Chapter 5

1K 197 53
                                    

“A busy life makes prayer harder, but prayer makes a busy life easier.”
~~~Anonymous~~~

♤♤♤♤♤

✍ZABI NA✍

Weeks later!!

KADUNA STATE UNIVERSITY

A yau satin su uku da fara zuwa KASU. Kamar yadda na fadi muku ajin Layla daya da Ameera.

Mai adaidaitan su yake kai su sannan ya dauko su. Da zarar sun shiga makarantar kuwa Layla da Ameera suke kasancewa tamkar ba daga gida daya suke ba.

Layla dai tun ranar farko da suka fara zuwa tayi screening 'yan ajin gaba daya.. tuni ta gano clique din manyan yara.. don haka ba tare da bata lokaci ba ta shige musu. Da ganin Layla dai ka san ba 'yar mai kudi bace amma kuma a dalilin bala'in kyan ta sai ta samu shigewa cikin su.

A yanzu haka clique dinsu su Hudu ne- Haleema (leema), Maryam (Mari), Yusrah (Yussy) sai ita Layla.

☆☆☆☆☆☆☆

HALEEMA IDRIS BUNGUDU: Mahaifinta Alhaji Idris Bungudu shine mamallakin IB Oil and Gas Nig. Ltd. Shahararren Oil and gas company dinnan wanda yayi fice wurin shigowa da fitar da mai a qasar nan.. Alhaji Idris yana da kudi sossai domin kuwa babu state din da babu gidan man shi a arewacin Nigeria. Haleema wadda aka fi sani da Leema ita kadai ce 'yar shi don haka ta taso cikin gata.. Babu abinda ta nema a rayuwarta ta rasa.. Haka kuma duk abinda take so tana samu. Sossai iyayen ta suka sangarta ta- they never say No to her. Da farko dai iyayen Haleema sun tura ta qasar America ne don tayi karatun jami'ar ta a can amma da zuwan ta wata daya aka kira mahaifinta ya zo ya tafi da ita saboda she was disregarding the school's moral ethics... Ko da aka mayar da ita Qasar Ingila nan ma haka.. Taurin kan bala'in Haleema ya hana ta zama.. Babu dama ka ce mata tayi abinda bata son yi... Da wannan ne mahaifinta ya dawo da ita Nigeria.. Da farko ya so ya sa ta Nile ko Baze a Abuja amma tace ta fi son KASU.. ta fadi hakan ne saboda ta raina ma makarantar, ta sani cewar zata iya yin duk abinda take so sannan ta taka duk wanda ta ga dama tunda dai Money speaks for her and mahaifinta made sure of it. Tunda ta shiga KASU kuwa sai ta ga dama take shiga class din, Haka lecturer bai isa yace mata tayi wani abu ba don kuwa babu wanda bai san she is untouchable ba. Haleema tana da manyan samari masu kudi.. Irin samarin nan da suke ji da kansu, irin spoilt brats dinnan... Haleema har party tana zuwa.. sai ta kwana a waje ba tare da iyayen ta sun damu ba. Yanzu haka tana da motocin hawa har guda uku and shekarunta Goma sha tara.

MARYAM SANI DAURA: Marainiya ce, iyayenta sun rasu tun tana qarama.. Ta girma a hannun babban yayan ta Mansir Sani Daura Manajan Banki a nan Kaduna. Iyayen su kafin su rasu sun tara dukiya mai yawa domin kuwa sunyi aiki a World bank na qasar Ingila tsawon shekaru. A dalilin tausayin Maryam da yake yi shiyasa yake yi mata duk wani abinda take so. Babu laifi Maryam tana da hankali, tana da qoqari a makaranta sannan tana girmama na gaba da ita. Wannan ne ya sa matar yayan ta take jin dadin zama da ita. Ta saba da familyn yayan ta sossai shiyasa ko da ta gama secondary school da yayanta yace ta zabi duk qasar da take son yin karatun jami'arta sai ta ce ta fi son KASU. Ta fi so ta cigaba da zama tare da su. Da wannan ne ta shiga KASU din. Maryam wadda aka fi sani da Mari dai tana mingling da Haleema ne ba don komai ba sai don Social class din su da ya kusa zama iri daya amma ba don hali ba.. Asali Haleema da Maryam are two different personalities.. Kusan a dalilin Maryam da Yusrah ne ma Haleema take shiga class. Maryam tana da motar hawa sannan shekarun ta goma sha takwas a yanzu. Tana da saurayinta mai suna Khalil Muhammad Bicci wanda yake karatun Law a qasar Ingila.. tuni maganar su ta kai wurin manya don haka jira kawai ake yi ya kammala idan ya dawo ayi bikin su.

ZABI NA | ✔Where stories live. Discover now