Chapter 32

1.4K 237 90
                                    

"Happiness will never come to those who fail to appreciate the blessings they already have. Say Alhamdulillah every moment of life"
~~~anonymous~~~

♤♤♤♤♤♤♤♤

✍ZABI NA✍

ZAYD AHMAD FADOUL'S RESIDENCE
UNGUWAN RIMI GRA

Wuraren qarfe tara na dare Ameera tana tsaye a gaban daya daga cikin wadrobes din dressing room na dakinta daure da towel... Da alama wanka tayi.

Basu dade da dawowa daga gidan Abba ba..

Ko da Zayd ya koma gidan Abba zama yayi akayi hira sossai harda Abban.. Sai da suka yi dinner sannan suka bar gidan..

Ita kuwa Mama tana can cikin daki tana ta faman lallashin 'yarta wadda duk ta bi ta haukace.. Ta qarfafa mata qwarin gwiwa akan lallai da zarar Hajiya Suwaiba ta ga Malam toh lallai Hanya zata yi musu kyau.

Ko da suka shigo gida kuwa Ameera wucewa tayi straight sashen ta don yin wanka.

Ameera tayi kusan minti biyar tsaye tana qare ma kayan baccin ta kallo.. Kayan bacci ne kala-kala har basu qirguwa..

Zaheera, Zarah da su Maheera ne suka jera mata su a wadrobe din tare da sauran kayan lefenta.. idan ka bude wadrobes din ka ga yadda aka jera kayan zaka yi zaton na sayarwa ne aka jera a shago..

Gani nayi ta sa hannu ta janyo wani pyjamas na riga mai dogon hannu da dogon wando cotton ta sanya sannan ta dauko hula ta sa a kanta tare da tura ta baya yadda bazata dinga taba stitches din da yake kan hairline dinta ba.

Ko da ta fito daga dressing room din sai gani nayi ta tsaya cak tana kallon shi cike da mamaki..

Yaushe ya shigo???

Zayd ne zaune a kan gadonta riqe da wayoyi a hannun shi.. Ga kuma kwalayen su a gefen shi bisa gadon harda sim cutter.

Sanye yake cikin three quarter sweat da T-shirt... sossai yayi kyau, Gashin nan nashi na larabawa ya sha gyara ya kwanta sai qyalli yake yi.. ya fito sak a balaraben shi. Duk turarukan da ta fesa bayan ta fito wanka sai ta ji ta daina jin qamshin su a dalilin na Zayd mai sanyi da dadin bala'i da ya cika ko ina..

Ameera dai zuba mishi idanuwa tayi babu ko qyaftawa yayinda tayi nisa a tunani..

Allah ma ya sani tana masifar son Zayd!

"Habibty wannan kallon fa??" ta jiyo muryar shi.

Ajiyar zuciya ta saki sannan tayi murmushi tare da wayancewa tace "me kake yi??"

Gani nayi ta qaraso wurin shi ta zauna kusa da shi a gefen gadon.

"Na kawo miki new phones ne shine nake sa miki sim card dinki a ciki.."

Ya miqa mata Samsung galaxy S21 ultra sannan yace "your main line is here.. na cire shi daga wayarki na sa miki a ciki" 

Ya miqa mata I-phone 12pro max yace "wannan kuma na sa miki sabon sim"

Ameera wadda ta karbi wayoyin tana kallon shi tace "Yaya me zanyi da wayoyi har biyu? wallahi daya ma ta isa"

Ba tare da yayi responding to maganar da tayi ba ne yace "kinyi kyau sossai Habibty.. you are beautiful"

Duqar da kanta tayi tana murmushi tace "nagode Yaya.."

"again, this..." ya janyo kwalin Macbook pro (laptop) ya cigaba da fadin "...is yours too, tunda na cinye miki kudin ta lokacin da na kwanta a asibiti"

ZABI NA | ✔Where stories live. Discover now