Ya shiga shashen Maamah ya tarar da Rahama, Lily(merama) da Azi a falon suna hira da Maamah, maamah taci ado kamar sarauniyar Dubai ya zauna gab da ita yana fadin kinga yadda kikayi kyau kuwa kamar sarauniyar duk duniyar nan tayi murmushi tace kaci tuwo yace yes thank you
Tace Allah ya nunamun kayi aure yayi dariya yace Ameen big bros welcome back cewan azi yawwa azi Lily kam ta dauke fuakanta gefe ita adole fushi take dashi wai bai zo auren ta ba Anty Rahma tace kaga Lily wai fushi takeyi dakai wai baka zo bikinta ba ya dago Kanshi yana fadin Ayyah wlhy nayi niyyar zuwa ki tambaye muhsin har dinkin manyan kaya sai da nasa aka mun sannna ya kalle Muhsin yace wai Ina kayana Muhsin yace ai na saka su abikin yan gidanmu modibbo yace wallahy sai ka biya su Dan renin wayyo su maamah suka kwashe da dariya
Modibbo yace maamah wai meyasa kowa yake fushi dani ne kinga yadda ouum khalid(khadija) ke fushi dani Anty Rahma tace toh saboda meyasa baza tayi fushi dakai ba yace wai nine nafi kowa lefi? Anty Rahma tace eh kuma wallahy ka tabbata aure ka dawo yi ko in baka mamaki yayi murmushi yace mamaki ba? Auren dole zaku mun Muhsin yace ai sai ayi ma sarki auren dole ai bai wuce hukuncin gomnati ba modibbo ya fara dariya yana fadin wato Anty Rahma kune gomnati kenan maamah tace ai ni bansan ma mai zance mishi ba gudunmu fa yakeyi merama tace Anisa fa masifar sonshi takeyi Anty Rahma tace Anisa Namoda? Merama tace tabbas a bikina taso ta ganshi modibbo yace kaji wata shugabar marasa aiki muhsin ya fara dariya yana fadin tayi hakuri saboda irinsu modibbo wadda suka so ce kawai za'a iya zama lafiya dasu modibbo ya daga mishi hannu alamar thumbs up yace amma baza su iya jira ba cewan modibbo Muhsin yace sai yar baka mai bakin gashi modibbo ya cira trow fillow din maamah ya cilla wa Muhsin maamah ta zuba ma modibbo ido ya kara zama namiji babba haba ai 33 ba wasa bane ba ga saje ya kwanta gashi dogo fari tas sosai yanayi mata yanayi da Marigayi maimartaba mahaifinta saboda yanzu sarautar borno ta koma hannu babban yayanta wanda suka hada uba ga gashi ya kwanta akanshi Idan kaga modibbo zaka rasa tsakanin larabawa da Fulani da shuwa wane yare ne shi Idan ya bude baki yayi hausa zaka sha mamaki saboda bashi kamada hausawa
Lily tace toh yaushe zaka zo gidana ya amsa da bari in huta manah ke azi yaushe zakiyi aure cewan modibbo ta amsa da Yaya final year fa nake kuma am just 23 yace toh ni Ina ruwana maza ki fitar da miji daga kofa kuma sa'id yace kai kuma maza ka fitar da mata ko muyi maka auren dole suka kalle kofar gaba daya nan take suka kwashe da dariya ya tako yazo dab da modibbo sai modibbo ya mike tsaye suka gaisa sai sukayi hugging din barin jiki yana fadin lallai kai Dan duniya ne toh modibbo ai nan gama sai munyi yaki da yan morocco don zasu ce kai nasu ne Muhsin yace ko maiduguri ba tunda duk adamawa(mubi) ba wanda ya kaishi fari su maamah suka kuma kwashewa da dariya modibbo ya zauna yana dariyar Muhsin yace ma said wallahy Muhsin ya cika shirme dazu fa cewa yayi tun da kayi aure baka fitowa waje wai ta mallake ka har da cewa ba sabanba Dan kauye yayi amarya Muhsin yace har da sharri? Dadin abun ba tsoron shi nake ba suka kuma dariya Muhsin yace kai modibbo gobe ne fa tafiyar Zaria Daga Chan zamu debi jiki sai garin sokoto yana murmushi modibbo yace wannan shirmen bada ni ba maamah tace aww baza ka bikin Muhsin din ba modibbo ya kalle maamah ya kuma kallar Muhsin har yanzu Muhsin din murmushi yake yana fadin am off the market ya kalle sa'id, sa'id yace ai abokina kai kadai ne ka rage😂 suka kwashe da dariya Modibbo ya daga kafadarsa alamar ko ajikinsa yace maamah I couldn't find my mtn sim so zanje inyi waya