CHAPTER SEVEN

6 3 0
                                    

🏹💘🏹 *KIBIYAR SO* 🏹💘🏹

*ADABI WRITER'S ASSO.*
(Home of exquisite writers)

                              *BY*
           *AMEENA IBRAHEEM*
                   *OUM AMEER*
           *WATTPAD-@ UMMU-AMEER*
               *MURUBUCIYAR....*
                  *ZAYTOONAH*
                  *ABARWA RAI*
                *NOW KIBIYAR SO......*

              

          👉🏹💘🏹 *PAGE 7*

           Inna batulu dai zaune take ta rabka uban tagumi tunani ne barkatai acikin ranta,bata ankara da cewar kuka take ba saida balkisu tace"mama kiyi haquri Dan Allah,insha Allah babu abunda zai samu ya omair lafiya Lou zai dawo garemu.

Qanqame balkisun tayi tace"nasani balkisu insha Allah lafiya Lou zai dawo.

Kamar daga sama taji Inna rahane na cewa"ahayye ni rahane! Sa'idu zo ka ga wani ikon Allah,akan wani banza bare dan haramun take tsiyayar hawaye,salon wani ciwo ya sameta a Dora maka wahalar saya mata magani,kaji wani kitififi Dan Allah! Shi ummarun jariri ne da zaki zo kina kuka akanshi.

"Kibarta kawai rahane wllhy tallhy idan wani ciwo ya sameta ko qasa bazan badamata ba,daga kawai anrage mugun iri ga gari,ke wllhy bari intaqaicemiki ban taba kwanan farinciki ba tun bayan samuwar yaronnan gidannan sai yanzu da ya tafi.....!

Cikin kuka tace"Amma dai malam sun gaya maka cewar zai dawo ko?? Dan Allah ka gayamin gaskiya cewar da ya samu lafiya zai dawo....!

Aiko kamar ta qara Mai fetur din bala'i yace"wllhy batulu sai in kokkoda Miki tafi,waike  wace irin mahaukaciyace, nagayamiki cewar sun sayardashi,bazai dawo ba,Ni nan Kuma Ni na Basu dama,saboda ai nine ubanshi ko??saboda haka ke bari in qare magana baki daya,wllhy idan kika sake yimin maganar yaronnan cikin gidana ban yafe Miki ba duniya da lahira,idan kinason zaman lafiya toh ki mance dashi,iskancin banza da qaryar banza harda cewa wai,ya ciyo kyautar dubbai dubbai,alhali qarya ce,yaronda bashi da mafadi kyautar mi zai ciyo,gashinan  dai ya ciwo kyautar barin gari Kuma Ni hakan yayimin daidai,ruwa su iza harda matuqa jirgin.

Duk da cewar maganar batayi mata dadi ba kalmar da yayi ta cewar danshi ne a yau tasa ta farinciki,ko ba komai yau zata shiga cikin tarihi cewar yasashi cikin jerin 'ya'yanshi.
Girgiza Kai tayi tace"malam nidai Ina jiyemaka ranar nadama,wllhy Ina jiyemaka ranar da zakazo kana roqon shi gafara,kariqa Sara kana duba bakin gatari.

"Naqi na duba bakin gatarin!! Nace naqi na duba bakin gatarin!! Batuluuu!! Toh,ki fita idona in rufe fa.
Yana kaiwa nan yasa takalmin shi faran daran ya fice daga gidan.

Itama rahane ta zauna abakin qofar dakinta tana ta jefo mata maganganu da habaici kala kala.

                                  ****

      Imtihal ce lullube acikin duvet jikinta sai kakkarwa yake da alama batada lafiya ne,mama ce nagani tsaye akanta tace" imtihal ki daure ki tashi kici abincannan koda kadan ne kinji??

Girgiza kanta tayi hawaye na diga ta gefen idonta tace"aa mama,bazan iya ci ba,Dan Allah mama omair fa?? Yaushe zai dawo gashi har Hutu ya qare andade da komawa makaranta Amma bai dawo ba,'yan ajinsu har sun fara karatu Amma baya nan.

Zaunawa mama tayi kusa da ita,ta janyota jikinta ahankali tashiga rarrashinta"kiyi haquri imtihal zangayamiki wata magana inaso ki nitsu sosai ki fahimceni.

"Haqiqa bayan mahaifiyar omair babu wata takusa dashi wadda zataji radadin rabuwa dashi da ta fiki,ako da yaushe mafi qololuwar abunda zaka yiwa mutuminda kakeso shine kayi qoqari kabashi farinciki,kayi duk yanda zakayi kaga ka fitar dashi daga halin damuwa ka Kuma bashi kariya gwargwadon iyawarka ta hanyar da zakasan bazai cutu ba.

   KIBIYAR SO (Complete)Where stories live. Discover now