Ta dad'e tana jimami ko bayan ta kashe wayar, dan dole da gaya ma neelam halin da ake ciki, dukda bata san yarda zata d'auki zancen ba amma ya wajabta tasan inda mijinta yayi, dan irin su asad ko kad'an basu cancanci a d'aga musu k'afa ba, dan basu da kirki, ta jima a haka, kafin can ta iya tashi tayi harkokin gaban ta, sai wuraran isha'i, khalaty ta dawo d'akin hannunta d'auke da wani box, akan wani d'an table a gefe ta ajiye, sannan ta koma ta zauna akan gado tana jiran fitowar neelam daga bathroom.
Ta kwashe kusan minti goma kafin ta fito, suna had'a idanu sukayi yi wa juna murmuhi, ta d'an samu kwarin jiki ba kamar d'azu ba, sai da har lokacin damuwa bata bar bayyana cikin yanayin ta ba, haka ta cigaba da k'are mata kallo har neelam ta iso gare ta ta zauna a k'asan carpet, tare da bata nustuwar ta, sun d'au d'akik'u babu wanda yace wa kowa komi, kafin khalaty ta kai hannun ta kan sumar gashin neelam da ta zubo ta maida ta baya.
Sosai yarinyar take bata tausayi dan shekarun ta sunyi kad'an da har take fuskantar tashin hankali kamar haka, tunani ta shiga ko ta boy'e mata maganar da ta zo fad'i mata, dan tasan ta sami labari abun zaiyi mata ciwo mutuk'a, sai dai kuma k'in gaya matan bashi da amfani dan hala tayi ta zaman jiran sa babu ranar dawowar sa.
Naunauyar ajiyar zuciya ta sauke, sannan tace, "kinsha maganin ki?" haka tayi ta ma neelam tambayar lafiyar ta, ita kuma tana d'aga mata kai, har sai da ta gamsu, kafin ta k'ara cewa,
"Tashi daga k'asa ki dawo kusa dani ki zauna"
Bata tashi ba har sai da ta cicib'eta, ta zaunar da ita da kanta, sannan ta k'ara ruk'o hannunta,
"Ki saurare ni da kyau neelam, kiji me zan fad'a miki"
Nan ma kai ta d'aga mata,
"D'azun nan nayi waya da aseem yake cewan asad na Nigeria mik'a gaisuwar mahaifin ki"
Da sauri da d'ago idanunta da suke kallon kan cinyarta ta saka kan khalaty, tana son ta gano ko wasa take mata, sai dai yanayin ta be nuna hakan ba, tuni abubuwan da suka faru tsakanin su tun samun rasuwar baba da tayi suka shiga dawo mata, shine sanadiyar kwace passport d'inta yarda baza ta tab'a samun hanyar fita daga garin ba, tuni zuciyar ta ta k'ara hantsulowa, ta k'ara jaddada rashin imanin sa a ranta, hala khalaty ta karanci k'unar zuciyar ta, dan ji tayi tace.
"Nima da naji hakan rai na yayi mutuk'ar b'acin, nayi fad'a a cewar uba ba wasa bane da har zai yi haka, sai dai aseem ya tabbatar mun cewa bazai tab'a yin haka ba sai da kwakwaran dalili"
Takaici ne ya rufe neelam, takaicin da har ake goya masa bayan abunda ya aikata, har ake cewa akwai dalilin bayan ita tasan tsananin k'iyyya ce, da kuma fansar da yake son d'auka akan ta.
"Zaki yarda dani nace miki bashi da wani dalili, yayi ne kawai dan ya k'untata mun"
"K'untatawa kuma? Akan me? Khalaty ta jefa mata tambayar.
Goge hawayen ta tayi da suka fara zuba, dan a lokacin a wurin tayi alqawarin baza ta saka zubar da kwalla ba ta dalilin sa ba, whalar da yake so ta shiga baza ta bari ya sami nasara ba, zata jure zata daure har sai ta samu kanta, sanin tana jiran amsar ta ya saka ta jawo nustuwar ta
"Ni da ya asad auran k'unci muke tare da k'iyyyaya, musgunawa junan mu ne ke kawai saka mu cikin walwala"
a karon farko a rayuwa ta da ta amayar wa wani matsalar auran ta, wani ma khalaty wacce batayi kwana biyu cikakku da sanin ta ba, sai dai a y'an lokutan kalilan ta shiga zuciyar ta, wanda take ji in har ta fad'i mata zata samu sukuni tare da ita, kullum tsoro da firgicin datse auran tare da son kasancewa da mjinta ke hana ta kwatanta gaya ma wani, amma sai dai yau ta kai k'oluluwa, komi ya faru ya faru, ta kai son ya asad can bayan ranta ta jefar, dan fushi take na gaske.