Chapter 41

1.2K 198 87
                                    

"Your Grave Is Your Next Room Remember Death Always"

♤♤♤♤♤♤

ZABI NA

Two Month later!!

It's exactly 2 month da rasuwar Habib...

A ranar da Haleema ta sanar da Layla rasuwar kuwa hankalinta yayi masifar tashi..

Babu shakka Habib ya lalata mata rayuwa, babu shakka duk duniya yana cikin wadanda ta tsana, tabbas ta yanke duk wata alaqa da take tsakanin su amma hakan bai hana ta ji mutuwar shi ba.. ko babu komai akwai tausayi na musulinci..

Hatta Mama ta ji mutuwar Habib domin kuwa ko babu komai sun ci dukiyar shi dukda barayi sun raba su da 70% of it.

Abinda ya fi bada mamaki kuwa shine har yau babu wanda ya san ainihin ciwon da ya kashe shi.. Duk nacin Haleema na son sani a wurin Yusuf ta kasa... Ya gwada mata shima bai sani ba amma ga dukkanin alamu ya sani, abinda ya daure mata kai shine yadda baya so ya fadi..

Shi kanshi Yusuf din yayi sanyi sossai tun bayan rasuwar abokin nashi... abin mamaki iskancin da suka saba yi da Haleema ma ya janye gaba daya.. Dayake yana bala'in son Haleema bai rabu da ita ba amma dai a kullum zancen shi bai wuce na maganar auren su ba... ita kuwa Haleema ba shirin auren tayi ba don haka kullum tana cikin yawo mishi da hankali..

Layla dai tuni ta fara soyayya da Sufyan..

Sufyan Abubkar Bicci dai Asalin shi mutumin Kano ne kamar yadda na fadi muku. Babban likita ne a Giwa Hospital da ke cikin garin Kaduna.. Yanzu haka shekarun shi talatin da uku a duniya.. Sufyan dai ya taba yin aure amma Allah yayi ma matar rasuwa wurin haihuwa.. Allah ya dauki ranta da abinda ke cikin ta. Shekaru biyu kenan da matar shi ta rasu, Tsawon shekaru biyun nan bai samu macen da zata cike mishi gurbin ta ba sai wata biyu da suka wuce da ya hadu da Layla..

Layla dai ta shiga ran Sufyan sossai... ita kanta ta tabbatar yana sonta tsakani da Allah. Tun tana noqewa har ta saki jiki suka fara soyayya.. Soyayya mai tsabta ba irin wadda tayi da Habib ba a baya. Ya ba Layla labarin rayuwar shi A-Z, bai boye mata komai ba a game da shi domin kuwa da gaske yake yi ba wasa ba... A bangaren ta kuwa ba komai ta fadi mishi ba domin kuwa tana gudun kar abinda suka fara ginawa ya wargaje..

Toh amma tambaya anan ita ce.. is it the right thing to do???🤔

Sufyan dai yana da arzikin shi daidai gwargwado.. Haka yana kyautata ma Layla sossai. Katin waya, Kayan ciye-ciye, kayan sawa da sauran su babu laifi yana bata.

A yanzu haka jira kawai yake yi Abba ya dawo don ya gabatar da kanshi.. as it is, baya so a dauki lokaci mai tsawo wurin maganar auren su domin kuwa he is all set...

Mama dai ta san Sufyan yana zuwa, Ya shiga har gida ya gaishe ta ma.. Ita kam har ga Allah bai yi mata ba don kuwa ta kula ba mai tarin arziki bane kamar Habib balle kuma Zayd.. ita har yanzu tana akan bakan ta na lallai 'yar ta mai kudi zata aura. Har zaunar da Layla tayi ta umurce ta akan ta cigaba da neman mijin aure mai arziki amma ba Sufyan ba.. Ita dai Layla amsa ta kawai tayi. Tuni ta riga ta dawo daga rakiyar Mama.. Tayi alqawari bazata qara bari ta bata mata rayuwa ba kamar yadda tayi a baya.. A yanzu kam jira kawai take yi Abba ya dawo a fara maganar auren su ta bar gidan ma ta huta.

Wannan Kenan!!

♤♤♤♤♤♤♤

Weeks later!!

ZAYD AHMAD FADOUL'S RESIDENCE
UNGUWAN RIMI GRA

Zaune take a kan kujerar falon shi yayinda yake kwance a kan cinyar ta. Kallon TV suke yi suna hira.. suna yi tana wasa da gashin kanshi wanda ta san yana jin dadin hakan sossai.

ZABI NA | ✔Where stories live. Discover now