Chapter 17

1.1K 205 69
                                    

“Sell this life for the next and you win both of them. Sell the next life for this and you lose both of them.”
~~~Hasan al-Basri~~~

♤♤♤♤♤♤♤

ZABI NA✍

Tun daga wannan ranar kuwa Ameera bata qara ganin Zayd ba.. bata qara jin labarin shi ba. Ta sa damuwa sossai a ranta don kuwa lokutta da dama takan zauna tayi ta kuka.. ta rasa wane irin so take yi ma Zayd.. takan yi tunanin anya akwai soyayya mai qarfin nata a duniya kuwa??? soyayyar ma wadda ita kadai take yin ta..

Qawarta Zarah ta tausaya mata matuqa akan halin da ta shiga.. kamar dai yadda Umma tayi mata nasiha akan mayar da hankali kan karatu ita ma Zarah hakan tayi.. musamman ganin jarabawar su ta matso.

Da taimakon Allah Ameera ta samu natsuwa tayi facing upcoming examz dinta.

Har a wannan lokacin dai Layla bata zama class.. kullum tana maqale da Habib.. Gaba daya jikinta ya saki don tana gurzuwa a hannun shi.. ya lashe ta tas, tun abinda suke yi yana yi mata dadi har ta daina jin dadi. Gaba daya ta daina sha'awa kawai dai tana yi ne don ta samu kudi daga hannun shi. Shi kanshi Habib din ta zo ta kula ya rage rawan jiki a kanta..

Ko da ta yi ma Haleema maganan abinda yake faruwa sai ta hada ta da wata mai sayar da kayan mata wadda ake kira 'Lami gyara su tsab' Lami dai kayan mata take sayarwa masu tsada wanda kuwa idan kika yi amfani da su tabbas zaki san baki kashe kudin ki a banza ba don kuwa biyan buqata 100%.

Aikuwa dai dayake harka ce ta kudi kuma Layla ta sakar ma Lami su nan da nan ta hada ta da magunguna kala-kala ita kuma ta shiga amfani da su..

Tuni ta koma danya shar... Nan da nan Habib ya dawo kanta.. Saboda faranta mishi da take yi ma kudin da yake bata har doubling yayi wanda rabin su suke zuwa wurin Lami yayinda sauran suke shiga ma'ajiyar su ita da mama 'Ghana must go'

A lokacin da aka fara examz ne Layla ta fara zama a makaranta domin kuwa ta sani sarai idan bata ci jarabawa ba zata hadu da fushin Abba.

Kamar yadda ta qudurta a ranta kusa da Ameera ta dinga zama tana kwasar amsa.. Abin har mamaki ya dinga ba Zarah yadda take wulaqanta Ameera amma da jarabawa ta zo babu ko kunya ta maqale mata tana satar amsa.

A haka dai aka gama examz aka bayar da hutun wata daya.

♤♤♤♤♤♤♤♤

HABIB ALIYU NASIDI RESIDENCE
MARAFA ESTATE

Kwance take a kan gadon dakin shi cikin Duvet yayinda take kallon shi a tsaye gaban Vanity mirror yana shiryawa.

Tunda aka basu hutu a kullum Habib zai shigo unguwar su ya jirata su tafi gidan shi.. Har yau dai ya qi zuwa ganin Abba, kullum excuse dinshi daban.. tun tana yi mishi magana har ta haqura ta qyale shi.

A yanzu haka tsawon awa uku kenan suna gurzar juna.. bayan sun sarara ma juna ne ya shiga bathroom yayi wanka.

"Sweetheart wai ya maganar auren mu ne?" ta tambaye shi.

Zuciyar shi ce ta buga da jin wannan tambayar nata.. Ya ma za'a yi ya aure ta?? ko giyan wake ya sha ai bazai aureta ba. A yanzu kuwa ya amince da zancen Yusuf da yake fadin babu yadda za'a yi ya auri macen da ya gama sani a titi...

Murmushi yayi ya juyo ya kalle ta yace "Very soon my pretty.. I really cant wait to have you everyday"

"Nima haka sweetheart.. na gaji da wannan harkar da muke yi babu aure a tsakanin mu kuma bana so yadda nake shan pills dinnan sossai domin kuwa ina tsoron kar suyi mun illa nan gaba"

ZABI NA | ✔Where stories live. Discover now