Chapter 37

1.3K 191 89
                                    

Born from different mothers skins of all colours come together as brothers . that’s the beauty of Islam.

♤♤♤♤♤♤♤

✍ZABI NA✍

GIDAN MALAM FAROUQ ABDALLAH
MALALI

Kwance take a kan gadon Mama tana ta rusa kuka kamar wadda aka aiko ma saqon mutuwa.

Layla dai da qyar ta iso gida bayan ta baro kamfanin Zayd. Babu abinda yake kai da komowa a qwalwarta sai kalan wulaqancin da Zayd yayi mata..

Mama wadda take zaune tayi tagumi mamaki ne ya hana ta magana..

"toh wai ban gane ba.. kenan kwallin malamin bai yi aiki bane ko me??? ko dai bai kalli cikin idanuwan naki bane?"

"wallahi Mama ya kalli cikin idanuwana.. idan kika ga irin kallon da yayi mun ma sai kin tausaya mun.. Zaune fa na ganta a bisa cinyar shi suna ta sumbatar juma kamar zasu cinye juna.. Yanzu fisabilillah ta ina wannan baqar banzar ta dace da shi?? Na shiga uku yanzu shikenan Ameera ta cuce ni a rayuwa.." Layla ta fada tana kuka.

Mama wadda kanta yake a kulle ta mirgina ta janyo wayarta tana fadin "aikuwa bari in kira Hajiya Suwaiba, ya za'a yi in sakar mata kudi har naira dubu dari tara sannan ace ba'a samu yadda ake so ba.. ai wannan ma zancen banza ne"

Bayan ta latsa lambar Hajiya Suwaiba ne tayi answering.. Mama ta sanya wayar a speakerphone yadda Layla zata ji.

"Hajiya Hindatu muna lafiya??"

"Hajiya Suwaiba ai babu zancen gaisuwa.. Ga yarinya ta yi ido hudu da yaro amma babu abinda ta samu sai wulaqanci, me ke faruwa ne??"

Shiru suka ji ta dan yi sannan tayi gyaran murya tace "ban gane wulaqanci ba.. in ce dai ta kira sunan shi sau uku kafin ta shafa kwallin??"

Cikin muryar kuka Layla tace "wallahi na kira sunan shi sau uku kamar yadda kika fada"

"Layla ki daina kuka.. dama na manta ban sanar muku ba.. Malamin yace akwai wadanda jinin su yake da qarfi don haka suna yin kwana biyu zuwa uku kafin maganin yayi tasiri akan su.. ina kyautata zaton wannan din yana da jini mai qarfi ne, idan har kin tabbatar kunyi ido hudu da shi mu jira nan da kwana ukun ina mai tabbatar miki cewar zai biyo ki har gida.."

"haba, yanzu na ji batu Hajiya Suwaiba.. ina nan har na fara tunanin kudaden da aka kashe ace babu sakamako mai kyau ai abu bai yi ba" cewar Mama wadda harda sakin murmushi.

"ai kar ki ji komai Hajiya Hindatu.. magani dai yana nan zai yi aikin shi"

A haka dai suka cigaba da hirar su yayinda hankalin Layla ya dan kwanta..

☆☆☆☆☆☆☆

GIDAN HAJIYA SUWAIBA
BADARAWA

Zaune take a falonta tare da qawar ta Hajiya Barira a lokacin da take waya da Mama.

Bayan sunyi sallama ne ta gyara zama tare da kallon Hajiya Barira tace "yau na shiga uku na ci kudin cizo.. aikuwa akwai matsala"

"ke kuwa wace matsala tunda dai kin riga kin gama da su.. ai kawai dagewa zakiyi akan lallai yarinyar bata yi amfani da kwallin kamar yadda ya kamata ba shiyasa aikin bai yiwu ba.." Hajiya Barira ta fada tana murmushi.

"ai baki sani ba.. Hajiya Hindatu muguwar taqadara ce.. wallahi idan nayi sake zata iya wulaqanta ni a dalilin wadannan kudade da na danne.."

Asali dai Hajiya Suwaiba ko da ta je gaban malaminta a garin Hadeja tayi mishi bayanin komai da abinda ake buqata.. ko da ya bubuga qasar shi ya duba ya gani ya fadi mata gaskiyar lamarin.. Gaskiyan lamarin kuwa shine babu wanda zai iya raba auren Ameera da Zayd, idan kuwa mutum yayi qoqarin raba su toh zai shiga babban matsala a rayuwa idan har bai rasa ran shi ba don haka yace bazai taba sa hannun shi a abinda ya fi qarfin shi ba kuma ya ba Hajiya Suwaiba shawara akan ta cire hannunta a lamarin domin kuwa ita kanta bazata gama lafiya ba balle those that are directly involved. Dayake ta riga ta shaqi kudade a hannun Hajiya Suwaiba sai ta ga bazata iya mayar mata da su ba musamman ganin yadda ta debo mata kudin daga qatuwar Ghana-must-go wadda ta tabbatar mata da tana da su dayawa kenan..

ZABI NA | ✔Where stories live. Discover now