Ya jima yana kallon k'ofar bayan fitar ta, k'irjinsa na masa zafi tare da rad'ad'i, yanayin da fa fita dashi be bar yawo a kwakwalrsa ba, numfashi ya fara saukewa d'aya bayan d'aya, yayin da ya juya ya maida kallon sa kan mirror, kamanin sa yake son ganin sai da sam mutum na daban ne a gaban sa, Lallai ya zama azalamin neelam, wanda baya komi sai k'untata mata, tare da wulaqanta ta, ya tozarta ta be d'auke shi a bakin komi ba, shi kansa besan haka yake da zuciya da rik'o ba, a ko yaushe yana d'aukan kansa me sauk'in kai, sai dai yanzu kam yana kokonton hakan.
A hankali ya ke sauke numfashi, dan yarda yaga karaya da rauni nasan luguda sa ta farar d'aya, yayi ma kansa alqawarin cewa neelam zata zo sa, da kuma bakinta zata ambata, wanda ko kusa bazai sab'a shi ba, kwarin gwiwa ne yazo masa da ya tuna da haka, sanadiyar da ya saka damuwar tasa ta fara sauk'i, closet d'inshi ya shiga ya d'auki sweats ya saka a jikin sa, kafin yayi kan gado ya fad'a dan yin bacci, sai dai sam sam be sami hakan cikin d'ad'in rai ba.
***
Neelam kuwa tun jiya da ta sha kukan ta, ta tashi washegari sakayau, cikin rashin damuwa, domin alqawarin da ta d'aukar ma kanta, dan kuwa da gaske take ta daina zubar da hawaye a sanadiyar mijinta, shid'in kwata kwata be cancancan ba, kuma ko ina za'a je tasan tayi iya kokarinta dan ta ruk'e auran ta, toh yanzu kam ta kai mak'ura, ta tattara ta ajiye shi gefe.Dan ma kada tunani yayi mata yawa yau tun safe ta sauko da akwati ta hau packing saboda ba Lallai su k'ara sati a garin ba, bikin anty ruky na zuwa nan da sati biyu, Sosai take cikin zumud'in komawa gida, ko taji sanyi in taga mahaifanta, tare da y'an uwanta gaba d'aya, kuma a zuciyar ta, ta gama yankewa cewa in har ta koma to tabbas baza ta dawo ba, dan zaman garin gaba ki d'aya ya sire mata a rai, shi ya saka take packing Sosai dan kada ta manta wani muhimmin abu.
Sai bayan azahar ta samu ta fito, dan tun tashin ta tana d'aki, tun fitowar ta take jin maganganu mutane biyu, sai da a ranta bata kawo komi ba tunanin ta masu aiki ne, haka ta sauko, sai dai tayi kicib'is akan benan, ganin me ta gani, ata wurin dining, mijinta na zaune, da wannan matar da ta gani kwanaki, abunda ya k'ara bata mamaki be wuce dariyar da take kyalkyalawa ba tana fad'a wa jikinsa, wani abu me zafi ne ya taho ya tare mata a mak'oshi da tuni taji idanunta sun fara cika da kwalla, ganin be dakatar da ita ba balle ya tsawatar mata.
Lallai ya k'ara tabbatar mata be d'auke ta a matsayin komi ba, dan beji kunya ba, tare da ganin girman auran su da har zai kawo wata k'atuwa cikin gidan su na sunna, haka abu me rad'ad'i ya cigaba da caccakar k'irjinta amma har lokacin tak'i amincewa hawayen ta su gangaro, dan in sun zubo babu abunda zasu k'ara mata sai dai takaicin kanta da zai dame ta.
Cikin kwarin gwiwa ta k'arasa sauka, sai a lokacin hankalin su ya karkata kanta, wata fara'a ce ta sauka akan fuskar matar ganinta, da sauri ta mik'e ta yi kanta, yayin da asad kuma ta kasa karanatar sa, mik'a mata hannu tayi cikin murmushi, tare da cewa "hello, I'm Grace"
Sai da ta kalli hannun tsab, kamar kada ta amsa gaisuwar wata zuciyar tace ta maida mata da aniyar ta, dan me amfani kishi akan namiji da yake wulaqanta ka, wanda baya daraja ka tare da ganin k'ima da mutuncin ka, haka, tana gama tunani, ta saka yak'e a fuskar ta, itama ta mik'a mata hannu sai dai bata ce mata komi ba,
Ganin haka Grace d'in, ta saki hannunta, da alama taji a jikinta, neelam d'in yak'e take, juyawa tayi ta nuna wurin dining d'in inda takardu suke a baje, sannan ta fara bayani,
"Nazo kan wasu takardu ne da suke buk'atar signing tare da tattanawa, Allah dai ya saka baza ki damu ba" ta harshan turanci ta fad'i.
Wannan murmushin nata me k'ara mata azabar kyau ta sake sakar mata, cikin wanan muryar tata, me sanyi tace, "kada ki damu ba sai kin mun bayani ba, tunda me gidan da kanshi ya baki damar zama, baki da matsala ko kad'an"
Tana ji, ya k'ara dasa mata kallo, amma yarda take jin haushin sa tare da takaicin sa a ranta be mutar mata da baki ba, k'arasa har inda Grace take a tsaye, tare da d'an tab'a kaf'ad'inta, "Make yourself at home, don't mind me"