fusace wannan karon cikin kokarin nuna jaarumta duk da tsoro ya gama cika shi a yanzu da jin furucin abunda yafi komai tsana a rayuwarsa. “ Nace waye? Kibayyana!”. Ya kuma fada cikin daga murya lokaci guda dariyar ta dauke gun yayi shiru dif kamar ba wata halitta agun. Jin motsin bude kofa yayi, da sauri idanunsa yabi inda yaji karar. Wata budurwace tafito cikin kayansu na bayi dauke da bucket hannunta da alama kayane hannunta. Ganin wanda ke gabanta yasa tayi saurin durkusawa gabansa jikinta na rawa ta soma gaisheshi. Ganin yanayinta da kayan jikinsa ya kwantar ma Sarki Aaron hankali duk da haryanzu bai daina jin abunda yake jiba. “ haka kuke barin gurin nan shiru ina sauran ma’aikatan?”. Yayi tambayar tare da kau da kansa. “ suna gun cin abinci”. Ta furta cikin hanzari. Alamu ya mata da tana iya tafiya yayinda shikuma bayan ta wuce ya lumshe idanunsa yana maida numfarfashi kan abunda yafaru. Ya jima a haka kafin ya nufi ciki dan ganin Mahaifiyar tasa.
Kofofine ba daya ba cikin katon falon wanda ke cike da fitilu haske kota ina. Wani daki naga ya kurama idanu ba kyaftawa ko kadan. Ya jima tsaye agun kafin naga ya shiga cikin daya daga cikin dakunan. Ban bishi ciki ba inatsaye a falon naga yafito cikin kayan bayi a maimakon kayansa na sarauta kamar yadda yake Sarki. Dakin daya kura ma ido ya nufa kai tsaye tun daga bakin kofa yake jin sheshekan kukanta. Shiru yayi batare da ya karasa shiga cikiba yayinda wasu hawaye masu zafi kebin kuncinsa. Lokaci guda sheshekar kukan ya dauke yayinda dariya yam aye gurbin kukan. “ Dana Aaron, Aaron!”. Jin ta kira sunansa yasa Sarki Aaron goge hawayensa da sauri ya tura kofa yasa kai. “ ga…”. Bai iya karasawa ba saboda kullin kayan dake hannunta wanda take wasa dashi tana jijjigawa da alama shi take kira da Aaron din. Ganin Sarki Aaron yasa ta saurin boye kullin kayan dake hannunta tare da turo lebukanta tana kallonsa. “ Bazan baka Aaron din aba, kazoo sace mun yarona, ba wanda zai taba mun Aaron dina”. Tafada tana kara boye kullin a bayanta tana kallon Sarki Aaron wanda idonsa ke cike taf da hawaye. A hankali ya soma matsawa inda take yayinda tayi saurin tashi ta sauya guri. “ Bazan taba miki Aaron dinky ba, bazan taba miki shiba na miki alkawari”. A maraice yake mata maganar. Abun tausayi dukansu abun sai wanda yagani. Duk yadda yaso matsawa kusa da ita abun yaci tura dan sam bata yarda da kowa kusa da ita inba kullin nan da take gani matsayin jaririnta ba.
Ya jima a dakin daga bisani ya fito idonsa cike da hawaye sosai yake kuka kamar ba Basarake ba. Yana fitowa yaci karo da Maad wanda yabiyo bayansa. Cikin wani irin radadi na damuwa ya rungume Maad yayinda Maad idanunsa ke cike da tsantsan tausayi. “ Sarki ma mutum ne Aaron kayi kuka bamai shigowa nan”. Yafada yana mai kara rarrashinsa shikansa a wannan lokacin hawaye sunfara sauka masa tuna Mahaifiyarsa. Sosai Sarki Aaron ya sake jiki cikin jikin Maad yasha kukansa mai isarsa. Kamar daga sama zancen wannan matar dayaji kan ya shigo kan shida Maad ya soma dawo masa, da sauri ya ture Maad yaja gefe tare da kauda kansa yana share hawayensa. “ Meya kawo ka nan?”. Ya tambaya cikin dakiya. Baiyi mamaki ba Maad share hawayensa shima yayi. “ Dama nayi tunanin ko kana bukatar wani kusane”. Maad ya bashi amsa. “ Nagode muje”. Sarki Aaron yayi maganar cikin sauri batare daya kalla Maad bay a juya ya wuce daya dakin da kayansa suke. Maad na tsaye najiransa ya shiga ya sauyo yafito. Tsayawa yayi bakin kofar yana kallon Maad wanda shima shi yake kallo kafin ya juya yayi waje Maad yabi bayansa sai dai basuyi magana ba kowa yahau dokinsa suka nufi fada.