dasu ayi mun welcome back ya mike nan take ta mike tace babana ina so inyi magana dakai sai alokacin ya kalle fuskarta sai ya gano damuwa acikin idonta yace toh muje ya shiga gaba ta biyoshi baya kai tsaye ya wuce main bedroom din ta wanda yayi biyun normal master bedroom dinda ake fadi gadon maamah ya cika dakin ga side din falon a dakin and a very large closet suna shiga modibbo ya zauna akan bedside dinta yace maamah gani ta zauna akan gado kusa dashi ta rike hannunshi sai hawaye hankalin modibbo ya tashi ya rasa mey zaice aranshi yana fadin Allah yasa ba Dad bane yayi hurting dinta ba Chan yace maamah dad ne yayi hurting dinki? Tace noo ur dad has always been a father, a sister, a mother, a husband, a best friend & the son I've missed all those years sai yace toh y are you crying? Tace last 3months dana je gida anyi mun fade sai ya bata fuska yace maamah badai maganar tsegumin mata bane yake damunki haba maamah da girman ki da iliminki sai ta dago da kanta daga duken da take cikin zuciyarta tana saka wa nda warwarewa wata zuciyar tace lallashi bazaiyi da wannan 'Dan naki ba bude zakiyi sai kiga ya zama dai dai tace damah damisar takarda ne shi sai tasa hannu ya share hawayen tace kai Dan reini wayyo kace banida ilimi manah kowa ya huta ma sai yayi shuru ta mike tace umarni zan baka Ba shawara ba, ta mike tayi taku uku ta juya mishi baya sannan tace Idan kaje bikin Muhsin ka dawo ka tabbatar da kaje borno kayi gaisuwa agidan sarki, sannan kaje yola kayi gaisuwa agidan sarki da duk wanda ya kamata sannan Idan ka dawo kaje gidan Governor din Sokoto state Alhaji Muhammad sani ka ga Hamida idan tayi maka sai iyaye su shiga maganar, Idan batayi maka ba kaje Gidan DG na port-authority a nan maitama akwai daughter dinshi Dr Zainab ka gwada sa'ar ka ko kuma 'yar sarkin Kano niece din Antynku Halima mey suna zulaihat she's so pretty & well educated I was invited to her call to bar a nan bwari all I could think of was a beautiful wife like her for you ta juyo tace kai akwai mata fa 'ya 'yan manya masu fadi aji, ta kuma fadin masu kyau da ilimi sannan tace daughter din sarkin Borno na yanzu Mai martaba big brother din mu(Yaya auwal) graduated with first class overall from Harvard, imagine such a beautiful damsel zeena she's so well brought up, modibbo ni ko cousin dinka daughter din anty marliya Kakeso please marry her saboda suna ta son ka aure ya or Fulani Hayfa thou she's not done with her studies sa'ar azi ce you can go for her sai ta gama karatu a dakinka, ya matso kusa dashi ta rage murya ta dafa kafadar shi tace my choice is Umma-Salma ya dago kai yana kallonta idonshi sun kada sunyi ja amma maamah ce fa sai ya Nemo murmushi yayi saboda she's the first & last he will never want her to get hurt but yau akwai matsala sai taci gaba da fadin umma salma daughter din minister of finance Honourable Amina walgis wamaiy yarinyar halfcast ce sosai go for her or ur daddy's best friend's daughter yarinyar Prof Ibrahim zam-zam Kamar suna kiraanta ummi nan take modibbo ya mike yace is that why u r crying? Sai ta daga kanta alamar e sai yace toh cikinsu ki zaba mun daya sai asaka rana ayi auren in 2months time alokacin ya duba wayarsa yace don bazan wuce hakan akasar nan ba sai tayi murmushi alokacin da ya kara fadin kinsan zan iya sadaukar da farin cikina saboda naki indai zakiyi murmushi har karshen rayuwarki I won't mind to cry every night b4 I fall asleep don't worry about my problems I don't need to solve them I can runaway from them, yayi shuru Chan sai yace I always do right from beginning & no1 ever cares mayb I won't even get a wife that would love & care for me as don armor dana saka or name or fame or....
