🏹💘🏹 *KIBIYAR SO* 🏹💘🏹
*ADABI WRITERS ASSO.*
*BY*
*AMEENA IBRAHEEM*
*OUM AMEER*👉 🏹💘🏹 *PAGE 4*
Haka Inna batulu tayita rayuwa cikin qunci da wahala,ci da Shan omair a qarqashin ta yake da tufafin sawarshi,haka rahane tayita shige da fice tana hada kutun guila saida ta bata omair da batulu a ko Ina tace Dan shege ne ko malam sa'idu yace ba danshi bane,Kuma batulu mayya ce ko a garinsu an shaideta kada su bari ta rabesu zata lashe musu kurwa data 'ya'yansu.Kowa gudunta yake shiyasa abun ya cakude mata,tashin omair sanda Yana qarami zance tunda suke Basu taba ganin kyakkyawa kamar shiba,shiyasa malam sa'idu da Inna rahane suka tsorata,yara har kallonshi suke idan ya fito waje,shiyasa Inna batulu ba koda yaushe take barin shi fita ba,Kuma idan Yana wasa da yaran unguwa sai uwayen yaran suzo su dauke yaransu suce su daina wasa dashi maye ne Kuma yaron aljanu.
Inna batulu bata qara tantance cikin wahala take ba,saida ta sake haihuwar balkisu da basma,alokacin tagane cewar bata da wani sauran daraja a wurin kishiyar ta rahane da mijinta sa'idu,harga diyan ita rahanen,idan suka samu omair saisu yita dukan shi babu laifin komai,idan ta sanya mishi kaya Kota wanke ta shanya a igiya kafin ta zo duk ansa reza an yayyagasu,hatta a jikinshi,a gaskiya omair yaga rayuwa ko ince yana cikin ganin rayuwa,dashida Inna da sauran qannenshi da yayunshi.
Haka kwatsam Rana tsaka Inna batulu na zaune malam sa'idu yazo tare da inna rahane yace yayiwa su bara'atu miji Kuma har garin daki takwas za'a yi auren wani wata.
Tace babu komai Allah ya sanya alheri.
Inna rahane bataji dadi ba taso tace bata yarda ba ayita masifa,Amma burinta bai cika ba.Haka akayi auren aka kaisu komai baiyi musu ba,Kuma wani abunda omair yakasa ganewa gameda Inna shine,duk inda zataje indai zata bar garin Anka toh bazata je dashi ba,saidai tabarshi nan,yayita ganin azaba har saita dawo,tun sanda aka haifeshi har zuwa yau baitaba barin garin Anka ba,da yayi batun tafiya yanzu zata nuna mishi bacin ranta,baisan miyasa ba,sonda take mishi daban ne,zance duk tafi sonshi acikin 'ya'yanta,ko mi yasa haka??kodai saboda shikadai ne namiji??
A islamiyya imtihal ta fara haduwa da omair ganin yanda yake komawa gefe daya yayi tagumi shine yasa ta fara kula da shi,da wasa wasa tun tana mishi magana yana qyaleta har ya fara karbata.
Tsoro yakeji kada itama aganta aje a hadata da iyayenta,acemusu maye ne,kada ya lashe musu kurwar 'ya.
A hankali alaqarsu ta fara nisa hartakai imtihal inbataga omair ba saitaje gidansu.
Ganin bashida kayan sawa ta gayawa Imran hakanan ya hada mishi kaya masu yawa duk da cewar sun mishi yawa sosai.
Inna batulu hadda kukanta tazo tayiwa su mama godiya.
Inna rahane kuwa tana gane alaqarsu da imtihal ta lulluba mayafin sharrinta taje gidansu imtihal ta zauna tagama munafurcin ta tsab,mama dai tayi murmushi tace ai shi da da dukiya ba'a yimusu mugunta,saboda bakasan mi gaba zatayi ba,Kuma ai da na kowa ne babu abunda omair zaiyiwa imtihal insha Allah,Kuma kada ki sake zomin da makamanciyar wannan maganar,zaki iya tafiya.
Ranar kam rahane ba'a samu sa'a ba.
Shaquwa Mai qarfi tashiga tsakaninsu.
Har zuwa yanzu bata taba yarda da yanda ake aibata shi ba,ita agareta duk canfi da qazafi kawai,Kuma Allah zai mishi sakayya.****
Cigaban labari
Yau ko da ta wayi gari tafito waje sai mamaki ya baibaye fuskarta,ganin dakin Imran a bude.
