🏹💘🏹 *KIBIYAR SO* 🏹💘🏹
*EXQUISITE WRITERS FORUM*
(Home of exquisite writers)*BY*
*AMEENA IBRAHEEM*
*OUM AMEER*
*WATTPAD @-UMMU AMEER*👉🏹💘🏹 *PAGE 9*
Haka rayuwa taci gabar musu da tafiya dukansu tsawon shekara uku,omair ya natsu sosai ya kwantar da hankalinshi,karatu yayi Mai kyau Wanda yasamu saka mako na qwarai yanzu yagama batun zuwa degree yake,duk wani gata ya sameshi daga bangaren mammi da abbah,haka shaquwa ce Mai qarfi tashiga tsakaninshi da arwa da anwar,suna girmama juna,komai na rayuwa omair ayanzu ya goge akai har mota yake ja,tsakaninshi da fu'ad kuwa abotarsu tayi girma suna nan tare hankalinsu yazo daya.Gefen imtihal kuwa,ss2 take ayanzu batasan cewar qaunar omair take ba saida yanzu da ta fara mallakar hankalin kanta,da ta dauka tausayinshi kawai take Amma yanzu ta tabbatar da zunzurutun qaunar da take mishi,ba Wanda ya taba tunkarota da sunan Yana sonta,saboda bata taba bada fuska ba,ko tare da ruqayya aka gansu ana shakkar yimusu magana,ba abunda tasa a gaba sai karatunta saikuma zaman jiran omair da take.
Kullum yah Imran Yana gefenta komai na rayuwar ta shine,koda yaushe qoqari yake yaga ya bata farinciki,Yana kula da ita Yana kula da iyayenta,hatta da Inna batulu da kanshi yake yimata siyayya taje ta kaimata har gida,idan malam sa'idu zai ganta so dubu yayi mata Jan ido bazai dameta ba,haka Inna rahane yanzu data ganta gidan zata yi shigewarta daki,hakan yasamo asali ne tun auren balkisu da akayi mommy nafi taci mata mutunci tace kuma idan tasake ko dagawa Inna batulu yatsa saita saka police sunkamata sun rufeta,toh fa tun alokacin tashiga taitayinta.
Shikuma Imran wani lokacin yana cewa ta shirya ya rakata da kanshi har qofar gida taje ta gaidata ta qara kwantar mata da hankali,ta gayamata cewar insha Allah omair zai dawo lafiya.
Kullum idan zata kwanta bacci saita dauko hoton su itada omair tana dubawa,a qirjinta take bacci tare da hoton.
Haryanzu baba baitaba yimata magana akan batun miji ba,batasan dalilinshi ba but tasan may be shima yasan cewar omair din take jira.
Yau ma da wuri ta kwanta bacci saboda gobe za'a kawo kayan ruqayya na gaisuwa,zan iya cewa ruqayya other half dinta ce,saboda tana qaunar ruqayya kuma ita kadai ce qawarta,tana son kasancewa tare da ruqayya saboda ruqayya ita kadaice tadamu da omair,tana son abunda takeso Kuma tanaqin abunda take qi,tana goyama ta baya sosai gameda da omair,tana gayamata maganganu masu kwantar da hankali.
Gari na wayewa tana gamawa mama aikin gida tafito daman Saturday ce,sanye take cikin atamfa riga da zani sai hijab tace"mama Ni zan tafi!
Cikin mamaki mama tace"Ina zaki da safennan imtihal??
"Haba mama kin manta da cewar yau za'a kawo kayan ruqayya, shine Nike sauri mama,kinsan halin ruqayya nan da nan tayi fushi.Mama tace"uhm! Indai tsakaninki da ruqayya ne duk Wanda ya shiga sai yayi kunya,amma dai kinsan cewar yayanki shima yace zai dawo yau ko??Kuma yace kada ki yarda yadawo baki nan,zai juya yakoma abinshi.
Murmushi tayi tace"hmm! Mama ki qyale yah Imran ya fadane kawai Amma bazai tafi ba sai ya ganni,wai mama haryanzu yah Imran shiru yaqi ya fitar muna da anty musha buki.
"Hmm! Ani imtihal abun Imran ya isheni,nayi magana har na gaji ke harta kai ga malam da kanshi ya mishi magana,Amma sai excuses yake kawowa wai yarinyar ce take ce mishi ya qara haquri akwai abunda take jira,Amma ke idan yazo wannan karon ki qara tun tubarshi kiji,ko Allah zaisa adace ya amince.
Tace"toh shikenan mama insha Allah I will talk to him, inyaso duk yanda mukayi zakiji,bari naje nayi sauri kafin ya iso.
Mama tace"toh Allah ya tsare,adawo lafiya.
