Chapter1

553 11 0
                                    

ADAMAWA YOLA
Yau kide kiden da akeyi agidan yayi yawa, busa akeyi sosai a government house din ADAMAWA state
Her Excellency First Lady of Adamawa State Hajiya Merama Hilda Ali Ammadu Taci Ado sosai irin na matan gawmnoni tana saukowa daga steps din side dinta dake cikin government house mata sun take mata baya suna mata shewa suna tayata murna sannan ga securities suna tareta ana boyeta ko kuda basu son ya taba ta Amaryar His excellency Alh Ali Ammadu kenan Governor din Adamawa state kuma Jikan Sarki muhammadu Jibril 11 of Yola state kenan currently the prince of YOLA state former Ambassador of Nigeria to America also for minister of FCT

Tun Ranar Wednesday agarin YOLA ba natsuwa suna bikin 5th Daughter din First family of YOLA state she's getting married to the first son of the current FCT Minister. Zayyad Mustafa Bankudi

Kinga Lily(Maryam) ki tashi ki daina wannan kukan saboda Uwar gidan sarki tana Falon her excellency ke take jira zata rakaki wurin his excellency zakuyi sallama zamu wuce airport saboda dangin ango sun zo daukan amaryansu cewa Anty Mimi (sister to her excellency Hilda) lily ta miki tana gyara bangles dinta na real Dubai gold sannan Asma Harun ta dauko alkyabba direct from gidan sarki ta daura wa lily(Maryam) Amarya akanta lily kuma tana ta kuka idonta har ya kumbura saboda kuka nan take ta fito yanmata suka take mata baya suna mata wakar 'ke kikace kinaso da bakice kinaso ba da ba'a baki shi ba'
A falon His excellency kuma ta fashe da kuka ya fada jikin daddy tana I don't want to go daddy tana ta kuka ya bata 3mins kafin yace Dr Maryam sannan tayi shuru dukka falon kowa yayi shuru shi kadai ake saurare sai kuma sheshekar kukan lily 'I'm a Proud Father, i'm so blessed to have you as a daughter I'm so happy for you that yau kin gama da iyayenki lafiya kin dau hanyar completing half of your deen, on your way to start a new journey Ina miki fatan alkhairi ina miki addu'an sauka lafiya, zama lafiya da kuma gamawa lafiya(Ameen) yayi ma kanuwarshi hannu wato uwargidan mai martaba sarkin YOLA hannu alamar su zo su wuce da ita Hajja Sa'ade tayi taku daya biyu uku ta duka ta dago maryam dake jikin mahaifinta tana rubzar kuka sosai (wannan rana tana nan zuwa ga kowace 'ya mace) sun fito a harabar gidan gamnati dake garin yola mata na shewa masu kida da busa sunayi sannan ga tawagar motoci bakake wuluk sunyi jerin gwano suna jiran su hau titi zuwa airport inda private jet har biyu suke jiran isowar Amarya(lily) Maryam

FCT
Nnamdi azikwe airport inda comboy na gani na fada ke jiran isowar Amarya Maryam lily da tawaggar ta, daga nan suka dauke maryam da mutanen ta sai Asokoro gidan FCT Minister Mustafa Bankudi, securities kam kamar agidan ake musu training ga SS Ga mopols ga sojoji duk kewaye da gidan, duk girman gidan nan mace daya ce sai 'ya 'yan sa uku Zayyad da usman sai amira yar auta, Haj safiyya ita ce ta kafa ta tsare no entry kuma no outing gata a tsakiyar yan uwanta suna ta bude akwatuna suna rufewa bayan lefe kuma ga kayan budan kai za'ayi dasu ga gwala gwalai ga diamond da rubbies Ma Sha Allah
Tsayuwar motocin kenan sai ga mata sun fito sun Tarbe matan da suka kawo Amarya direct suka wuce da ita side din Honorable Minister mata nata guda ana busan sarakuna fuskokinsu cike da annashuwa

