Chapter 29

1.5K 256 107
                                    

"When Allah talks about giving to those who are in need of money, food, clothing, etc. in surah al-isra, He doesn't refer to it as "helping the miskeen" or "giving charity to the miskeen" Allah refers to this act as giving them what is their right and what they deserve. It is their right upon me and you and Allah is watching"
~~~ Nouman Ali Khan~~~

♤♤♤♤♤♤♤

✍ZABI NA✍

3 days Later..

AHMAD MUHAMMAD FADOUL RESIDENCE
UNGUWAN RIMI GRA

Kwance take a cikin Duvet a kan gadon dakin tana ta kuka yayinda Zaheera take zaune a gefenta tana lallashinta.

Tun ranar da ta farka aka sanar da ita komai ta birkice musu.. Roqon Abba ta dinga yi akan a warware auren don ita ba Zayd din da take so bane wannan amma sam Abba ya qi sauraron ta. Gaba daya yinin ranar ana ta faman lallashin Ameera amma ta qi sauraron kowa.. Wannan abu ya ba Aunties dinta mamaki sossai.. Zarah da Zaheera tare da 'yan biyu kuwa har rasa bakin lallashi suka yi..

Ammi ce ma tayi qoqari ta shawo kanta har ta daina kukan da take yi amma fa ta qi yi ma kowa magana musamman Zayd wanda da zarar ya shigo dakin nata sai ta juya mishi baya tayi kamar tana bacci.. haka yake zama yayi ta mata magana yana bata haquri amma sam bata ce mishi komai.

Sossai wannan abu ya dame shi.. Da ka gan shi a 'yan kwanakin zaka gane yana da damuwa.

Ko da ya ga abu ya qi gaba ya qi baya ne ya matsa ma likitocin akan a sallame ta tunda she is doing very much better, a ganin shi maybe change of environment will help clear her mind kuma ma shi kanshi ya gaji da asibitin..

Dr George ya amince Ameera ta tafi gida.. nan da nan yayi discharging dinta tare da basu medication dinta da kuma yi musu alqawarin zuwa duba ta.

A nan asibitin Abba da Umma suka zaunar da Ameera suka yi mata nasiha sossai sannan suka yi mata addu'a... tana ji tana gani suka tafi suka barta yayinda ta dinga kuka.

Ammi dai ta sani sarai idan ta bar Zayd ya tafi da Ameera wahala zai sha don kuwa ta kula yarinyar akwai kafiya da tsatsaurar ra'ayi..

Nan da nan tayi shawara da Zayd din akan lallai a wuce da ita gidan ta tayi koda kwana daya sannan ta tare.

Da farko bai so hakan ba don kuwa ya sa a ranshi lallai idan yayi ma Ameera bayanin komai zata gane.. all he need is space with her and he believes he can clear the air.. he couldn't refuse his mom and so he had no choice but to agree to her decision.

A nan asibitin Zarah da Mustapha suka yi musu sallama..

Zarah tayi ma qawarta alqawarin zata ziyarce ta idan ta tare gidan mijinta.

Zayd ma ganin ko ya bi su matar tashi ba fuska zata bashi bane ya wuce Kamfanin shi inda ake needing attention dinshi for the past days...

Tunda suka shigo gidan Abbu kuwa hankalinta ya qara tashi domin kuwa bata taba ganin danqareren gida kamar shi ba.. ta ya zatayi adjusting da irin wannan rayuwar?? Ga qannen shi Zaheera, Maheera, Meher harda dangin Ammi na Adamawa da suke maqale da ita kamar chewing gum.. Hatta Ridwan, Riyaz da Baby eesh (yaran Zaheera) suna nan maqale kamar sun san ta dama.. Ta ya zata yi adjusting da wadannan mutanen???

Duk inda ta juya all she see is kyawawan yara masu dogon gashi na larabawa da fulanin asali, ko alama bata dace ba a matsayin matar yayan su.. class dinsu bai yi matching ba.. for the first time ta amince da maganar Layla da tace ta fi dacewa da shi, atleast ita kyakyawa ce fara mai dogon gashi don haka ko banza sunyi matching a ta nan bangaren..

ZABI NA | ✔Where stories live. Discover now