Chapter 15

1.1K 182 62
                                    

 “The richest of the rich is the one who is not a prisoner to greed.”
~~~Ali Ibn Abi Talib (R.A)~~~

♤♤♤♤♤

ZABI NA✍

Wani ikon Allah kuwa tun daga wannan ranar Layla ta fita harkar Habib gaba daya.. idan ya kira wayarta bata picking, haka idan ya aika mata text message bata replying. Idan ya je school wurinta bata fitowa.. Haka saqonnin da yake ba Haleema ta bata duk bata sauraron ta.. Abin mamaki sai gashi kullum tare da Layla ake lectures har a gama...

Ameera ta ji dadi sossai ganin yadda ta mayar da hankali akan karatu musamman don saboda an kusa fara jarabawa. Qawayen su Yusrah da Maryam sunyi mamakin yadda Layla ta canza.. sun kula kwana biyu Habib ya daina zuwa.. Ko da suka tambayeta sai ce musu tayi sunyi fada ne. Su kam har ga Allah sun ji dadi don kuwa daga Yusuf har Habib basu kwanta musu a rai ba. Fatan su shine Allah yasa kar su shirya..

A bangaren Habib tun yana sa ran Layla zata haqura ta biyo shi har abin ya fara bashi tsoro.. Ya kula dagaske fushi tayi kuma da alama bazata sauko ba.. sossai ya shiga damuwa sannan ga muguwar sha'awar ta da ke addabar shi. Gaba daya ya kasa mu'amala da wata mace tun daga wannan ranar, hatta Fiddy da yake jin dadin kasancewa da ita ya kasa samun natsuwa tare da ita.. Ya qudiri niyyar dawo da Layla cikin rayuwar shi ta kowacce hanya.

A cikin 'yan kwanakin kuwa Mama ta kula Layla ta daina kawo kudi.. Ko da ta tambaye ta sai tayi mata qaryar yayi tafiya ne.

Har ga Allah Layla tayi missing din Habib.. wani lokaci idan ya kira wayarta ko ya aiko mata text message sai ta ji kamar tayi responding.. Kalaman da yake aiko mata ne suke qara tabbatar mata da lallai yana son ta kuma yana son auren ta amma kuma abinda ya faru tsakanin su fa?? Wannan abu dai ya tsaya mata a rai, tabbas wannan abu yayi mata dadi bazata yi qarya ba, kai har mafarki take yi na abin.. takan tashi bacci da muguwar sha'awar son sake yin wannan abu..

Akwai lokuttan da take ji kamar ta koma ma Habib su cigaba da rayuwar su tunda dai Haleema ma tana yi kuma babu wanda ya sani sannan the most important thing is akwai pills din da zasu iya hana ta daukan ciki..

Subhanalillah...

A wannan lokacin Layla ta zama so confused.. Na daya ga feelings dinta da take qoqarin yin yaqi da shi, gashi kwana biyu ta daina kama kudade sannan kuma ga nacin shi Habib din da kuma pressure da Haleema take applying...

Shaidan ne yayi galaba a kanta inda ta bada kai bori ya hau..

Tuni ta amince ma Habib suka koma gidan jiya.. Ya masifar jin dadin wannan abu don kuwa har ya fidda ran qara samun ta..

A yanzu kuwa musamman yake zuwa makaranta ya dauke ta su tafi gidan shi suyi iskancin su son ran su sannan ya bata kudi ya dawo da ita school.

Yusrah da Maryam basu ji dadin shiryawar Habib da Layla ba.. Gaba daya hankalinta baya kan karatu. Sun yi musu nasiha ita da Haleema amma sam sun qi saurarar su. Ameera tana kula da yadda Layla bata zama class sam-sam. wannan abu yana baqanta mata rai.. qawarta Zarah ce tace ta daina damuwa da ita tunda dai tayi nisa bata jin kira kuma ma idan tana sa kanta cikin hidimar Layla babu abinda yake qara janyo mata ita da mahaifiyarta sai baqin jini.

Ita dai Mama tana nan kullum tana boye kudade cikin Ghana must go a wadrobe... kullum tana cikin sanya ma Layla albarka. A yanzu ta dinka manyan atamfofi dayawa wanda idan ta sanya ta shiga qawayenta sossai suke respecting dinta.. dama dai abinda take so kenan

Abba dai bai san abinda yake faruwa ba.. ita kanta Umma ta dai ga Mama tana sanya manyan atamfofi idan zata fita amma bata san ina take samun su ba...

ZABI NA | ✔Where stories live. Discover now