Daga Chan sama side din Ango Zayyad, dakinshi cike da Abokanen ango sai tsiya ake mishi, fahad Mahe commissioner yana fadin ku tashi mu tafi gasu Chan sun iso, ibrahim yaron ex governor na Skt yace fahad ka cika rawan jiki ka bari sai an kiramu saboda mu yanzu ake son gani da ji, Zayyad yace haka dai kace yana murmushi ya kuma fadin ni wlhy am worried saboda tun jiya banyi waya da lily ba kuma asmau harun tace she has been crying that's why I'm so upset yayi shuru suka dau ihu suna fadin angon maryam bankudi yau daga kai sai ita babu mai rabawa Idan kayi lallashi Kuma shikenan mansur ya amsa da cewan gsky I cant wait to get married fahad yace badai wannan sokuwar gidan Minister na Skt zaka aura ba mai goshin nan Zayyad ya fashe da dariya yana fadin Ibrahim zaka iya tuna auren Suleiman AY da muka biya gidansu yarinyar mansur tana fitowa tana yanga tana laudi nan take fahad ya fara fadin mansur badai yarinyar nan mai kai kamar jirgi zaka aura ba gaba dayansu suka fashe da dariya suna kyakyatawa announcement dinda akeyi acikin gidan chan Garden dinda akayi decoration na budan kai ana kira ango da abokansa su sauko su zo su bude amarya
Nan take suka fara ma ango tsiya ya dauki babbar rigarshi ya saka sannan ya fito balcony dinshi ya fara saukowa steps din nan take suka Mara mishi baya suna fadin ango merama mai farin barka da kuma farin yadi suna ihu suna kara suga shi haka ya sauko sai hanyar garden security's suka taso suka Mara mishi baya wasu agaba wasu abaya daga nesa zaka hango maryam Lily Ali Ammadu bankudi azaune akan kujerar da aka tanada saboda amarya da ango cikin shigar alfarma kanta akasa kuma arufe saboda alkyebbar data saka, agefenta kowa kyautar akwatina ne kiran LV setin uku kowane set mai hudu that makes them sha biyu laces dinda ke ciki kuwa sunfi karfin 100k zuwa sama gaba daya atamfofi kuma duk kirar super was ne vlisco sai takalmi jimmy chop, Versace, da Gucci har da su Prada abu na masu shi kam
Isowar anko keda wuya ya bude Amaryar sa yayi mata ruwan kudi sai da fahad ya rikeshi ya Dago makullin mota kirar Benz ta mata saloon ya damka mata nan take zance ya chanza daga nan kuwa suka wuce gefen Justis Haj Safiyya Mustafa Bankudi aka kebeta awani daki sai da tayi sallah sannan ta zauna aka kawo wannan aka kawo wancan amma duk ta kasa cin komai kafin aka fara makeup na zuwa English dinner inda suka gyara mata gashi ga white wedding dress kamar disney princess kai Ma sha Allah daga ballroomabuja ango ya saka Amaryarsa a mota suka wuce abunsu yan dinner kuwa sai ihu suke suna karawa barin ma friends din ango da suke fadin sai Kayi Zy sai kayi zy

A adamawa fa
Mutane sun watse sun bar government house daga security's sai ma aikata saboda gidan ba ma'abocin hayaniya bane yawancin yan uwa da suka zo daga nesa duk yan borno ne kuma tun da yamma sun wuce sai yan uwan governor yan adamawa kowa ya koma gidanshi manyan mutane kuma sun koma masauki bi ma'ana na hotel sun koma hotel gobe zasu wuce haka kuma manyan governors da matansu suna government lounge
By 11 na dare wuri duk yayi shuru kamar ba 8hours back ba kamar ba'a gidan akayi biki ba

Alh Ali Ammadu
Waye wannan mai tarin mulki da sarauta?
Ku biyo ni kusha labari
Ali Ammadu 'da ne wurin ammadu wazirin sarki Muhammad jibril na biyu
A lokacin jibril lokaci ne wanda gaskiya tafi yawa kuma ya tara mata da 'ya'ya amma Allah bai bashi 'da namiji ba sai alokacin da yayi wata tafiya zuwa egypt yayo aure ya dawo da matar nan gida Nigeria bayan ya dawo ne ya fara jinya ashe tafi yar kenan ita kuma amaryar tasa mai sona Diza ashe ta kamo bayan tafiyarsa ta wata bakwai Allah ya bata 'da namiji wanda yaci sunan Ammadu
Saboda tsabar kiyayya da hassadar da kishiyoyin nata suka nuna mata shiyasa wata rana aka waye gari aka ga babu ta ya gudu ita da 'danta ammadu jinin sarki guda anyi ta nemanta har kasar tasu amma shuru bayan shekarar sarki jibril daya da rasuwa ne aka nada kaninsa wato Tijjani, Bayan shekara ashirin da biyar Ammadu ya dawo masarautar ubansa amma bai zo da niyyar karbar sarautar ba, bayan ya dawo ya samu cousin dinsa wato jibril(wanda yaci sunan tsohon sarki wanda Allah yayi ma rasuwa wato mahaifin Ammadu) takwaran sarki jibril. Had uwar jininsu yafi komai yima iyayen nasu dadi, sau da dama sarki tijjani yana kiran Ammadu fada yayi mishi tambayoyi akan kujerar da is his birth right amma da mamakin sarki tijjani sai dai ammadu yace ai shi baya ra'ayin sarauta ya ban ma 'Dan uwanshi Abba (wato jibril) haka suka tara mata da 'ya'ya har lokacin tafiyar sarki tijjani yayi (Allah yayi masa rasuwa bayan yayi shekara 61 akan kujerar sarauta) kishin kishin dinda ammadu yaji anayi na shi za'a nada ai kujerar tashi ce sai yaga kuma kan yan uwa na kokarin rabuwa gashi kuma Abba ya dauki son sarautar nan ya saka aranshi ne cikin dare ya tattara matarshi daya da 'ya 'yanshi biyar suka keta hazo sai saudiyya nan take wasu fada wa suka samu bakin magana akan lallai baza su zauna zaman jiran sarkin da ya gaji guduwa tun daga uwa ba haka dai aka nada sarki muhammadu jibril tijjani wanda har yanzu shine akan karagar mulki