Suna isa bayi sukayo gunsu dan taimaka ma Sarkinsu. Maad yanayin sarkin ke bashi mamaki cike da tausayi. Suna shirin shiga cikin fada Aaron ya juyo ya kalla Maad dake biye dashi a baya. Dakatawa sukai suna kallonsa. “ Kaje gida, yanzu bazan iya tattauna komai ba”. Maad godiya yayi ya juya kamar yadda Sarki Aaron ya bukata kowa ya kama gabansa. Yana shiga ciki tun kan ya karasa kukan Azar ya karade kunnuwansa dan haka bai nufi sashinsa ba duk da yana bukatar kadaici ya nufi sashin bayi inda ake rainonta yake jin kukan. Ganinsa yasa duka suka zube wajen gaida shi. Sama sama ya masa musu yayinda ya karbi Azar bai tsaya gun ba kai tsaye ya wuce dakinsa da ita yayinda tayi tsit a hannunsa kamar jira take ya dauketa. Kallon juna bayin sukai. “ Kai, kunga ‘ya yana daukarta tayi shiru”. daya daga cikin bayin tafada. “ nima wannan abun ya bani mamaki yadda tayi shiru kamar ba ita keta fitinar mu ba”. Fitowar Goggon Sarki Aaron yasa dukansu sukai shiru. “ Me kuke tattaunawa? Ina yarinyar?”. Tayi tamabayr tana kallon bayin wadanda tunda tafito sukai kasa da kawukansu. Nan suka shaida mata abunda yafaru murmushi tayi ta wuce abunta hartakai kofa ta juya ta kallesu. “ Atika muje ko!”. Cike da murmushi baiwar da aka kira atika ta juya tabi bayan uwargijiyar tata da alama fita zasuyi.
Tuni Sarkin Aaron ya manta da damuwarsa yana wasa da yar Jaririyar sosai kamar wani dan karamin yaro. Dalia ce ta bayyana d'akin, sai dai Sam baisan da bayyanar taba kusan wannan karon ne farko data bayyana agu batare da yaji koya San da zuwan nata ba. Duk da abun ya bata mata Rai sosai yadda harta daga hannu zata kaima jaririyar hari, Amma ganin yanayin Sarkin nata da yadda yake murmushi yasa ta maida hanunta da sauri, haka kawai ta tsinci kanta da kallon yadda yake wasa Azar. Abubuwa da dama ne ke zuwa ranta dan gane da hakan.
Sun Jima a haka. Haka kawai jikinsa ke basa ana kallonsa, a hankali ya waiga yaganta tsaye, murmushi yayi ya tashi tsaye da sauri ya nufeta. " Kinga ta soma dariya ko?". Ya fada lokacin daya karasa gabanta Wanda sai a lokacin Dalia ta dawo daga duniyar data shiga. Dakyar ta kakalo murmushi ta da'ura kan fuskarta sai dai tana kallon Azar taga wani irin haske. Zaro ido Dalia tayi da sauri. Ganin yadda take kallon jaririyar yasa sarkin Aaron kallonta cike da mamaki . "Lafiya meye faru?". A zabure take kallonsa. " Kalla idonta ka...". Abunda yake gani idon ne ya dauke Wanda ita kadai ke iya gani dama.
Dan tsaki Sarki Aaron yayi tare da dan jijjiga Azar dake shirin bare musu baki da kuka. "Mekika gani? Nibanga komai ba Masoyiyarka". Ya bata amsa shiru Dalia tayi a dan tsorace taja da baya tana kada Kai, saboda Wani irin abu me zafi dake ziyartar ta. Cikin gaggawa ta bace yabar Sarki Aaron na kiranta. Maida dubansa yayi Kan Azar tare da dan tabe bakinsa. "Kinganta ko?". Ya tambaya yana kara tsura mata idanu. " Haka take tazo wuf ta tafi Duk sanda taso". Yaba kansa amsa yana murmushi ya koma ya zauna. Kalmarsa na wuf yasa ya tuna abunda ya Gani sanda yaje gun Sarauniya Awatif Mahaifiyarsa. Girgiza Kai yayi saboda Dalia yake nema ta hasko mishi Kan wacce yagani ya manta shaf.
Sai Munhadu a next Page Wanda ke Nan Tafe bada jimawa ba thanks 🙏
YOU ARE READING
Boyayyar Masarauta
General FictionHidden kingdom wato Boyayyar Masarauta labarine me cike da abubuwan ban mamaki...inda Azar zata fuskanci kalubale da dama. Azar yar Sarki Nazdal ce daya haifa tare da daya daga cikin matan da aka zaba dan zama