Chapter 2

178 4 0
                                    

Ta amsa sallamar daga cikin bedroom dinta ta fito tana yi mishi kirarin 'Dan kasuwa kamar wani sarki yayi murmushi yace maamah kenan kullum kina nan da kyau tace rufamun asiri ya zauna gab da kafafunta tana jin dadi idan dan autan ta ya ziyarce ta
Ta kuma dago fuska tana kallonshi tace ya akayi auta yace maamah ban tashi aure ba fa bani ma da budurwa sai tayi dariya tana fadin danAllah duk kyan dan nan nawa tace delu ki duba fa ki gani wai 'dana bashi da budurwa delu ya amsa da cewan kodai baya kulasu ne sai maamah tace ai toh ni nayi mishi mata nan take ya bata rai zai mike tace gwara dai ka cika mun burina kafin in mutu banga jikokina ba yayi shiru kuma ya koma ya zauna Chan yace maamah wadda kikeso in aura tana sona? Maamah ta girgiza kanta alamar eh ta Kuma cewa tabbas tana sonka yace toh ku fara shiri kuma ki gayama Baffa zabinki shine zabina Idan iyayenta sun amince dani su shirya za'a hada dana Ibrahim habah dadi kamar zai kashe ta azaune yana fita ta fara kiran delu ya bata labari tace mata maza ki shiga bangaren Amaryar sarki ki kiramun Azeema tazo maza Ina kiranta
Tafiya takeyi kamar bata son takawa ba daga ganinta yanayin shigar ta da tafiyarta zaka gano jinin sarauta ne saboda shi abun baya boyuwa ai
Azeema ta shigo dakin ami Hidaya  tana fadin ammi nazo sau uku ban samu ganinki ba tace zo nan 'ya ta cewan ami hidaya tace Allah ya amsa addu'a na da taki kedai alee yace ya yarda a hada aurenshi da duk wadda nakeso ya aura tare da bikin ibrahim dadi ya kama azeema dukda tanada kunya dadi yasa ta fada jikin ami Hidaya  tana fadin za'a kai maganar fada ki shirya basu amsa azeema tace toh ba damuwa nagode ya mike tana tafiya har ta bace ma ami Hidaya  daga gani ita dai natsuwar ta ce ka burgeta da azeema shiyasa tun ba yau ba takeda burin ta hada aurensu gashi kuma Allah zai karbi addu'an ta. Mahaifiyar azeema yar sarkin musulmin sokoto ce mai martaba yaje ya auro toh ita Umaima Amaryar sarki da kyar ta samu haihuwar azeema 'yar ta taso cikin gata amma hakan bai bata mata tarbiya ba.
Magana taje kunnen sarki nan take yace toh a samu waziri saboda shine ke bada auren 'ya 'yansu mata shikuma yaje nemar ma 'ya 'yansu maza
Ai kuwa kamar zancen iyayen ke jira
Cikin sati biyu duk sunyi shirye shiryen daya kamata
Duk wannan neman auren da akeyi gogan baya gari saboda yaje kano wasu kayansa sun iso yaje yayi clearing dinsu
Ranar da ya dawo kuwa yan gidan sai barka suke mishi shidai yana ta amsa wa da fara'a duk da bai gane menene ba amma dai yasan zancen auren sa ne kuma bai San waye matar tasa ba wadda maamah ta zaba mishi bayan yayi gaisuwa afada yau dai soyayyar da mai martaba ya nuna mishi daban ce don har da cewa yayi ya matso ya daura kanshi akan kafar mai martaba ya shafa kanshi yayi mishi addu'a yace ya isa ciki yayi godiya ya mike ya shiga ciki
A bangaren Waziri ya tarar da Mama fati tayi list tana yi ma waziri bayani shidai ya gurfana ya Isar da gaisuwa har mama fati sai da ta amsa tana fadin sannu da zuwa Yarima angon gimbiya yayi murmushi yayi mata nata gaisuwar na girma sai ta mike ta basu wuri anan ne waziri ke shaida ma alee zabin da yayi yayi matukar burgeshi kuma ya roki Allah da ya cika mishi burinshi na son kara damkon zumunci shi dai alee binsu yake da murmushi da kuma toh don dai bai gane abunda suke fadi ba amma da alamun maganar mama fati kenan yar sarki zai aura shin sarkin YOLA ko kuma wane sarki wata zuciyar ta bashi amsa da cewan wannan soyayyar da mai martaba ya nuna maka yau ai ya isa ka gane 'yarsa ce zaka aura Waziri ne ya katseshi da tambayar shin wane unguwa yakeson asiya mishi gida saboda ya siyan ma 'Dan uwan nashi har an gama gyara wurin yanzu fenti fenti na mai akeyi
Ni baffa banida zabi ko matar nan da zan aura maamah ce nace ta zaba mun don haka duk wasu shirye shirye da akeyi duk ku zaba sai dai Idan ana bukatar kudi wanda zan iya zanyi cewan alee banda shashancin ka alee ni zaka kallah kace Idan ana bukatar kudi ai auren Ka na farko duk nauyi yana a kaina kuma in Allah ya yarda zam saukeshi gabadaya cewan waziri alee yace inshaAllah zan karasa ciki in ga maamah Ina son in huta yau sosai toh shikenan baffanshi yace bisimillah