Bayan shekaru goma sha takwas kwatsam sai ga Ammadu ya dawo da iyali mata biyu har da 'ya 'ya takwas nan take 'Dan uwansa yasa aka gyare mishi gefen waziri na da aka fitar mishi da bangare babba ya zauna dashi da iyalinshi sai dai abun mamaki wai Ammadu ya auro balarabiya har da 'ya'ya biyu mace da namiji ita kuma matar da ya tafi da ita yar nan cikin fada ce ya aura yar wani bawa ce da aka yenta ita ce keda 'ya 'ya shida maza biyu mata hudu
Bayan ya huta sarki ya samu kebewa dashi shine sarki keson yaji karin bayani akan wai mey ya saka shi guduwa a wancan lokacin Ammadu ya nuna mishi shi bashida ra'ayin zama akan wannan kujerar saboda shi yanason Idan ya gaji da zama Anan ya kara gaba sarki yayi dariya yana fadin toh mu dai kar atafi Chan China a auro muna le min ho suka kwashe da dariya, da kyar dai Ammadu ya yarda aka nada shi wazirin YOLA
Har alokacin matansa biyu, Fatima da amarya Hidaya. Fatima keda maryam, Suwaiba, sadiya muhammad, shafaatu sai ibrahima ita kuma yar mutan saudiyya kuma keda marliya sai Alee take kiranshi amma mutanen cikin gidan fada suke kiranshi Ali
Akwana a tashi duk 'ya 'yan fatima mata sunyi aure sai 'dan gidan sarki Ahmed(wanda akayi ma Ammadu takwara dashi) 'Dan uwargidan Sarki wato Hajja Sa'ade (mai babban daki) wadda suka hada uba da Ammadu (auren zumunta akayi musu bayan tafiyar mahaifiyar ammadu dashi) Ahmed din ya makale zai auri marliya ai kuwa cikin dan kankanin lokaci akayi shi kuma alee alokacin yana BUK yana karatun business kafin ya fara aiki a Nan wani kamfani dake kawo kaya daga China direct suna taya mai kamfanin sayar wa daga nan ya samu jari ya Ware kasuwancin sa babu abunda ya taimaka mishi kamar hanyar daya samu na zuwa China ya dawo gida YOLA ya sanar da babanshi, Ammadu ya ware wasu makudan kudi ya baiwa alee, ahankali har ya bude shagunan anan kano da kaduna kaya yake zuwa yana kawowa kamar baisan zafin Kansa ba acikin haka ne kudi suka zauna kusan kaf gidan sarkin YOLA ba wanda ya kai alee yin kasuwanci da samu kwatsam sai ranar Ammadu yayi kiransa yace mishi lallai sallah nan ya dawo gida yayi tare da yan uwansa
Bayan dawowarsa ne ya samu labari auren ibrahim damah acikin 'ya 'yan waziri su biyu ne kawai suka rage basuyi aure ma nan take waziri ya chanza ido yana fadin a ce mutum shekara 32 amma baya zancen aure toh tabbas ya fitar da mata suje su Nemo aure a hada da Ibrahim wanda za'ayi sati uku bayan sallah azumi nan take hankalin alee ya tashi saboda shi yaushe ma ya tsaya soyayya balle maganar aure ta fito, yaje wurin Maamah haka suke kiranta duk da ta tsufa ta Kode zaka gane kyanta ya kuma tsayin gashinta gata kuma fara fat alokaci daya zaka gane ba yar kasar mu bace ba

Laylatu Aman👑Where stories live. Discover now