maamah Good night ku fara shirye shirye sai ya fita ya sauka ya staircases din baya ya wuce parlour dinshi na side dinshi
His excellency yayi Sallama ya shigo ya zauna a inda yaronsa ya tashi sai yace Hilda karkiyi babban kuskuren da zakiyi babban dana sani sannan kuma ace duk gatan modibbo wai sai ayi masa auren dole toh wlhy bazaiyu ba kibi ahankali ya mike ya fara tafiya sai tace Haba Honourable wlhy idan muka kyale modibbo bazai yi aure ba yayi tsaye chak ba tare da ya waiwayo ba yace in ji wa? Sai ta tako tazo ta tsaya bayanshi tace akwai lokacin dana je neman addu'a akan modibbo saboda ya guje iyayenshi da tushen shi sai ya juyo yana fuskantarta yana kallon kwayar idonta da ya rine da hawaye, yace uhm Ina jinki shamuwa yar kuka🥺 tace aka ce mun bazaiyi aure ba sai na matsa sannan kuma matarshi ba yar wani babba bane akasar nan ba sai hawayen da take rikewa ya zubo sannan tace inaga zata mallake sai yayi murmushi ya jawota ajikinshi yace tun kafin inyi auren farko akace mun zan auri balarabiya amma akasar Nigeria zata mallake ni kuma gashi yanzu kin malake ni duk matana da yan uwa na sun sani kuma ya zasuyi? Sai ta kara fashewa da kuka tace wlhy I'm worried tsoro nakeji bansan inda zaije ya dauko wata ba ya kara yin murmushi yace yanzu zan wuce ana jirana ki tayani da addu'a ya juya ya wuce ita kuma ta koma ta zauna akan gadonta
Fitar da yayi ce yace ma rahama taje wurin maamah ta tana nemanki ya wuce a waje harabar gidanshi tawagar jama'a na jiranshi har da modibbo da yayi ma mahaifin nashi rakiya tare da Muhsin da sa'id comboy ta dau jiniya ta wuce sai suka wuce side dinsu sa'id da Muhsin Sunata Hirar yadda abun zai kasance modibbo bai ce komai ba duk da abokanan nasa sun San ba mai yawan surutu bane ba amma sun gano akwai damuwa a tare dashi
Bayan wucewar dadyn su Anty Rahma tayi sallama a dakin maamah sai ta tarar da maamah ta rike kanta da hannunta tana shakar hawaye Rahma tayi sauri taje ta zauna kusa da maamah ta daura hannunta akan kafadar maamah tace what's happening maamah ta dago Kanta tace I'm scared for modibbo ina jin tsoron kada yaje ya dauko yar talakawa matsiyaciya Tazo ta tarwatsa family dina Anty Rahma tace yace miki yana da wata ne tace no abunda Baba Mallam ya gayamuna some months back nayi mishi magana akan ya zaba mata yace wai in zaba mishi idan dai hakan zai sani farin ciki shi he won't mind ko da zai mutu da bakin ciki arayuwarsa anty rahama ta bude ido tace babbar magana, toh maamah baba mallam ya gayamiki fa ba makawa auren yar matsiyatan nan saboda akwai rabo ya dai ce zamu iya matsala mu bashi wata amma baza mu hana wannan auren ba maamah tace daddynku yace kada inyi kuskuren takura ma dansa wai bazan ji dadi ba nidai yanzu zan cigaba da addu'ar alkhairi zuwa gareshi In sha AllahYa kamata ace muje muga gyaran da sukayi ma gidan chan na jabi fa, sa'id yace aw ka gama ruwan idon kenan Muhsin yace ai bana son atakura mun ne da matata wlhy akwai dan jayawa from asokoro kuma dai bana son inji Karan hayaniya sa'id yace kaje wani Dan iska suka kwashe da dariya amma banda modibbo bai ma san abunda suke fadi ba Muhsin ya girgiza kafadar modibbo yayi firgigit kamar mai tunani sa'id yace a'ah Ahmed lafiya kuwa ya dago idonsa suka hada ido da sa'id, sai sa'id yace sarki ba lafiya kenan yace mey ka gani? Inji Modibbo kai Dan duniya idonka ya kada yayi jajir kamar shine zaka cemun mey na gani modibbo yayi murmushi azahirin gaskiya suna shiri sosai da Muhsin hasalima muhsin yana masifar sonshi amma jininsu yafi haduwa da sa'id, ko Maganar aure ne sa'id ya jefo masa tambayar daga sama sai modibbo ya daga kanshi sama alamar eh, sai sukayi shuru Chan sai Muhsin yace toh kayi auren manah mey kake jira daga sama modibbo yace kanuwar babarka suka kwashe da dariya sai Muhsin yace ka bari zan baka mata daughter din yayata ce modibbo yace bana so nagode sa'id yace haka kawai kace zaka bashi mata yace eh ai irinsu ce modibbo har ya mike ya juyo yace kamar ya? Muhsin yace she's beautiful ne naban mamaki wlhy amma akwai natsuwa yarinyar mahaifinta 'Dan Qatar ne wlhy modibbo yace ja jiki ka bani wuri kawai sai ya wuce cikin bedroom dinshi ya dauko traveling bag yazo ya daura akan center table din parlour dinshi ya fara fitar da designer shirts ya wurga ma Muhsin kamar guda shida yace kayi angwanci ya gyara zaman shi daga kwancen da yake yace ah lallai bari mu gani ya fara warwaresu sa'id yace toh zaka karbi maganar yarinyar ne sai modibbo ya tsaya chak da duba kayanshi da yakeyi yace sa'id kenan sai kuma ya zauna yace I have someone in mind already amma nasan bazaiyu yanzu in kawo musu ita as wife ba let's say later on zasu saurareni said ya bude ido yace badai bakar America ba modibbo ya dauko laptop din apple ya bude sai ga picture din anita gilford akan screen din shi fuskarta mai shegen kyau ya juya mishi kan laptop din yace kalle ta sai da said yayi ajiyar zuciya yace gaskiya she's pretty sai Muhsin yace amma Laila ta fita kyau sosai wlhy ga diri dan Bala'in Chan ga iya tafiya kai madallah sai said yace toh sai muje mu ganta...
YOU ARE READING
Laylatu Aman👑
RomanceDestiny!!! Can never be denied it can only be delayed for some mysterious reasons