Ya mike ya karasa bangaren Ammi Hidaya
Ita damah mai jama'a ce kullum zaka ganta cikin jama'a kowa sonta yake acikin fada saboda ita batada abokin ko abokiyar fada haka kuma 'yar ta da ta kafa ta tsare acikin gidan sarkin YOLA  wanda ke auren 'Dan Sarki na farko wato ahmed(Baffah) da marliya a america suke zama abunsu shi likita ne da 'yar su guda daya Ami(Hidaya) duk da tsegumin mutanen gidan sarki suna fadin cewa bata haihuwa sosai ta biyo uwarta Amaryar waziri ko gayyu ne oho musu kunsan gidan jama'a ba'a rasa gutsiri tsoma
Ya karaso bangaren maamah mai tarin jama'a da fara gashi murmushinta sai ya sanyaya ran ko waye zai zo wurinta fa kamshi na musamman ga gyara ga iya girki yana fatan ace duk ranar da zaiyi aure ya samu kamar maamah dinshi
Ya karasa shiga daga ciki ya Tarar da delu mai aika ciyar Amaryar waziri tun yana karamin yaro duk dawowarsu asalinsu
Kamshin abuncin ne ya hade da kamshin maamah ya amsa gaisuwar delu yace mata Ina maamah gani ango cewan maamah dake fitowa daga kitchen dauke da class tray cike da salad teaser ga wasu maaikatan biye da ita da kayan gani na kallo sosai
Maamah ban taba jin yunwa irin na yau ba haba dai babana Allah maamah wallahi kadaina wannan shagwabar ka kusan angwancewa yayi shuru sabanin da da baki shi baya shuru Indai delu maamah tace delu kawo kunun gyara yau Anan autana zai sha ruwa tareda waziri bayan ya dawo daga sallah magriba ya shigo ta gaba waziri kuma ya karaso ta baya saboda sai da ya fara zuwa bangarenshi anan suka hade suka zauna suna buda baki alee na masifar son girkin mahaifiyarshi saboda ita tasan kan maggi gashi bata wasa da damah ko kaza ko kayan ciki bayan waziri ya koshi yace ta nuna mishi kayan lefe Idan basu mishi ba sai ya karo tunda yanada kudi sai maamah tace haba dai waziri mey yayi zafi haka cewan maamah eh toh 'danki ya nuna mun kudi danki yayi kudi yace wai Idan Ina da matsalar kudi in gayamishi shi bashida ra'ayin maganar don ko gidan zama dana tambayeshi cemun yayi wai in zaba ko matar sa ke kika zaba mishi waziri ya miki ya gyara rawaninsa ya wuce maamah ta juyo ya kalle alee dukda bai ji dadin yadda baffanshi ya dauki abun da zafi ba yasan maamah is a calm person bazata mishi fada ba she will try to understand him babana baka son azeema ne sai gaban shi ya fadi saboda a karo na farko yana jin sunan abokiyar rayuwarshi saboda arayuwarshi ko ranshi ne zai ba maamah bazai ji komai ba
Ya dago kai yana murmushi yace maamah abincin ki yayi dadi wannan veg salad dinnan ki koya ma surukarki ya mike yace maamah karki damu komai kike so zanyi bari inje in dawo cewan alee
Haka akayi bikin aka gama, alee ya koma kano/kaduna bakin aikinshi sannu ahankali ya fada siyasa ana ta tafiya har ya samu manya suka Mara mishi baya saboda Indai farin jini ne da kwarjini ba dai a gun alee ba ba wani saurayi acikin gidan sarki da zai goga dashi wata baiwa ce kyauta daga Allah
Bayan shekara goma sha biyu da aure alokacin yana daya daga cikin manyan siyasa na yola/kano/kaduna amma Allah bai bashi haihuwa ba ga Dan uwanshi da sukayi aure tare 'ya'yansa uku kwatsam ya samu mukami as commissioner of education anan yola dole ya dawo yola bayan shekara hudu gwamnati da chanza sai ya koma birnin tarayya yayi ambassador of Nigeria to America alokacin iyayenshi suka matsa yayi aure saboda har yanzu shuru akwai ranar da ya ziyarci maamah tace mishi alee har yanzu azeema yace maamah ni bana damunta da maganar cikin nan Allah ne bai kawo ba ni bansan ko matsalar daga wurina take ba cewan alee maamah tace alee a asibiti ance maka baka da issue din fertility danAllah ka kara aure yayi murmushi yace zanyi tunda kikayi magana ai na dauka baza ki taba cewa inyi aure ba
Taron da akayi a garin Abuja na ambassador ne ya hango wata kyakkyawar mace mai ilimi nan take yasa yaransa nemo details dinta sai gashi anzo mishi da information dinta wai yar gidan sarkin kano ne nan take ya shiga jirgi sai garin kano yayi ma Hussein waya saboda tare sukayi karatu a BUK kuma dan gidan sarki ne ba Dansa bane amma yana da alaka dashi ya sameshi a guest house dinshi na kano a nasarawa suka ci abinci sukayi sallah har Hussein na tambayarsa yayi masa hanya ya samu wata kwangilar tunda su manya Idan sukayi magana ana ji yayi murmushi yace Hussein kasan Halima Salis ado namarwa? Yace yar sarkin kano kenan? Tabbas ita taya ya zanbi in nema auren ta cewa Amb. Alee Hussein yayi murmushi yace kaji wata wadda maza ke rububi kenan ranka ya dade cewar Hussein ai zaka je ka samu matar senato Habu ali suleiman ita zata shigar da kai cewar Hussein alee yace a'ah har sokoto Hussein yace ranka ya dade yayarta ce ai suna masifar shiri wlhy toh yanzu cewar ambassador alee ta Ina zan fara Hussein yace ka nema senator da kanshi zai zo ya sameka abu na girma ne ai ranka ya dade yace toh shikenan yanzu kayi letter zuwa ga wannan email din kayi proposing kwangilar da kakeso a yadda kakeson ta haka za'ayi maka ita in Sha Allah

