16

366 69 21
                                    

Ranar juma'a bayan ta dawo daga makaranta ta far shirin tatarawa zuwa gidan ya naana, daman sunyi hutun islamiyya, ta zauna a gidan isarta zaiyi.

Wata cotton candy backpack me kyau ta samu ta had'a kayanta da duk abubuwan da zata buk'ata a ciki, sannan tayi shirin ta cikin doguwar riga ta atamfa wacce style din yake plain, ta d'aura d'ankwalin ta irin d'aurin zarah buhari saurin gashin ta me yawa duk ya sauka a gadon bayan ta.

Fitowa tayi daga d'aki, a parlor ta tsinci maama na kallo, sallama tayi mata domin driver na jiranta a waje, iya dubu, sabuwar me aikin su ta rako ta da wata bak'ar leda da maama ta had'a ma ya naana kayan k'anshi.

Sauri sauri ta shiga mota, bayan ta saka komi a boot, tun driver ya figa, tana ji iya dubu nata mata Allah ya kiyaye.

A hanya suka tsaya suka d'auke asiya da yake duk unguwar su d'aya da ya nanan, sannan suka wuce.

Ko da suka isa gidan neelam taga abubuwa da dama da suka canza, sakwamakon watanin da tayi bata zo, har wani gida aka gina a kusa dashi, sak irin na ya naana, ba abunda ya raba su har kalar painti.

"Amarayar mu gafa gidan ki an kamala shi"

Asiya ce ta katse ta kamar ta fahimci tunani da take, daka mata wata muguwar harara tayi da murgud'a baki tare da cewa "na tambayeki"

Asiya ita dai dariya tayi bata sake tanka mata ba har suka shige gidan, daman tuni me aiki ta bud'e musu k'ofar shiga.

A parlor suka iske ya nana ta baje, tana ta kwalamar gyad'a da rogo, abunka da me k'aramin ciki, farhan a guje ya taho musu oyoyo, neelam tuni ta cafe shi sama.

Nan suka zauna bayan sun gama gaisawa, me aiki ta shigar musu da kayan su wani d'aki da yake cikin parlon, sai da suka sha hirar suka gama su neelam suka tuna suna jin yunwa dan tun safe rabon su da abinci.

Naana dai cewa tayi su tashi su dafa me zasu ci dan rabon ta da shiga kitchen tunda ta sami ciki, bata san kamshin abinci kwata kwata.

"Allah sarki Ya aseem bawan Allah ko me yake ci?" Cikin tsantsar zolaya neelam ta fad'a.

"Kun zo ai sai ku ciyar dashi, tunda ni mugunta na sani"

A tare asiya da neelam suka kwashe da dariya, sannan sukayi kitchen, nan suka sauri suka d'ora tuwon semo da miyar k'ubewa busarshiya, har ya aseem sai sa suka d'ibar ma a flask d'inshi suka kai mishi kan dinning suka ajiye.

**

Da daddare bayan an idar da sallar isha, ya naana tace su fito su raka ta makwabta barka, anyi haihuwa, neelam ta so ta k'in zuwa ganin series d'inta ake a ZeeTv, sai da yayar tata tayi mata jan idano tukun, asiya daman ko bata ce ayi rakayar ba binta zatayi dan akwai ta da san  yawon masifa.

Dad'in da taji gidan ba wani nisa d'an gaba ne kad'an, gida ne babba yarda dai yawancin gidajen umguwar suke, cikin kuma fara'a aka k'arbe su, abunda yayi ma neelam dad'i ta saki ranta dukda ba wani sanin su tayi, tana ma ji basu dad'e da tarewa ba dan duk zuwan ta gidan yayar tata bata san da su ba.

Bayan an kawo musu kayan tarb'a, baby na hannunta, yarinya ce mace kyakyawa, da yake matar gidan itama irin bak'aken nan ne da ake ce musu black beauty, hira ya nana take da ita Sosai kace sunyi shekara da sanin juna. Sai dai sallama da akayi duk ta tssayar da zancen su, kowa na parlon hankalin shi ya maida kan k'ofar shigowa.

Baki neelam ta saki ganin me shigowar, tare da mannewa a mazaunin ta, bata kalli asiya da take kusa da ita ba amma tasan sarai itama mamaki ne d'auke akan fuskar ta.

Shima kanshi turus yayi a k'ofar ya kasa gaba ya kasa baya, idanunsa akan neelam, dukda fuskar sa bata nuna ba tasan mamakin ganin su yake shi ma.

"Sannu dai"

SON ASALI.Kde žijí příběhy. Začni objevovat