Chapter 16

1K 210 94
                                    

 “And whoever puts all his trust in Allah (God), then He will suffice him.”
~~~Quran 65:3~~~

♤♤♤♤♤

✍ZABI NA✍

MONARCH HOSPITAL

Zaune take a kan kujerar da take gefen gadon da yake kwance yayinda ta qura mishi idanuwa.

Likita dai yayi mata bayanin cewar jinin shi ne ya hau a dalilin tashin hankalin da ya shiga sannan akwai alamun stress a tattare da shi don haka ya bata shawara akan a kula da shi sossai.

Kusan tsawon awanni hudu kenan Zayd yana bacci.. tsawon wannan lokacin Ameera tana nan zaune tana jiran a bata damar ganin shi... Gaba daya hankalinta a tashe yake. A nan masallacin asibitin tayi sallar Azahar da la'asar.

Zayd dai har a wannan lokacin da Ameera ta shigo dakin bacci yake yi... Cannula ce maqale a hannun shi yayinda ledar ruwa take sagale a wani qarfe.. A yanzu haka yana kan leda na biyu kenan.

Kyakyawar fuskar shi take ta kallo yayinda soyayyar shi take bi jini da jijiyar ta. Cikin dan qanqanin lokaci har ya rame.. dukda yana kwance a gadon asibiti yayi masifar kyau.

"Ya Zayd meyasa kake nema ka halakar da rayuwar ka saboda Ya Layla?? someone that doesnt care about you.. For crying out loud it's not the end of the world don tace bata sonka.. wai baka san akwai masu sonka bane??? Ya Zayd kana da hali mai kyau, to me you are perfect in every aspect, Ya Layla doesn't know what she has missed.. she doesn't even deserve a kind hearted soul like you.. Ya Zayd why does it have to be her?? saboda ita kyakyawa ce? saboda tana da jiki mai kyau? saboda ita fara ce?? saboda tana da dogon gashi??? is it all about the physical appearance?? what about the feeling??"

Shiru tayi yayinda take share hawayen fuskarta sannan ta cigaba da fadin "How I wish ranar ni ka gani, how I wish ni kace kana so, But No, a ranar ko kallo ka baka yi ba, it was as if I was invisible, as if I didnt exist.. was it because I was all covered up in Hijab??, saboda ni baqa ce??, bani da kyau??, saboda I was looking all dull?? Ya Zayd shin ka san cewar tun ranar da na fara ganin ka nake sonka?? ka sani cewar a kullum da sonka nake bacci da shi nake tashi??? shin ka san yadda zuciya ta take zafi a duk lokacin da Ya Layla ta wulaqanta ka?? Ka san yadda nake ji a zuciya ta ganin ka kwance a kan gadon nan a dalilin wulaqancin da Ya Layla tayi maka?? Ya Zayd do you know how very special you are to me?? do you know that I can sacrifice my everything just to see you happy? Ya Zayd meyasa baka ce ni kake so ba??"

Gani nayi ta kwantar da kanta kan gadon da yake kwance daf da hannuwan shi tana kuka yayinda ta cigaba da fadin "Ban taba yin soyayya ba, ban san meye soyayya ba sai a kanka Ya Zayd.. Allah ya sani nayi qoqarin in cire ka daga zuciya ta knowing cewar kai saurayin Ya Layla ne but it wasnt just possible.. it's as if soyayyarka wani chip ne da aka dasa shi permanently a cikin zuciya ta.. Ya Zayd please tell me, ya kake so inyi da rayuwa ta?? ta ya zan cire ka daga cikin zuciya ta?? If only one day zaka zo kace kana sona Ya Zayd, if only that day you will ask me to marry you wallahi I wont think twice before accepting saboda ina bala'in sonka.. I love you for who you are and what you are.. I love you more than Life itself Ya Zayd.. Kai ne ZABI NA a koda yaushe. See, Unlike my sister ni ban damu da rashin arzikin ka ba, arziki na Allah ne na sani kuma ma ni bana sha'awar auren mai arziki.. Kawai ina son in auri namijin da zai bani lokacin shi.. Idan har zan samu soyayyarka da lokacin ka wallahi bani da sauran matsala a rayuwa ta. Na sani cewar bazaka taba so na ba and again na sani cewar har in mutu bazan taba daina sonka ba kuma bazan taba son wani kamar yadda nake son ka ba.. A matsayina na wadda take sonka zan cigaba da yi maka addu'a akan Allah ya hada ka da wadda zata so ka tsakani da Allah ta kula da kai.. Ni kuma zan cigaba da rayuwa cikin soyayyarka, I will continue to dwell in your love till the day I die.."

ZABI NA | ✔Where stories live. Discover now