Ji take kamar ta toshe kunuwanta ta pasa k'ara tare da rusa kuka dan takaici, kallo d'aya zaka mata kasan a k'ule take da haushi, ba kuma komi ya hardasa ba sai dan zancen mutun d'aya da ake tun bayan fitowar su daga taron mintuna 30 da suka wuce.
Ko alamun canza hirar basa yi, yaban shi kawai suke, ga farin ciki da ya mamaye fuskokin ko wannan su, ba shakka ya cancanci yabo, domin shi d'in abun alfahari ne, mutumin da ya kusa lashe kyatukan rankatataf, baya zama ake dad'e kiran shi, zai wuya mutanan da suka hallari wurin ba su tafi gida ba da mamakin shi a zuk'atun su.
Amma ita abunda bata gane ba shine, yarda za'ai ta maimaita zancen kusan awa ba'a gaji ba.
Turo baki tayi, ta taji mahaifiyar ta wacce suka fi kira da maama ta k'ara kud'a shi, ta tabbata da yana cikin motar da kansa sai ya kusa ciki ta, yarda ake zuba masa wani irin yabo, ba gaggautawa sai kace wani sahabi, mita ta ci gaba da yi a cikin ranta ita d'aya har bacci yayi gaba da ita bama ta sani ba.
***
Suna isa gida ammi ta umarce ta ita da asiya, da su kwashi kayan sa da suke cikin wasu boxes guda biyu su kai mishi d'aki, sauran k'iris neelam ta saka daru, dan ga bacci a idanunta ga gajiya, ya naana ce tayi mata wani kallo da ya saka a take ta shiga hankalin ta.
Haka suka kwasa, tana tafiya tana zumb'uro baki har suka isa d'akin nasa, dad'inta d'aya baya cikin dan sun baro su a baya shi da su ya aseem.
Box d'in dake dauke da awards d'in asiya ta bud'e tare da shirin fara zuba su akan wasu shelves dake mak'ale a jikin bango, wanda dama can yana d'auke da wasu k'anan awards d'in, ka ganta sai zumud'i take.
Ita dai neelam kai ta girgiza, dan bata ga amfani ba abunda kwanaki kad'an duk za'a kwashe su su wuce kano, sai dai bata ce komi ba, dan yarda taga jikinta na rawa ko ta fad'a ba sauraron ta zatayi ba, juyawa tayi ta fuce ta barta a d'akin.
Tana tafe tana rurufa ido, snadiyar wani naunauyan bacci da ya addabe ta, har suka kusa cin karo badan yayi saurin ruk'e kafad'unta dan tsayar da ita.
"Careful"
Deep voice d'inshi, tare da dadda d'an kamshin turaran shi ne suka wartsakar da ita, zara zara idanunta wanda suke cike da gajiya tayi saurin saukewa akan shi.
Daga yanayin shigarsa zaka san shima d'in a gajiye yake, dan tie d'inshi is undone, yayin da suit jacket d'inshi itama ya cire ta, ya sagale a hannunshi.
Amma duk wannan be hana arnan murmushi bayyana akan fuskar sa ba, wanda ta tabbata yana tafiya da imanin y'an mata.
"Duk gajiyar ce?"
Maganar sa ce ta dawo da ita duniyar da ta afka, da sauri ta zare jikinta daga hannunsa, tare da sunkuyar da kanta dan ji tayi kuma ta kasa had'a idanu dashi.
Kasa tanka mishi tayi, sai ma sum sum da tayi ta samu ta gefan shi ta wuce, sai kace bata ji me ya tambaya.
Sauri sauri take ta shiga d'aki, dan Allah ya sani, ta tsani ta gansu a inuwa d'aya, barin ma in su kad'ai ne, fad'ar sunan ta da yayi ne ya saka ta ci burki cak ta tsaya, a sanyaye ta juyo gare shi.
Suna k'ara had'a ido a karo na biyu taji wata mumunar fad'uwar gaba, kwarjinin da tsoran sa na yawan hardasa mata wannan, da gudu tayi saurin tattro nustuwarta.
"Kowa yayi congratulating d'ina banda ke, ko laifi na miki?"
Baki ta kusan saki dan mamakin da ya d'ibeta, domin shine mutumi na k'arshe da tayi zatan zai damu da hakan da har zai tamabayi dalili, amma kuma ta wani b'angaran batayi mamaki ba, dan kwana biyu tun bashi zoben nan da tayi ta lura yana yawan sakar mata fuska ba kamar daa ba.
Juyowa tayi da jikinta sosai dan ta fuskan ce shi, sannan a sanyaye tace, "i didn't think it would matter to you"
Yanayin sa ne ya d'an canza, da zaka san maganar ta ba dad'i tayi mai ba, ita kam neelam da taga shirun yayi yawa bashi da shirin cewa komi, sai dai idanunshi da suke kaf akanta, ya k'ara tabbatar mata cewa ba abunda yake san ji daga wurin ta ba kenan, tunanin me zata ce da zai gamsar da shi ta fara yi, domin ta k'agu ta bar wurin.