Bayan ya koma Garin abuja sai ya nema yaron senator Habu Ali suleiman yace yana son ayi mishi iso zuwa gidan senator dake asokoro nan take kuwa akayi mishi iso bayan sun zauna sun gaisa tunda babu abunda ya taba hada su ba sai ambassador yace ranka ya dade kanuwar matarka na biyo inda hali ayi mun magana da ita a'ah ai ba damuwa yanzu kuwa senator ya aika aka kira mishi ita bayan yayi mata bayani ya bar number dinshi after a week aka kirashi aka shaida mishi ta amince ya tura a chan masarautar kano nan take ya gayama wazirin YOLA suka tada tawaggar sarkin YOLA zuwa gidan mai martaba sarkin kano
Abu na manya cikin karamin lokaci aka saka har aka zo aka daura amarya ta tare agidan ambassador na yola GRA
Abu kamar almara cikin wata biyu ta gano tana da ciki ai kuwa fi'ili iri iri
Ta haife 'yarta mace wadda taci sunan Hidaya(Mami) kamar daga sama sai ga azeema tayi ciki a karo na farko a rayuwarta haba gidan sarki ba wasa amma sai ta haiho yar bata zo da rai ba
Daga lokacin kuwa haihuwa gidan ambassador aka fara sai dai sai da Gimbiya.Halima ta Haifa 'ya ya mata uku kafin gimb azeema ta samu daya alokacin kuwa ambassador ya zama Honourable minister of FCT alokacin ne suka je Garin borno gidan Sarkin maiduguri inda akayi gasar wasar gwalagwalai amma a mamakinsu sai dan YOLA yaro (saboda alokacin baifi 48 ba) nan dai sarkin maiduguri ya kulla zumunta dashi minister saboda su mutanen borno akwai son masu shi sannan gashi yaro yazo da kudi daga nan minister yana ziyarar sarkin maiduguri akai akai har ranar suka hadu a saudiyya da iyalen su anan ne suka gaisa gaba daya har honourable minister mazatakan ya motsa bayan ya hango 'yar mai martaba merama(hilda) kyakkyawa ce ta ban mamaki ga kyanta ya zauna dai dai da jikinta subhanallah kawai honourable ke maimaitawa acikin hirarsu ne mai martaba yake gayama honourable minister ai 'yar tasa hilda law ta karanta tayi masters a law yanzu yana son yayi mata aure amma hankalinta yafi komawa a karatu anan ne yake gayama honourable cewan duk cikin 'ya'yanshi yafi tausaya mata saboda mahaifiyarta ta rasu

Laylatu Aman👑Where stories live. Discover now