1

2.1K 120 30
                                    


(بِسْمِ ٱللَّٰهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ), "
In the name of God, the Most Gracious, the Most Merciful.



KANO, NIGERIA.
2014


Garin kano cike yake mak'il da jama'a, dukda garin yana da yalwar mutane amma na ranar yau ya fita daban, ba abinda kake ji sai k'arar siren, wanda ya zama tamkar kid'a aka saka sun karaye ko ina, wala kana cikin gida wala kana waje, dole k'arar ta tarda kunuwan ka, babu masakaya tsinke a titina dan in har ka kuskara ka fito to ba kai ba isa inda zaka je da wuri har sai tswan wasu lukuta sandaiyar wani masifaffan traffic din da ya had'e garin, wasu titunan ma gaba ki d'aya a kulle suke, saboda tsaron da aka zuba, na sojoji, yan sanda, ko ince kusan duk wata hukuma me uniform, a dalilin manyan mutanan k'asar nigeria da zasu ziyarci garin a ranar.

Cikin garin kuwa, inda tanfastsan gidan sarki yake yafi ko ina cika, ita kanta hanyar kan ka bita sai kasha gwagwar maya da dama, mutane ne ke binta, da masu mota har ma masu tafiya a k'asa, da kuma y'an jarida na gidan tv da radio da dama, duk yarda aka saka hukuma a wurin sun kasa controlling jama'ar, a dole aka bud'e wata hanya musumman indan manyan bak'in zasu dunk'a bi, aka bar d'aya hanyar ga ragowar mutanan gari sannan aka sami sauk'i.

Wasu maza je ne da sun kai a k'alla guda a shirin ke tafiya, a harabar masarautar', maza ne wanda suka amsa sunan su maza, wanda kallo d'aya zaka yi musu kasan sun tashi cikin gata da kud'i, dukkan su suna sanye cikin manyan kaya na shadda, wanda suka daku, daga gani d'unkunan nasu sun sha kud'i, babu wanda be yi kyau ba a cikin su, takawa suke a niste cikin jan aji, yayin da bodyguards sun musu runfa, sun zagaye so, harda wasu dogarai ma da sojoji, sun saka su a tsakiya dan yi musu gadi.

A cikin su akwai wasu su biyu da suka fita daban, wanda kana kallon wurin, biyun ne zasu fara jan hankalin ka, farare ne sol dan sunfi kuwa haske a wurin, wanda zaka iya cewa sun had'a ruwa biyu, kama suke, kama sosai kamar an tsaga kara da zai baka tabbacin, lallai ciki d'aya suka fito, in ka musu kallon tsoro, zaka iya ce musu y'an biyu sai dai in har ka k'ara musu kallon k'urulla sannan zaka san yaya da k'ani ne, kawai k'arfin jini ne, dan daga yanayin fuskar su zaka ga d'aya ya manyanta, d'aya kuma akwai k'uruciya a tare dashi.

Babban na cikin wata farar getzner da ta sha aiki, yayin da k'aramin yana sanye cikin wani yadi bak'i da ya k'ara fitowa da ainayin farar fatar shi, da kyawun fuskar shi, kud'in kayan kad'ai zai iya ciyar da gidan wani k'aramin attajirin na wata d'aya, koma fiye da haka.

Ta fiya suke cikin izza da k'asaita, barin ma k'aramin wanda kana gani kasan bashi da fara'a, wani banbacin tsakanin shi da yayan nashi, duk inda suka kusta, sai wani ni'imantaccan kamshin turare ya gwaraye wurin, kuma duk inda suka ratsa sai idanu sun bisu da kallo, da yake masarautar itama a cike yake ba laifa, dan yau an bud'e ta tare da bama mutanan gari izini su shigo su taya murna, amma a haka mutane sunyi yawa har sai da masu tsaro suka fara aikin korar jama'ar da sukayi cincirindu a wurin.

Takawa suka cigaba da yi cikin girma da isa har su ka iso makekiyar fadar sarkin, wanda ita ma zagaye ta ke da masu tsare ta, da kuma marok'a da suke ta zuba ma sarki kirarari, ganin angon ne ya saka su k'ara zafin nama, sarkin k'ofa na ganin su, ya fara masu iso, yana ga angwaye sun k'araso, murmushi sukayi mishi, sannan suka kusta kai suka shige bayan an basu izinin.

Sarki Aliyu, na kan karagar shi, yayin da fadawan shi suma suana zazzaune, manyan sarakuna da y'an siyasa ne burcik a fadar, ganin haka ya saka angwayen zubewa da fara mik'a gaisuwar su cikin girmama, wasun su harda had'aw da kirari yarda sun tabbata zai ma mai martaba dad'i, sai da sarkin be ce komi ba in ba dogarin shi da yake amsa musu gaisuwar ba, sai da suka gama gaishe shi, sannan suka mik'e sukayi cikin masarautar, dan mik'a gaisuwar su wurin me babban d'aki wato mahaifiyar sarki, kafin a gudanar da d'aurin auren.

SON ASALI.Kde žijí příběhy. Začni objevovat