40

843 91 70
                                    

Ko bayan shigar ta d'aki ya shafe kusan minti goma yana jingina da bango yayin da idanunsa na sauke akan wayar da ta bar masa a hannu, ya karanta message d'in yaje ya dawo, ya k'ara karantawa babu adadi, a lokacin ya rasa k'unar rai zai cigaba da yi ko kuma danasanin abunda ya aikata a kanta, tabbas ta aika masa da text d'in amma me ya saka tayi gaban kanta bata tsaya taga amsar sa ba, abunda ya k'ara tabbatar mai da tasan me tayi, dan tana da ilim

Ya dad'e a haka sai numfashi da yake faman saukewa da zai nuna maka har lokacin be sauko ba, dole ya kawo k'arshan rashin mutuncin ta dan ya lura in har yana mata sanyi baza ta tab'a canzawa ba, sama ya hau rai a b'ace dan yayi k'uduri niyyar aikata mata dukkan abunda yayi niyya kuma babu wanda ya isa ya hana sa.

A cikin ranar sai da ya saka aka manna CCTV a ko ina na gidan yarda zai dunk'a ganin duk wani mostin ta in har baya nan, sannan kuma ya saka aka canza lock na k'ofar waje yarda ko muk'ullin ta bazai yi amfani ba, in har ta kira sa mugu zai nuna mata tsantsar mugunta, daga yau ba ita babu fita babu kuma wanda zai shigo ganin ta, zai nuna mata iko dan kuwa shine me ikon akan ta ba ita ba.

***
Kwance take akan gado, yayin da idanunta na lumshe, ka ganta zaka yi zatan tana cikin kunciyar hankali, ko kuma bacci take amma sam sam, tana cikin k'uncin da ta kasa tab'uka komi, abunda ya faru da ita jiya ya tafiyar mata da duk wani kuzarin ta, k'arfin ta tare da kwad'ayin zama matar gidan, a cikin wata d'aya, ya nuna mata zallan halin sa, ya nuna mata maza duk d'aya suke, babu imani a tare dasu, dan da ya asad daban yake da duk fushi duk b'acin ran da  yake ciki bazai yi mata kalar wulaqancin da yayi mata ba, abunda yafi d'aga mata hankali be wuce yarda ya hau kanta dan aikata son zuciyar sa bayan ya jefe ta da kalamu mafi muni a rayuwarta wanda bata ji ko mak'iyin sa zai fad'awa kwatankwacin su.

Hannunta ta saka ta share kwallar ta, wacce ta zuba babu iyaka, dan ka ganta yanzu ta canza kamni dan tsanani kuka, farar fuskar ta koma ja sol, idanunta sun kumburo sunyi suntum, ga wani ciwon kai me azaba da ya addabe ta dan rashin bacci da rashin saka wani abu a cikin ta, babu farin ciki a tare da ita tun bayan auran, zama take a gidan zaman da babu dad'i wanda bata tab'a yi wa wani k'orafin hakan ba, dan a ganin ta aje a dawo zai dawo nuna mata zallar kula kamar a baya dan kuwa me sonka me sonka ne, sai dai jiya ya dakatar mata da duk wani tunanin ta da burin da take akan sa na nuna mata tsnatsar tsana da k'iyayya wanda shine abunda yafi komi yi mata ciwo.

Da zai tsaga zuciyarta da zai ga babu ko da d'igo d'aya na k'in sa, ko kuma cutar sa da har zai iya cewa zata k'untata mai, duk yarda take yawan nuna ko in kula a alamaran sa, tare da son kunno sa ta wani b'angaran, tana yi ne dan kawai ta hana zuciyar ta hab'akar mata da duk wani abu da take ji game dashi, a yanzu farin cikin sa na gaba da komi a gare ta, tsoron gwaliya a wurin sa, da fargabar in har ta shiga gonar sa sai iya aikata mata son ransa, shi ya saka take yak'e ta nuna masa halayar da yafi tsana da kyamata a rayuwar sa.

Saukar numfashi kawai take dan har ji tayi jikinta ya d'au zafi dan tsananin damuwar da take luguda ta, sanin kwanciyar ta babu abunda zata k'ara mata sai k'unci ya saka ta mik'e daga kan gadon, a gaban dressing mirror d'inta ta tsaya tana k'arewa kanta kallo dan har ta fad'a, ajiyar zuciya ta k'ar saukewa tare da saka hannu da share sauran hawayen ta, sannan tayi band'aki dan watsa ruwa me d'an d'umi dan taji dad'in jikinta, bayan ta kammala ta fito ta shirya cikin wani blue jeans, da wata cream top sannan ta fito.

Kitchen ta wuce ta dafa indomie sannan ta dawo parlor ta zauna, a lokacin neelam ta kawar da duk wata damuwa da lamarin ya asad, a niste take kallon ta a tv, har ta sami taci rabin indomien da ta dafa dukda guda d'aya ce, bayan ta kamala takai kitchen ta tuna cewa ya kamata ace ta kira simna da rahama, dan tasan ko babu komi sun shiga cikin tashin hankali jiya, d'akin ta ta shiga dan d'auko wayar sai dai duban duniya bata gani ba, tsayawa tayi tana tunanin inda da saka sai can ta tuna ta barta a hannun sa jiya.

SON ASALI.Kde žijí příběhy. Začni objevovat