19

362 55 46
                                    

Present day.
 

Kwanci tashi ba wuya a wurin Allah, su neelam an kamala karatu, kuma alhamdulilah an fito da sakwanako mai kyau barin ma dai auwal da asiya, da yake su gifted ne, shekarun ba wuya, ka gansu duk sun k'ara cika, daga jiki harda ido, neelam kuwa a lokacin take tashen ji da kai tare yanga da iyayin da baza a rasa, ga samari sunyo kanta, dan bata isa ta fita ba sai ta samu masu tare ta.

Ita kuwa ba wanda take kulawa, dan yanzu tayi nisa cikin soyayyar zaid, sanshi take tamkar ranta wanda tana gani in bashi baza ta rayu ba, haka shima daga wurin sa, ji da ita yake kamar mene, soyayya suke me dad'i da anushuwa, sai dai duk yarda yake so ta bari a sanshi a gida tak'i, abunda yake saka su samun sab'ani kenan, gashi ta kasa gaya masa dalilin haka, sau da yawa yana tambayar ta kodai ba san auran sa take ba, dan yarda yaga har lokacin kaf kaf take wurin had'uwar su dan yawanci kullum sai da su had'u a waje, badai a gida ba, ita dai sai da tayi rarrashi yayi fushi tare da bashi hak'uri ya k'ara bata lokaci, inda taji dad'i san da yake mata baya saka ya dad'e yana fushi da ita.

Shirya shiryan dowwar asad yayi dai dai da lokacin bikin nusy, wacce tun bayan gama makaranta aka saka bikin, lokacin da ta fad'a musu anyo baikon ta sun dad'e suna mamaki dan basu tab'a zata tana da tsayye ba, sai da tayi musu bayanin d'an uwanta zata aura tukun, neelam kuwa tayi takaici dan ji tayi kamar ta zuga ta a fasa auran, haka kawai ka auri wani da ya gama gane yarintar ka, ai raini zai jawo, dan ita har lokacin ba wanda a cikin su yasan an saka auran ta da ya asad, kuma bata da shirin fad'a.

Yau ce dawowar asad ya kuma zamana da ranar kamun nusy, tun safe neelam ta bar gida a cewar ta zata raka nusaiba makeup domin daman ita da simna ne manya k'awaye, ganin shak'uwar su ya saka maama bata hana ta ba dukda tafi so ace asad d'in ya dawo neelam na gida.

Ita kuwa gwanar dad'i fal ciki dan ko babu komi baza ta ga dawowar sa ba, da takaicin murnar da rawar k'afar sauran dangi, daman yanzu ita da dashi ko gaisuwa bata had'a su, dan tafi shekara da blocking d'inshi a ko ina, tun yana neman ta ta wurin asiya, ko ya nana da sauran su har ya hak'ura ya daina, abun kuma ba k'aramin dad'i yayi ma mata ba, saka ranar bikin su kowa tasan baza'ayi ta ba sai ya dawo, wanda zai bata lokaci ta gama shirin da zatayi dan hana auran.

Suna sanye cikin ankon su, wanda ya zamana atamfa sai sak'i na d'aurawa da yafawa, d'inki neelam bubu simple da yake atamfar nada ado, tayi mutuk'ar kyau barin ma makeup d'in da tasha ya sake fito da ainayin kyanta dukda kwaliyar ba me yawa bace, ka kalle ta sai ka k'ara kallo, dan tafi amayar d'aukar hankali, ga baza kamshin da take duk inda ta ratsa.

Waya ce a kunnanta daga gani wayar da take na saka ta mutuk'ar nishad'i, dan yarda take ta zuba murmushi, simna da nusy kuwa sai gulmar ta suke dan sun lura soyyayar ta da zaid k'ara gaba take, sun mata murna kuwa dan duk matan da suka zuba wawtar su akan shi iata kad'ai tayi nasara.

Bayan an gana makeup d'in ne sukayi wani hotel da dangin mijin nusy suke dashi, anan akayi photoshoot masu yawa, lokacin da za'a tafi wurin event d'in kuwa, cewa simna tayi ita ta bi amarya dan tana da me kaita, bata tsaya yin bayani ba dan sunsan wane.

Tunda zaid ya d'auko neelam, ya kasa sauke idanun sa daga kanta, wani irin masifafan kyau tayi da ya saka duk yabi ya susuce, ko driving d'in da yake rabi da rabi yake yinshi dan hankalin shi gaba ki d'aya na kanta, ga wasu sunbatu da yake mata abun ma dariya ya ba ta, a haka suka samu har suka k'arasa wurin event d'in, tana ganin yayi parking ta saka hannu dan bud'ewa ta fita daga cikin motar amma yayi saurin dakatar da ita.

"Baby ya da sauri haka ne, ban gaji da ganin ki ba" cikin wani irin salo ya fad'i da tuni neelam taji jikinta yayi sanyi, itama cikin nata salon tace.

"Kana gani sai taruwa ake, yanzu za'a fara nema na"

Karkatar da kanshi yayi, tare da yi kamar zaiyi kuka, sannan yace. "Toh ki tsaya in amaryar ta k'araso sai ki tafi mana"

SON ASALI.Kde žijí příběhy. Začni objevovat