🏹💘🏹 *KIBIYAR SO* 🏹💘🏹
*ADABI WRITERS ASSO.*
*BY*
*AMEENA IBRAHEEM*
*OUM AMEER*
*WATTPAD@ UMMU-AMEER*
👉 🏹💘🏹 *PAGE 5*Cikin sati biyu mama taga canji sosai a wurin imtihal tadaina duk wasu abubuwanda mama bataso,yanzu idan mama ta gama abinci zuba mata take taje takai mishi tadawo,sannan ta daina yawan haduwa dashi saidai a makaranta,daman tashin hankalinta baifi ace omair baisamu yaci abinci ba,ko ace ya na neman wani abun baisamu ba.
Toh yanzu duk inda hankalinta yake zai tashi bazata samu natsuwa ba saita ga yasamu din,Kuma tun lokacinda sa'idu yayi mata kashedi da shiga gidan su,har wurin ibrahim yaje yakai qararta,yace tashiga gidanshi taci wa matarshi mutunci Kara itace,tun lokacin baba yayimata fada bata qara shigaba saidai idan taga su basma tace su gayawa Inna tana gaidata.
Mama sosai taji dadin zuwan imran,shiyasa takejin dadin shawararshi yarone Mai hankali da hangen nesa,duk lokacinda wani abu ya shige mata duhu shi take Kira ko ta kira nafisa (mommyn intisar),saboda suna da good contact sosai da ita.
Nafisa macecen Mai kirki wadda tasan yakamata a halin yanzu qaseem yafi malam ibrahim kudi nesa ba kusa ba,da goyon bayanta da kulawarta,komai qaseem ne yakeyiwa malam ibrahim da iyalinshi,abinci,sutura komai na rayuwa,cewa take ai komai qaseem zai zama aduniya yin Allah ne da Kuma malam ibrahim da ya tsaya mishi,batada baqin ciki ko kadan,komai zaiyiwa malam ibrahim bazai iya biyanshi wahalarshi ba saidai yayi iya abunda zai iya.
Gashi tana qaunar imtihal sosai,duk abunda za'ayiwa intisar iri daya ake musu,hatta da kayan makaranta komai na provision iri daya ake musu,Kuma gashi day suke,tun daga littafai kayan rubutu, school bag,shoes and what ever, though ba makaranta daya suke ba,saboda ita intisar ta kudi take acan gusau din,itakuma imtihal government school ce.
Amma tana da qoqari sosai.****
Alhamduillah a yanzu komai Yana zuwar musu smoothly,omair ya zana jarabawarshi ya gama ta zuwa ss1 yayinda itakuma ta yi tata jarabawar zuwa jss2.
Yanzu sosai ya maida hankali ga harkokin karatun islamiyya daman ba wani aiki yakeba,koda yaushe cikin lokaci yake halartar makaranta,ayanzu shirye shirye ake ta walimar mutum hamsin da sukayi sauka a makarantar,Wanda yau asabar ya rage saura one week,wato wata Saturday kenan.
Walima ce za'ayi gagaruma wacce ba'a taba yin irinta ba a makarantar islamiyyar madrasatul darul qur'an wal-hadith,Kuma daman ita makarantar tana cikin manyan islamiyya guda uku da akeji dasu acikin garin Anka,ba'a taba yin walima wadda zata dauki taron al'umma kamar taba,walima ce wadda aka dauki tsawon shekara bakwai ba'ayi ba sai yanzu.
Manyan maluma ne da manyan mutane aka gayyata masu manyan muqamai dakuma sarauta.Daliban sun hada harda imtihal da omair,da ruqayya qawarta,da yasir dai dai sauran yara.
Anshirya musabaqa,drama ta larabci,speach na larabci,karatun alqur'ni Mai girma daga dalibai masu sauka,tafsir,da dai sauransu.
Kullum sai anzo anyi gwaji,Wanda da alama malaman suna jin dadin yanda omair yake qoqari,da ya fara kwararo qira'a saikaga andade ba'a tsaidashi ba,akan yanda yake ba ko wane harafi haqqinshi,ga muryarshi Mai dadin sauraro.
Aduk lokacinda imtihal taga ana yabon omair ana zuzutashi cikin dalibai wani farinciki takeji har cikin ranta.
****
